"Jabiru mu ɗauke ta kawai mun samu ganimar da za mu ƙarawa Iman."
Gyaɗa masa kai wanda aka kira da Jabirun ya yi yana mai rataya zungureriyar bindigarsa a kafadarsa.
Ita kuwa tunda ta samu kanta ta hau jijjiga Abbati tana kiran sunansa, amman Ina! Shiru kake ji yaron babu wani alamun motsi a tattare dashi.
Rashin abinyi ya saka ta ɗago kai ido jajur tana kallon dan ta'addan da ya rufe rabin fuskarsa da wani koren ƙyalle. To shi ɗinma ita ya ke kallo, kafin kuma ya ce, "ba abinda aka masa, tsora ta ya yi. . .
Hi