Ƙarfin zuciya ne kawai ya saka shi ɗagowa ya fice daga gidan cikin sassarfa. Ya daɗe tsaye ƙofar gidan idanuwansa lumshe yana daidaita luguden da zuciyarsa ke yi, shi kaɗai yasan illar da kalamanta suka yiwa zuciyarsa, shi kaɗai yasan raunin da yake ji a duk ɗora idonsa da zai yi kanta. Daga in da yake tsayen, yana iya jiyo shessheƙar kukanta da ke barazanar ruguza masa duk wani ƙarfin gwiwa da yake da shi. Abu ɗaya ya sani a yanzu, ko da ya tafi ba shi da wani sauran ƙarfin da zai iya. . .
Fadime