Ga Faɗi kuwa, rayuwa ta fara kyawu gidan Malam Liman. Dan kuwa tana rufa wata uku ya shiga ya fita ya sama mata gurbin karatu a secondry ƴan mata ta jeka ka dawo dake nan saman unguwar tasu. Haƙurin Abbati ya saka sam bata jin wahalar karatun musamman da Inna Bilki ta ke ɗaukan dukkan ɗawainiyar yaron. Wani sa’in kafin ta daga shi sau ɗaya, Innan ta ɗaga shi sau goma. Tufafi kam sai dai idan Malam bai shiga kasuwa ranar jumma’a ba, duk abinda ya gani haka nan yake ɗauko masa, wasu ma sai dai a aje dan gaba, wasu kuma a kyautar saboda matsi, amman hakan bazai sa wata jumma’ar ya sake shigo dasu ba.
Yaron cikin gata yake girma cike da soyayyar mutum ukun nan. Yana girma ya na gane uwarta sa da wata soyayya da ita kanta take mamakinta, dan kuwa yanzu ko makarantar in za ta je sai dai da dabara in ba haka ba kuwa ya dinga kuka ke nan ya ƙi kuma karɓar abincinsa. To, ita ɗinma haka nan ko makaranta take da ta tuna Abbati za ta hau murmushi ita ɗaya, fatanta a tashi ta komo gida, ta jefa shi sama, ta cafe, ta rarrawarshi, su kwashe da dariya a tare. Dariyar da Inna in tana kallo nan da nan za ta hau share hawaye musamman idan ta tuna yau idan babu su ina waɗannan bayin Allah za su sanya kansu.
“Akwai Allah.” Takance da kanta.
Yau ma dai dawowarta ke nan cikin murnan ta kammala jarrabawar zangon shiga SS1. Tana tsaka da wasa da Abbati ta jiyo kiran Malam ɗin dan haka ta riƙo hannunsa suka isa turakar Malam. Ruwan rubutu ya bata cikin wani ɗan koko yana faɗin.
“Shanye maza, ki shafe ma jikan nawa guntun a jikinsa, maganin duk wani sammu da ƙulumboto ne cikin yardar Allah.” Da murmushi ta karɓa ta yi kamar yadda ya ce.
“Yauwa ko ke fa. Ki ci gaba da haƙuri da rayuwa kinji Faɗima. Shi haƙuri idan har ba ka yi ba rashinsa ba zai ma kome ba, ki yi hakuri ko kya zam mai dacewa, ki kuma mu’amalanci ɗan uwanki domin Allah, za ki tashi ranar gobe kina me fahari da shi, karki zama maƙaryaci ya, don wataran za ki ji kunya, kar kuma ki yi ƙarya, don wataran za a tsaneki. Dukkanninmu nan bamu san ranar ɗayan mu ba. Don haka kowane mutum yana da ranarsa, ko gare ki, ko kuma ga waninki. Dan haka kiji tsoron Allah a duk inda za ki tsinci kanki. Shi kuma wannan rubutun insha Allahu duk shekara zan dinga yi miki shi in muna da rabon ganinta.”
Tsam ta yi! kalaman Malaman sun tsaya mata arai sosai, haka nan dai ta tashi ta koma ɗakin nasu, a hankali gwarancin Abbati ya fara dawo da ita daga in da ta dulmiya, sai ta biye masa suka ci gaba da wasansu.
Ilai kuwa, sati ɗaya da maganarsu da Malam babban tashin hankalin da yafi kowanne muni cikin tarihin rayuwarta ya same su. Tana cikin makaranta aka hau sanarwar ‘yan bindigi sun shigo cikin unguwar Ngrannam dan haka ba shiga ba fita, nan da nan aka kulle ƙofofin makarantar aka watsa Malamai ajujuwan dalibai dan su kula da duk motsinsu, su kuma yi ƙoƙarin kwantar musu da hankali. Nan fa aka taru musulmai na kiran Allah mai kowa da komai, kafirai na kiran Jesus! Banda Fadime da gaba ɗaya nutsuwarta ta ɗauke, Abbati kawai take hange a duk wani bugu na zuciyarta. Waige-waigen neman mafita ta hau yi, Allah da ikonsa kuwa ƙarar wata kakkarfar bindiga ya cika ilahirin ajin nasu wanda ya haddasa ruɗewar malaman da dalibai, suka kwanta ƙasan ajin suna ihu da kururuwa, shi ya bawa Faɗimen damar haura yar tagar dake gefenta ta fice daga ajin.
A dudduke take saɗaɗawa daga wannan taga zuwa wanann ƙofa har ta isa bayan banɗakin Makarantar inda gajeriyar katangar da suka gagara gine ta take. Nan da nan ta ɗare gami da haurawa. Haka ta dinga tafiya cikin sassarfar wani sa’in ta haɗa da gudu, wani sa’in in taga taron yan ta’addar ta ɓoye har su wuce, har ta iso ƙofar gidan Malam da tun daga bakin ƙofa ƙirjinta ya fara dukan tara-tara sakamakon ganin ƙofar da ta yi a karairaye. Sanya kanta ta yi cikin gidan, ta kuwa yi kyakkyawan ganin da ya tsaida tafiyar jininta na wucin gadi, kafin kuma ta yi wani tsalle ta riƙe tsinin wuƙar da ɗan ta’addan ke ƙoƙarin gagarawa a wuyan sandararren Abbatin!
“Karka kashe mini shi! Na haɗa ka da girman mahallacinka kabar mini shi, shi ne uwata, shi ne ubana, shi ne dangina, ba ni da kowa sai shi sai Allah. Dan girman mahallacinka ka mini abinda ni zaka mini amman banda Abbati!
Ta furta a gigice hannunta da ta riƙe wuƙar na tsiyayar jini.
To shi ɗinma turus ya yi yana ƙare mata kallon irin ƙarfin zuciyarta. A hankali ya zare wuƙar daga hannunta, yana kallon abokin tafiyarsa da ke muzurai.
“Jabiru, mu ɗauke ta kawai, mun samu ganimar da za mu ƙarawa Iman.”