Kwana ɗaya, biyu, kai har aka tafi sati da mutuwar Mamuda, Faɗi ba ta ji Imam ya ɗau wani mataki kan na ta lefin ba. Sai kawai ta fidda rai ganin ƙara wani girmamata ake yi a ƙaryar ma. Sai dai babu walwala, ko magana ta rage yi daga ita har Abbati da ya fara haƙura da neman Babansa. Kuka kam, kullum ta sa kanta saman katifa ta dinga yinsa ke nan tana shafa gurin da Mamuda ya saba kwanciya.
Haka dai har ta fita daga takaba. Inda Jabiru ya je ya matsama Imam da rikicin a aura masa Faɗi, wani abu da ya bata mamaki yadda Imam ya ture zancen Jabiru gefe da cewar ya yi haƙuri ba yanzu ba. Wannan abin ya sanyata cikin tunanin anya Imam ba ya wani shiri yake kanta ba?
Ilai kuwa yau ta je karɓo shinkafar da za ta dafa, kamar ance matsa ƙofar Imam ta jiyo zancen da ya saka ta maƙalewa tana saurara cikin mabayyani.
“Wannan fa da kai na na jarrabata na ga aikinta, ka ga da fatar baƙar kyanwar da bata buɗe ido ba aka yi rufin farko, sa’annan aka sake naɗeta da fatar ɗan tayin cikin Tunkiya, sa’ananan aka naɗeta da fatar baƙin kumurci, sa’annan aka kewaye ta da baƙin saƙi. Da gaske har bango tana ratsewa, dan kuwa na gwada ratsewar kuma na ratsen. Saboda haka zan karɓi makaman, amman dole ka ƙara mini cikon Million guda namu na Nijeriya. Game da bayi kuwa, akwai Faɗima matar Mamuda, shekaran jiyan nan ta fita takaba, sai ka siye ta ka haɗa da sauran ku tafi.”
“La la ba na son farar mace.”
Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi tana mai godewa Allah da ya yo ta a jinsin fararen mata. Sai yanzu ta gane wanda ke maganar ma da taji bagwariyar hausarsa. Balarabe Ma’amun ne da yake zuwa jefi-jefi gurin Imam ɗin. Ba ta taɓa sanin abinda ke kawo shi ba sai yau. Ashe shike kawowa Imam wasu muggan makaman da suke ta’addancinsu.
“To Allah ya kyauta.”
Ta furta tana ƙoƙarin daga ƙafarta dan ta bar wurin, sai dai turus ta yi jin zancen da ya kaɗa mata ‘ya’yan hanji ta riƙe mararta da ƙarfi cikin tana dare idanuwa.
“To ai shi ke nan, na saka ta cikin waɗanda za su fita Jihadi gobe” Abinda Imam ya ce ke nan!
Sau takwas tana kewaya makewayi sakamakon wani zawo da ta ɓarke dashi cikin rashin sanin abin yi. A na taran ne aka doka mata sallama ana umartar ta da tazo fada Imam na son ganinta. San da ta isa, ‘yammata uku ta tarar zube gaban Imam, nan da nan itama ta zube yadda ta ga sunyi. Nan ya hau sanarsu jihadin da za su fita gobe yana mai kwaɗaita musu tagamoshin ladan da kowacce za ta samu idan ta mutu wurin jihadin.
Kowacce akwai garin da za ta ta saka bomb din cikin tsakiyar kasuwa. In da aka tura Faɗi kano ita da Kwamanda Jabiru da zai tuƙata a motar da za ta tafin, ya kuma sanya ido kanta dan kar a samu matsala. Sai da ya gama kashe-kashensa tas! Tukunna ya tambaya ko da mai magana. Da gaggawa Faɗi ta ɗaga kai.
“Ina son abar ni na fita wanann babban jihadin da ɗa na Abbati, dan shi ma ya samu tagomashin da ake samu.”
“Allahu Akbar!” Sautin kabbara ya ratsa ilahirin fadar, cikin jinjinawa Faɗime na ganin yadda ta riƙe da’awar Imam hannu bibbiyu.
Nan da nan Imam ya amince, in da ya tashi kwamanda Sambo da yaje ya koya musu yadda za su ta da bomb ɗin.
Aka ce wai zaman duniya da mai rai ake yinsa, tsakar dare Faɗi ta jawo Akwatin Mamuda ta hau birkita ta. Ba ta daɗe ba ko ta jawo wata baƙar ledar viva, da aka shirya wasu miƙaƙƙun takardu cikinta, ko buɗewa ba ta yi ba ta aje gefenta. Ci gaba ta yi da binciken cikin ikon Allah sai gashi ta jawo kuɗin da adadinsu zai kai dubu goma. Sauke ajiyar zuciya ta yi tana mai godewa Allah da Mamuda da ya yi tunanin aje kuɗi haka.
Kafin ƙarfe shida na safe sai ga Faɗime ta shirya tsaf cikin zani da riga, ta soka doguwar ledar tsakiyar bayanta, kuɗin kuma ta cusa cikin gashinta ta naɗe. Ta nemo wani katon gyale ta naɗe kannata da shi, kafin kuma ta kima koren hijabin da aka rarraba musu jiya. Sai sannan ta kallo Abbati da ke ta mata tambayar ina za su je.
“Gurin Baba na ce maka.” Amsar da ta bashi ke nan ta zauna zaman jiran ace su fito.
Karfe bakwai dai-dai Faɗime ta harɗe cikin baƙar Hilux mai ɗauke da bakaken tagogi. Gefenta Abbati ne zaune shi ma an ɗaura masa koren kyalle a goshinsa. Sai Jabiru dake gaban motar yana ƙoƙarin tashinta.
A hankali take ƙarewa garin na Maiduguri kallo sa’ilin da suke wucewa ta kusa dashi, cikin tuna abubuwan da suka faru da ita cikinsa, a zamanta na shekaru biyar da tayi. “Allah sarki Maama Rizbaan ko ina zan sake ganinki.” Ta furta a ranta sa’ilin da take sauke idanuwanta ɓarin da Abbati yake.