"Yauwa ni ko na tambayeka?" Ta furta tana zame jikinta da ga nasa.
"Ina jinki Fati" ya faɗa da son daidaita kansa.
"Wai a ina ka iya Turanci?"
"Ji da Allah. Da ke gingimemen jahili kike ɗaukata? To har kwalin Degree gardin mijin naki ya mallaka."
"Dan Allah fa? To ina suke? Mai kuma ya kawoka nan gurin bacin da iliminka? Ina ne ma garinku da iyayenka ko kaima sun rasu?"
"Wai! To duk ki tattara tamboyinki zuwa waccar akwatin, amsarki na ciki."
Da saurinta ta miƙe za ta je ga inda ya nuna ma tan. Ya kuwa. . .
Amazing
Interesting