Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Sha Tara

5
(1)

<< Previous

Rage gudun motar ya yi sa’ilin da suka iso kusa da babbar kasuwar, nan gefe guda can da bai da wadatar mutane ya faka motar gami da waigowa yana dubanta. 

“Ɗauki ki saita minti goma kacal, ki ɗaure shi a kwankwason ki, yadda da mun shiga tsakiyar kasuwar zai tashi. Ko ni zan ɗaura miki in cika ƙa’idar Imam?” Ya furta yana mata wani shu’umin kallo.

“Zan so hakan, amma zan iya.” Ta furta tana kaɗa masa manyan idanuwanta. Salon Ya dake shi, dan haka cikin  rawar baki ya fara magana.

“Wallahi ban so ki mutu yanzu Faɗima, gani nake ko Mamuda bazai fini ƙaunarki ba, da ina da iko da tuni na hana Imam sakaki cikin masu shahadar nan, amman ba yadda zanyi.” 

“Ba kome ai jihadi ne.”

Ta mayar masa da wata murya da ta sake gigita shi har bai san sa’adda ya matso sosai, ita ma ta matso sosai yadda ba dan kujerar dake gabansu daba abinda zai hana jikinsu haɗuwa. A hankali ta busa masa iskar bakinta tana kallon cikin idanuwansa. Lumshe idanuwan ya yi ya tafi tunanin wucen gadi yana jiran saukan laɓɓanta saman fuskarsa, cikin hanzari ta tura bomb din ƙasan kujeran motan, sai ta wayance kamar tana ɗaure shi.

“Yauwa ki daure shi da kyau, har mu isa gurin kiyi ta hailala da kabbara. ” 

Ya furta cike da mutuwar jiki a bayan ya ankara da abinda ta yi.

Sai da suka isa tsakiyar kasuwar gurin ya ɗaga mata ido, alamun ta shirya, nan da nan ya juya da zummar barin gurin, runtse idonta tayi ta fara lissafa takunsa,  ji kake duruum! Bomb ɗin ya tashi wanda ya sa da yawan mutanen gurin zubewa ƙasa cikin ihu da kururawa, kankace me wanann ta miƙe gami da yaye hijabin jikinta ta yi jifa da shi, bai sauka fuskar kowa ba sai ta Jabiru da ƙarar bomb din ta saka shi cin tuntuɓe da wani dutse ya faɗi. A kan idonsa ta sunkuci Abbati gami da kutsawa cikin ɗumbin jama’ar da ke rige-rigen ceton ransu. Tashi ya yi da ƙyar dan ya cimmata sai dai inaa! Ta daɗe da ɓacewa ganinsa!

Sai da ta tabbatar motar ta fara barin birnin na Kano, tukunna taji hankalinta ya fara kwanciya, nan ta hau jijjiga Abbati da har yanzu ke kukan tsoron ƙarar bomb ɗun. Kafin kuma ta tsunduma tunanin abinda za ta tarar a inda za ta nufa.

To, ina ma zata nufa idan ba can ba? Dole kam gidan Uwale za ta koma, tunda dai Malam din shi ne kaɗai ta sani a matsayin ubanta mariƙi, sai kuma wata Goggonta da Babanta ya taɓa bata labarinta tana aure Maƙarfi.  To idan ma can zata ita ina tasan gidan, ba ta jin ko sunan Goggon za ta iya tunawa balle tasa ran sanin wanda ya santa. Dole dai Bebejin za ta nufa, ko banza nan cibiyarta take binne.

Abubuwa da yawa ta tuna sa’ilin da ta shigo cikin garin, Abubuwa da yawa kuma ta gaza tunawar. Abu ɗaya ya ƙi ɓacewa idanuwanta shi ne haɗuwarta da yayanta mai koya mata karatu, murmushi take ita kaɗai sa’ilin da ta tuno wasu kalmominsa da yake yawan furta mata a wancan lokacin, sai yanzu ma’anarsu ke wanzuwa fess! Cikin kwakwalwarta suna samun matsugunni a zuciyarta. Lalle kam tana da masoyin da za ta bugi ƙirji da shi a bayan babban masoyinta Mamuda. Fatan ta Allah ya haɗa su watarana idan har da Alheri. Haka nan dai tana tafe tana ɗan tunane-tunanenta har ta ƙarasa ƙofar gidan nasu ta tura gami da kwarara sallama.

Ita da tiren zogalen da take tsinkewa ta miƙe tana ƙarewa kyakkyaawar budurwar da ke gaban nata kallo. Sai kuma ta cika tiren da sauri zogalen ya watsu a farfarjiyar tsakar gidan, tana mai sake wara manyan idanuwan nata.

Ya ma za ai ta kasa gane Faɗime ko da ace za ta kwashe shekaru Talatin ba ta saka ta a ido ba, ballantana wannan da duka-duka shekara bakwai ne rabonta da ita. Inaa! Ai in ta manta kamannin Faɗi, tamkar ta goge Bashari ne daga kwayar idonta, cikin sauri ta tattara tunaninta gefe, ta isa ga Faɗin tana mai fa din.

“Tsaya daga zaure, karki shigo mini ciki!” 

“Me ya kawoki tukun ? Wa gareki a cikin gidan nan?” Sai kuma idanuwanta suka sauka kan Abbati dake tsaye wuƙi-wuki yana kallonta

“Tirƙashi! Ta furta, tana mai tafa hannuwa.

“Aww wai da guda ɗaya kika komo? Inaa! Wallahi bai isheni ba Fadi. ‘Ya’ya goma nake sonki da su, kowanne da ubansa. A lokacinne zaki samu gurbin zama cikin gidan nan. Yanzu kam ki gaggauta komawa inda kika fito tun kafin na zuciya na kelaya miki kananzir na kyasta ashana wallahi! Ki fita na ce!”

Ta furta a tsawace gami da hankaɗa ta ta yi taga-taga ta dafe bango.

Hakan da Abbati ya gani ne ya saka shi matsawa da sauri ya hau Bugun kafafuwan Uwale, yana faɗin.

“karki sake bugun Ammita”. 

Mamaki ne ya kama Uwalen ganin abinda yaron da ba tafi ta tatsile shi ba ke yi. Ba ɓata lokaci ta finceke hannuwansa gami da jefa shi jikin uwarsa, ta masa ko kyakkyawar runguma tana rarrashi cikin zubar hawaye. Miƙewa ta yi tana kallon Uwalen, a hankali sai ta juya da hazari tana mai toshe bakinta da gyalen jikinta. 

Ta daɗe tsaye ƙofar gidan cikin wani irin kukan bakin ciki da duk wanda ya gani sai ya ji na sa hawayen na shirin zu ba. Da sauri kuma sai ta hau share fuskarta, ta sunkuya tana sharewa Abbati na sa da ke taya ta.

“Bari kuka Abbati, bai kamata uwarka ta yi kuka ba kaima kayi. Alƙawari ne wannan, daga yau uwarka ma ta daina zubar da hawaye balle kai. Mu tafi kawai, mu tafi duk inda Allah ya kaimu muyi zamanmu, na saka ka makaranta, kayi karatu yadda Babanka ya yi, ba zaka yi rayuwa irin ta uwarka ba, zan yi kome dan ka samu kyakkyawar rayuwa ba irin tawa ba.  Ba za kayi maraicin Uba ba, haka ba zaka yi na uwa ba. Zan yi kome dan na nuna ma Ubanka babu maraya sai rago, yau da ace da iyayena, na sani, bai isa ya jefa ni cikin wannan wahalalliyar rayuwar ba. Bari kuka kaji Abbati na.”

“To kema ki daina kukan!” Ya furta yana mai sa hannunsa saman fuskarta ya share mata hawayen yadda take masa.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×