Ko da ta isa cikin tashar zuru ta yi tana ƙarewa motocin kallo, sunayen garuruwa kawai kake ji na tashi, Lagos, Gombe, Bauchi, Kebbi, Jos.. ga suñan dai kala-kala. Lumshe idanuwanta ta yi sa'ilin da ta tuna hirarta da Mamuda "Babana Balarabe ne, muna zaune a Lagos, cikin..." Sai kawai ta saki murmushi ita ɗaya tana dosar motar lagos din. Gwara kam ta tafi garinsu masoyin nata, ko banza ta din gajin ƙamshin ƙasar da ya taka.
Da ikon Allah ko mutum guda suke jira, nan da nan ta biya abinda suka caje ta, in da. . .