Skip to content
Part 16 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

To fa tun daga ranar suka hau kula junansu sama-sama, kowa na son ƙaryata abinda yake ji game da ɗan uwansa. Musamman ita da take ganin shigarta jikinsa zai sa ta ci galaba kansa ya bar fita kashe mutane, kai ya ma bar ƙaryar gaba ɗaya, ta yi ta shigo rayuwarsa ne ma dan ta yi silar shiryuwarsa. 

Saɓanin shi da yake gudun abinda zai haɗa shi da ita, balle har ta ribace shi ya aikata abinda gaba ɗayansu ba zai musu kyawu ba.

To ƙarshe dai ita ta fara sauke kome, ta hanyar kula da shi kama daga tufafinsa, abincinsa, kai da duk wata hanyar da ta san zai ji dadinsa. A hankali sai gashi har yana zama ya yi hira da ita, kai har ta kai in zai abu sai ya sanarta da roƙon ta masa addu’ar dacewa.

To yau ma dai tana tsaka da cin abinci ya shigo, kai tsaye ya doshi gurin kayansa ya hau fiddo da wanda da ta ga ya saka tasan fita ce za ayi. Kasa kai lomar da ta ɗebo bakinta ta yi, ta tsaya tana kallonsa. 

To, shi ma ganin hakan, sai ya aje kayan hannunsa, ya zo ya zauna gefenta yana mai riƙo hannuwanta cikin nasa.

“Gobe za mu fita, ki mini addu’ar dawowa lafiya.”

Kallonsa ta yi, idanuwanta har sun fara fiddo kwalla.

Nan da nan ya hau girgiza ma ta kai alamun bai so ta yi kukan. 

“Karki damu, lafiya za mu je mu dawo, ba abinda zai samu wannan gardin mijin naki.”

Murmushi ta yi jin ƙarshen zancensa.

“Ni fa ba shi ne damuwa ta ba, ba na so ka je ka kashe musulmi ɗan uwanka, wanda bai takaleka da yaƙi ba, bai tsaya gaban masallacinka ba, bai saka ma wuƙa kabar addininka ba, kalmar Ashhadu anla’ilaha illallah ai ta haɗa kome. Dan Allah ka ce ma Imam ba zaka je ba, ni ko ƙaryar ciwo ne ka yi.”

 Sai kuma ta sakar masa kuka a hankali.

“Kisa ne ba ki so na yi ko? To na miki alƙawarin ko jinin kiyashi ba zan ɗauka ba a wannan fitar, amman fa tafiya dole ce na yi, dan kuwa ran Imam a ɓace yake sakamakon mutuwar Lamiɗo da jami’an tsaro suka kashe. Baki san Lamido ɗansa ne na cikinsa ba? Inaaa! Ki yi haƙuri Fati, bazan iya ƙarya ga Imam ba.”

“To idan ka ce ba zaka kashe kowa ba, in kuma kai aka kawo maka hari fa?”

“Sai in tsaya koma mene ne ya same ni, kinga idan na mutu, sai ki yiwa gardin mijinki takaba.”

“Ka gani ba na so.” Ta furta tana langa6e kai.

“Kin gani ina so.” Ya furta shi ma yana langaɓe ma ta kan.

Murmushi ta yi ganin yadda na yi.

“To kaje da ni mana, ka ga duk wanda zai taɓaka sai inyi saurin faɗa maka ka kauce.”

Sosai ya kwashe da dariya irin wacce bata taɓa sanin ya iya ta ba. Sai ta yi tsai tana kallonsa ganin irin kyawun da dariyar ta masa.

hure ma ta idon ya yi a hankali da ya maido ta cikin tunaninta.

“Bari kallona, bansan irin kakanninki ba.”

“Ka na da kyau!” Ta furta tana kallon yatsunta.

“I know.” Ya mayar mata, sai kuma suka kwashe da dariya a tare suna nuna juna.

Tun daga ranar suka fara nuna ma junansu matsananciyar soyayar da basu san farkonta ba, kowa burinsa ya farantama ɗan uwansa da duk abinda yake so, rikice ne kullum ya ce zai fita Jihadin nasu sai an yi shi, ta dinga kuka ke nan, wani zubin har yaje ya komo. Jan hankalinsa ga gaskiya kuwa dan ya bijirewa Imam ba ta fasa ba, amman inaa! Taurin kai, kai kace a nono suka sha biyayya ga Imam.

To yau ma haka nan ta kawo masa hirar da idan haddarta zai yi, ya riga da ya gama haddacewar.

“Kasan me nake saƙawa a raina?” Ta furta tana ɗora kanta saman cinyarsa.

Shiru ya mata ya hau shafa lallausan gashinta. Ganin haka ya sa ta ɗora.

“Me zai hana ba zaka haɗa kungiya ba kai ma, idan ya so sai ka horar dasu, rana ɗaya sai ku yi ƙunan baƙin wake ku afkama Iman. Nima kuma a hankali sai in dinga jan hankalin matan da muke tare, ka ga zamu yi yawan da zamu iya karkashe su baki ɗaya. Shi ke nan sai muyi rayuwar mu cikin aminci da kwanciyar hankali.”

“Amman Ali Nuhu ne Director film ɗin, umm Smart girl ?” Ya furta yana kewaya hannunsa saman girarta.

“Ni ba wanann za ka ce mini ba, ka ce to kawai.”

“To!” Na ce to.”

“Ka gani ban son haka.”

“Haaa’an to me na yi kuma? Kince na ce to, kuma ai na ce to ɗin.”

“To ai wannan to ɗin ba ta kai zuci ba”.

“Haka na ce miki? To wanann to ɗin har kusa da inda Fati ta maƙale ta je.”

“Allah kai ka faye bagarar da zance.” Ta furta tana kumbura.

“To ya zan yi miki Fati ? Kinfi kowa sanin abinda kike faɗa ba zai taɓa yiwuwa ba. Ki cire irin waɗannan tunane-tunanen idan ba so kike ƙaramar takaba ta kamaki ba.”

“To wai kai mu gudu mana, tunda kasan kan jejin nan.”

Kallonta yake cikin murmushin wautarta.

“Lalle ke har kina sakawa kanki gudu da ga nan?”

“Me zai hana kuwa ?”

“Bakin sha ruwan ƙoƙon nan ba? To ai kafi ne, ba zaki taɓa iya barin nan ba sai da umarnin Imam.”

“Lalle ma, ni kam ina jin zan iya tafiya duk sanda na so.”

“Af! Yanzu ma ba ta ɓaci ba, tafi mu gani.”

“Hmm! Bazan iya tafiya yanzu ba, saboda nasan ko na tafi bazan zauna lafiya ba. Ba kasan yadda nake jinka a raina ba ne. Allah Baban Abbati ina jin, yau ace babu kai, babu abinda zai hana ni bin ka in da ka tafi. Kaga wanann abin shi zai hanani tafiya, na gwammace in dawwama da kai a duk halin da kake ciki, yo ina ma za ni ? bacin kai ne uwa da ubana, sam! Ba na fatan ƙaddara da za ta raba ni da kai. Wata irin ƙauna nake maka da bansan dalilinta ba.” 

Da ƙarfinsa ya rungumeta a faffaɗan kirjinsa jin wata kwalla na ƙoƙarin sakko masa. Shakka babu yasan ko shi yana jin fin abinda take ji a tare da shi.

 Lumshe idanuwansa ya yi sa’ilin da yaji tsoron mutuwa ya ratsa shi a karo na farko tun wanzuwarsa cikin karyar!

<< Fadime 15Fadime 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×