Skip to content
Part 11 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Tafiya kawai take yi bata san inda take jefa ƙafarta ba. Gani take da ta tsaya Maama zata cimmata ta kashe tan kamar yarda Rizban ya faɗi. Ikon Allah ne kawai ya kawota nan wata unguwa Ngrannam, jikin wani massallaci ta durƙushe jin wani zazaafaman ciwo da ya taso mata tun daga yatsanta har cikin kokon kanta. Ganin wani ruwa na binta ya saka ta rintse ido tana faɗin wayyo zan mutu! Liman da fitowarsa ke nan daga Masallacin ya hangi sanda ta durƙushe ya ƙaraso gurin da gaggawa.

“Sannu yarinya, lafiya kuwa, ina gidanku kika fito da wannan maghribar farin da tsohon ciki?”

“Wayyo Baba cikina! Wayyo!! Taimaka mini zan mutu. Innalillahi!”

Ta furta tana cize laɓbanta kamar za ta fasasu.

Da saurinsa ya koma gida ya kira matarsa, ita ta kama Faɗime sukai cikin gidan da ita. Jin ihun da take yi cike da azaba ya sa liman kasa fita.

“Bilki ko asibiti zaku tafi ne.”

“A’ah malam a ɗan jinkirta dai dan naga haihuwar ta gabato sosai, mu kace za mu asibiti sai ta haife a mota. Tura dai yaro gidan Yakura ya kira ta.”

“To, ni ma bari na mata rubutu ko a samu sauƙi.”

“Yauwa Malam da kuwa ka taimaka.”

Ladan na kwala kiran Sallar Isha. Faɗime na santalo santalelan ɗanta da babu inda ya baro Babansa. Kai ko ta farce bai yi karambanin ɗauko uwar ba. Kafin ƙarfe goma na dare, Faɗime ta yi fes abinta cikin kayan da Inna Bilki ta fidda mata, an ɗora mata yaron saman hannuwanta sai kallonsa take tana murmushi ita ɗaya.

“Ikon Allah! Nono fa na ce ki ba shi ba kallo ba?”

A kunyace ta ɗauke kanta.

“Inna ai ban iya ba, ya zan bashin?”

“Au hakane fa! Kinsan fa abin da ni ma din ba taɓa haihuwar na yi ba, bara to mu gani.”

Nan da nan ta hau gwada mata sai kuwa ga ɗan Sagiru ya riƙe nono caraf yana jawo ruwansa da dukkan ƙarfinsa. Da sauri ta runtse idanuwanta tana furta wash Allah!

Liman ne ya shigo shi ma aka miƙa masa yaron ya kuwa rumgume shi tsantsan a jikinsa. Ina ma ace nasa ne wananna da bai san irin farin cikin da zai yi ba, sai dai ina! Shekaru sun shura sai dai kawai suyi fatan samu a aljannah in suna da rabo.

“Da wane suna za a ma yaron huɗu ba, ko in kin isa gida anyi masa?”

Ta tsinkayi muryar liman din.

Sadda kanta ta yi a hankali ta furta; “Ai ni ba ni da gida.” Sai kuma ta hau basu labarinta iyakar abinda za ta iya tunawa tana yi tana sharce hawaye, ita kanta Inna Bilkin hawayen take sharewa tana ƙarewar ƴar yarinyar dake ɗaukan irin wanɗannan manyan ƙaddarorin kallo.

Jikin liman ya yi matuƙar sanyi, ya yi matuƙar tausayawa mata da jinjina ƙarfin imanin da take da shi da bata yarda an zubar da cikin ba. Nan ya ƙara gasgata lalle yin hakan ba halinta ba ne kawai iftila’ine na rayuwa da ruɗun shaidan. “Lallai kam yarinya ki na cikin tashin hankali da ruɗun rayuwa. Haƙiƙa wannan shi ne tsoron Allah na haƙiƙa, tabbas da za a dinga samun mutane masu irin wannan tunanin na ƙin zubar da ciki, ko kuma su haife su kashe da tuni duniyar nan tana nan zaune lafiya. To amma ina! Kullum abubuwa ƙara taɓarɓarewa suke yi. In sha Allahu daga yau dukkan wani ruɗun rayuwa ya ƙare, za ki zauna damu, idan kinga kinbar cikinmu to ke ce kika gajiya damu. Ba mu da wata matsala da gani har matar tawa. Makaranta kuwa da kaina zan nema miki wacce zaki yi. Mai ki ke so a sakawa jikan nawa?”

Ya furta fuskarsa ɗauke da murmushi. Daɗi ne ya kashe ta jin ance za ta yi karatu, kenan zata cika burin Yayanta? Kai lalle wanan shi ne ake cewa karka fidda rai da tsammani, mai rabon ganin baɗi kuwa, ko ana dakata a turmi sai ya ganta, ita ina ta taɓa zaton wanann ranar za ta zo gareta. Da sauri takalli liman bakinta har kunne.

“Na gode Baba, Allah ya saka da alheri yaji ƙan magabata. Shi kuma a saka masa Sagir, sai ana kiransa ABBATI. Ta furta tana murmushi a ƙasan ranta. Tuna wasu kalaman Sagir. Hmmm!

*****

Can gidan Hajiya kuwa da gagarumin tashin hankalin ɓatan Faɗime suka tashi. Sosai suke kokawa kan lamarin da ya same su ta inda ba su taɓa za ta ba. Sai dai gaba ɗaya sun aje wani abin aka sake mata shi ya sa aka wayi gari babu ita, babu kuma wanda ya ganta ga dai Maigadi a bakin gate bare ace buɗewa ta yi ta fice. Sun fi aje hakan kan kawai muguntar uwar ɗakinta ne ya motsa ta ƙara wargaza rayuwar ɗiyar da lafiya ta fara samuwa gareta. Hakan ya sa Babban Mutum ba za cigiya gidajen Radio. Amman ina! Ko kiyashi bai zo ya ce musu ya ga mai kama da ita ba ma. Alhaji kam Malamai ya tara ya saka su roƙon Allah, babban fatansa ko bata dawo ba, to ta dawwama cikin kwanciyar hankali duk in da take. Kande kuwa ta so sanar ma Hajiya inda Fadime take ganin da tayi Hajiyar duk ta zuge yar walwalar ma ta rage, kullum ita ce cikin carbi tana kokawa mai kowa da kome, amman da Sagir ya ƙara mamayarta dolenta ta haƙura, ita dai dadinta ɗaya da ya ce mata Faɗi ta daɗe da isa ƙauyensu.

To, sai dai shi ma fa ta ɓangarensa abin ya fara wuce yadda yake tsammani. A da can, sanda take gabansa ya ɗauka ganinta shine babbar damuwar zuciyarsa, sai bayan fitarta daga rayuwarsa kamar yadda ya nema, ya fara gane lalle zaman Fati cikin gidansu shi ne abincin da zuciyar ta sa ke son ci. Yana gida ne, yana ofis ne, babu abinda yake gani sai murmushinta cikin hawaye a sanda zata bar gidan. Sosai ya maida kansa (busy) a gida da ofis duk dan ya bar tuna Faɗime da lamuranta. Amman ina! Zuciyarsa bata san wannan ba tunda ba daga gare shi ba ne, daga indallahi ne mai wassafa lamura ta inda baka yi zatonsa ba. Ya kuma ƙi yardarma kansa soyayyarta ce ke nuƙurƙusarsa, sai dai ya yi ta aje ma kansa tausayi ne, kai kace ada can da take cikin tausayin ya taɓa tausaya matan.

A tsaye yake rama yana zabgewa tsabar tunani da fargaba da suka cika zuciyarsa, amman ya ƙi zama ya hutawa kansa da aikin ofis, sai dai kullum ya loda wanda kwakwalwarsa ba za ta iya ɗauka ba, balle gangar jikinsa. Yau ne dai da abin ke neman kwantar dashi ya haye gadon Hajiyarsa ya ƙudundune, sa’ilin da wani zazzafan zazzabi ke ratsa ɓargonsa.

Sau biyu Hajiya tana leƙowa duba shi ganin har anyi la’asar bai tashi ba, ana ukun ne ta gaji ta janye bargon, yadda ta ganshi ba ƙaramin firgita ta yi ba ba ta taɓa kula ramar da autan nata ke yi ta kai haka ba. Jikinsa ta taɓa ta ji zafin da ya ƙara gigitata, ba shiri ta miƙe danta ɗauko waya a kira Babban Mutum, sai dai caraf ya riƙo hannuwanta yana dubanta a wahale. Zamewa ta yi ta zauna a hankali ta ɗago kansa ta ɗora saman cinyarta.

Ajiyar zuciyar ya sauke da ƙarfi, kafin kuma hawayen da ya daɗe yana so su zubo suka fara sauka saman cinyar Hajiyar ta sa, ita ɗinma ba ta yi ƙoƙarin hana shi ba, dan tasan ko mene ke damun autan nata, to yanzu ko zai ji salamarsa tunda ya yi kukan.

“Ki yafe mini Hajiya, ki roƙar mini Yaya Abdallah ma ya yafe mini dan na muku muguntar da idan kuka ji ta ba lalle ku iya yafe mini ba. Ni ne na cutar da rayuwar Fatima, na ɓata rayuwarta, ƙarshe na koreta daga gidan…nan da nan ya fara bawa Hajiyar labari cikin fitar hawaye, tun daga ranar da ta bashi (Hisnul Muslim) har zuwa farar asubar da Faɗi tabar gidan. Ya ƙare da “Wallahi Hajiya ban sani ba, bansan yarda akai na nemeta har na kai ga aikata wannan ɗanyen aikin.”

Da sauri ya sauka daga jikin Hajiyan da ta ɗade da daskarewa, ganin Babban mutum tsaye bakin ƙofa yana kallonsu. Tsugunnawa ya yi gabansa cikin kuka yana rokon ya yafe masa amanar sa da ya ci.

Cikin ƙunar rai ya daga hannu ya wanke shi da mari, ji kake tasss!

“Idan baka tashi ka bar gurin nan ba zanyi kasa-kasa da kai naga uban da ya tsaya maka, mara mutuncin banza, munafukin wofi.”

Ya furta cikin ɗaga murya.

Miƙewa ya yi daga wurin da ya faɗi domin ya yi mutuƙar jin marin, amman haka nan ya sake dawowa gabansa.

“Yaya duk abinda zaka yi min kayi mini matuƙar za ka huce daga ɓacin ran da na saka ka. Amman wallahi sharrin zuciya ne haɗe da ruɗun shaiɗan, wanda ni kaina bansan sanda na aikata hakan ba.”

Wani marin ya ƙara kai masa a karo na biyu nan ma ya ƙara samun sa, a karo na uku ne Alhaji da tahowarsa ke nan jin Hayaniya ya yi saurin saka hannu ya tare.

“Abdallah barshi haka tunda abin da zai faru ya riga da ya faru, kai kuma tashi ka tafi abinka Allah ya shirye ka, zalunci kuwa da zubar da daraja ka riga da ka yi mana shi, kai namu ne babu yadda za muyi da kai, amman ba don haka ba ni da kaina zan sa a rufe ka a gwada maka hankali ka gane abin da kayi ba adalci ba ne, idan  ma ba sakarci ba, ya za a yi ka yi ma yarinya ciki, ka kuma koreta, ina kake son ta kai shi a wanann shekarun nata da ko nauyin kanta ba za ta iya ɗauka ba, balle na yaron ciki? To wallahi ka yi gaggawar nemo ta ta yafe maka, domin Allah baya bacci, yana amsa addu’ar wanda aka zalunta cikin gaggawa.”

Shi kam sunkuyar da kansa ya yi ganin lamarin ya zo masa ta inda bai taɓa zata ba. Bai san cewa a baya zinariya ya ke tare da ita ba sai a yanzu da ya yi watsi da ita ya rabata da dukkan wani lamari da ya shafe shi, ina ma ace yana da ikon dawo da hannun agogo baya. Ina ma zai iya kasancewa mafarki ne ya ke yi ya buɗe idanunsa ya farka daga hakan. Ya runtse idanu sa’ilin da yake jin zuciyarsa kamar ta haukace tsabar matsanancin so da ƙaunar yar Faɗin da ya raina a baya can. A yanzu ko ya tabbata kowane namiji zai so mallakarta ta zame mi shi abar killacewa da kallo a kowane lokaci. Tabbas yasan ya yi babban rashin da samun kamarsa zai yi wuya. Wai neman Faɗi har sai an tuna masa? Sam! Bazai karaya ba, zai ci gaba da lalube da cigiya har sai ya kai ga mallakarta wacce ta fi komai yanzu a wajensa da zuciyarsa.

Wannan ke nan!

<< Fadime 10Fadime 12 >>

1 thought on “Fadime 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×