Skip to content
Part 14 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Ga Fadime ko tunda ta shiga cikin gidan take tsaye rungume da Abbati har yanzu ta gagara zuba masa ruwan da aka faɗa mata. Suma ne, barci ne, a’ah mutuwa ya yi, masani kam sai Allah. Ta yi tsaye tana jiran ta ga ta inda wanda ke amsa sunan mijin nata zai farmata, amman shiru kake ji ba ko motsinsa balle ta sa ran zai shigo gidan. Hakan bai sa ta gaji da tsayuwar ba har gurin ƙarfe goma na dare da ya shigo. 

To shima turus ya yi ganinta tsaye , sai kuma ya kaɗa kai gami da faɗawa ɗakin dake gefenta. Rage kayan jikinsa ya yi sai gashi ya fito.

“Idan ke ba zaki shiga ba, to ki shigar da yaron karki ja masa raɓar da za ta haddasa masa ciwo.” 

Shiru ta yi kamar ba da ita yake magana ba. Ganin haka ya sa hannunsa ya zare yaron da ƙarfi yana shimfiɗe  shi a ƙirjinsa, sai dai jin yaron ya kwanta yarab ba alamun numfashi, ya saka shi kallonta da sauri yana mamakin sakarcinta, kafin kuma ya doka mata uban tsaki cikin mugun kallo. 

Da saurinsa ya kamfato sassanyan ruwa ya fara shafa masa a hankali yana yi yana jan yatsun ƙafarsa, ya ɗau tsahon lokaci yana aikata hakan sai ga Abbati ya fara sauke ajiyar zuciyar, kafin kuma ya sa kuka yana kiran Ammi. Rungume shi ya sake yi yana bubbuga bayansa a hankali, nan da nan kuwa ya yi shiru, gami da sake langaɓewa jikin ɗan ta’adda Mamuda.

To, shi ɗinma miƙewa ya yi ya shige ɗakin ba tare da ya kalli jihar da Faɗime take ba.

Ganin an shige ma ta da yaro ciki ya saka ta binsu da hanzarinta, turus ta yi ganin yayi rashe-rashe saman katifa yana ba wa Abbati abincin da bata san mene ne ba, yaron ko sai ci yake yana ƙarewa baƙuwar fuskar kallo. Ai ko da gudunta ta isa garesu tana mai leƙa abincin. Da sauri ta sauke ajiyar zuciya ganin shinkafa da miya ce har da naman kaza. 

Sai da ya tabbatar ya ƙoshi tukunna ya tura mata sauran gabanta. Nan ya hau jijjiga Abbati da ya sake langaɓewa jikinsa. A hankali kuma sai ya kwantar shi saman katifan, shi ma ya kwanta suna mai juya mata baya.

Ita kam mamakin ƙyale tan da Abbati ya yi ne ya gama kashe ta, wannan fa shi ne (Mahabba Fii Auwal Nazrah). To ai shi ke nan bari ta saka musu ido.

Tashi ta yi ta hau ƙarewa ɗakin kallo cikin hasken fitilan kwan. Babu wani shirgi cikinsa, daga kwatuwar katifar sai akwatin ƙarfen Mamuda, sai kuma wasu tarin kwanukan abinci dake can kusurwar ɗakin. Ganin Buzu ya saka ta tuna sallolin da ke kanta. Da sauri ta tashi ta yo Alwala ta fara rama sallolinta. Nan ta bingire saman Buzun, tun tana ma Liman addu’ar samun rahma ga mai kowa da kome har nannauyan barcin ya sace ta.

Surutun Abbati ne ya tada ta daga nannauyan barcin da ya sace ta. 

“Baba ya ce ki tashi ki shalla.” 

Da sauri ta ruƙo shi cikin zare ido.

“Waya ce maka  Babanka ne? Kul na sake jin ka sake kiran mai zubar da jinin musulmai yan uwansa da Baba. Ba kasan shi ya kashe mana Baba Liman ba?. Duk zaluncin naka mahaifin ba zai taɓa iya kisa ba, dan haka kar na sake ganin ka je ko kusa da shi ne.”

Sai da ya gama ƙarewa bakinta kallo yana kwaɓe baki da shirin saka kuka, sai kuma ya maƙe kafaɗa yana girigiza kai.

“Babana ne ni, ai Baba kai ne Babana ko?” 

Gyada masa kai kawai ya yiwa Faɗime wani mugun kallo. Tana ruƙoshi yana fizgewa, haka ya sake komawa jikin Mamuda yana kai ƙararta cikin gwarancinsa. Ai sai ta zubawa sarautar Allah ido tana mamakin inda rayuwa ta kawo su yanzu kuma. Sai kuma ta  sakarma Mamudan harara haɗe da sakin kwafar za ka sani ne.

Haka rayuwar Faɗime ta ci gaba da tafiya cikin yan ta’adda, kullum su ake kira daga fada a rarraba musu abinda zasu girkama mutanen ƙaryar cikin  manyan takwanan. Har ya zama tana cikin madafan da Imam ke ji dasu. Wani sa’in kuma a tura su cikin ƙauyen Tikuwa su je su kamo kifin da za suci ranar a kogin garin. Abu ɗaya ke ta da ma Faɗime hankali a zaman ƙaryar, wanda bata fatan ya hau kanta. Shi ne Jihadin da ake tura ƴan matan lokaci zuwa lokaci, wanda kan idonta ake ɗaura musu bomb a kwankwaso ana yi ana sakin kabbara da faɗin tagoma shin da duk wacce ta mutu gurin jihadin za ta samu. Wannan abu shi kaɗai take addu’ar kar ya hau kanta. 

Game da zamanta da Mamuda kam babu wata matsala da take fuskanta daga gare shi, yo ina ma ta ishe she kallo ? Ita har mamakin dalilin da yasa ya furta zai aureta take yi, tunda dai babu alamun soyayya ce ta saka hakan. Abbati kam kullum da irin kalan wa’azin da za ta ma sa dan ya bar kula Mamuda mai kashe jama’a, amman ina! Yaro bai san wanann ba, sai dai in bai hangi Baban nasa ba. 

Kai har sai da ta kai ga dukansa a ranar nan ne ta san wanene Mamuda. Dan kuwa maƙureta ya yi jikin bango cike da gargadin karta sake faɗa wa yaronsa abinda zai ruɗa masa tunani balle akai ga bugu. Idan ko taƙi ji, to ita ma ba ta wuce ya mata duka kwatankwacin wanda ta ma ɗan nasa ba. Ita dai da ta samu ta kwace da ga maƙurar, ai sai ta fada ɗaki tana sakin kukan azaba da binsa da Allah Ya isa.

*****

Yau kowa ka gani fadar jikinsa ya yi sanyi, dan kuwa Babban kwamandan Imam ta ɓangaren duk wata hanyar sadarwa (communications) ya iso da mummunan labarin da ya gani a dandalin sadarwa na Facebook cewar, dandazon jami’an tsaro sun kewaye ilahirin ƙaryar tasu, har cikin kauyen Tikuwa sun wawwatsu. Nan da nan Imam ya fara shirya manyan yaran nasa da umarnin su gaggauta fita su tare su kafin su shigo su musu ta’adi. 

Ita kam Faɗime haka nan take ji ba ta son fitar nan da Mamuda zai yi, sai dai kafin ta yanke shawarar tunkararsa, har ya gama kintsa kansa. Akan idonta ya sunkuya ya sumbaci Abbati da ke barci, bai ko kalle ta ba ya fara ƙoƙarin fice wa. 

“Mamuda!” Tsai ya yi jin saukar muryarta ta cikin zuciyarsa, a karo na farko da ta kira sunansa ba tare da ta ƙara dan ta’adda ba. 

“Kayi mantuwa.” Ta furta tana ƙarasawa gare shi. Shi ɗin ma juyowa ya yi yana duban hannunta da take miƙa masa layarsa da ya manta. Cikin arashi hannuwansu suka gogi na juna, da sauri sukai saurin janye hannuwan jin wani shock da hakan ya haifar.

Tsayawa ɗaura layar a dantsen hannunsa ya yi, kasancewar hannunsa na rawa sai ta sake zamewa ta faɗi. A kusan tare suka sunkuya zasu ɗauka wanda ya haddasa musu gwara kai, kafin kuma idanuwansu su lume cikin na juna duk a duƙen.

A marairace take kallonsa idanuwanta har sun fara ciko da kwalla.

“Dan Allah karka tafi ka kashe Musulmi ɗan uwanka, dan Allah.” 

Ta furta tana mai sakar masa kuka a hankali.

<< Fadime 13Fadime 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×