“Tunda kika tako gidan nan kin shiga ke nan, tunda kika sha ruwan gidana babu mai raba ni da ke, i swear by Allah!”
“Har wannan?”
Ta furta tana jefa mata wasiƙar da ke hannunta, bayan ta aje mata wani kasalallen kallo mai nuna na shirya miki.
Cafewa ta yi ta fara jujjuya takardar, sai kuma idanuwanta suka sauka kan Adreshin. Tana kula da sa’adda suka ƙara girma, gumi ya fara tsattsafo mata, kafin kuma ta ɗago tana aje su cikin nata.
“Yo…You mean gidan Murad Abduljabbar kike nema? Kin san waye shi kuwa…?”
“Suruki na ne.”
“Ƙarya kike.”
Ta furta kai tsaye tana ƙarasawa jikin tagar ɗakin ta rufe, ta dawo ga ƙofa ma ta rufe, ta sauke labulaye tamkar mai tsoron wani zai musu laɓe.
“Ki karanta takardar duka kafin ki ƙaryata ni.”
Ta furta, zuciyarta cunkushe da mamakin waye wannan da kai tsaye Linda ke ƙaryata ta da saninsa.
“Ai ba zan iya ba ne rubutun da yawa. Abu ɗaya na sani zan faɗa miki shi yanzu. Ko da za ki fito da 1 million a yanzu, to fa ba za su siyo miki Mai Gadi ɗaya da ke farkon shiga unguwar da gidan ma yake ba, balle har kisa rai za ki iya isa ƙofar da za ta sadaki da cikin gidan. A yanzu shugaban ƙasa ne kawai zai nuna masa tsaro. Shiga unguwarsa daidai yake da ace ki haɗiye Maciji cikin mintuna biyar!”
“Zan shiga, kuma tare da ke.”
Zuwa yanzu ta fara tunanin anya ba a taɓa fidda mata wata shaida a gidan mahaukata ba? Kamar ba ta fahimtar me take faɗa mata. Ganin tana ɓata lokacinta ya sakata lalubar hannun kujera ta zauna tana warware takardar gabaɗaya. Zuciyarta na daɗa tuna tar mata ai ba a ƙwacewa yaro garma. Idan kuma mutum ya ce zai haɗiyi gatari, sai ka sakar masa ƙotar.
Sai dai duk wannan tunanin nata ya canja a bayan ta gama duba takardar, ba ta ce kome ba sai da ta isa ga fridge ɗinta ta zaro ruwa ta cika tambulan da shi ta kwankwaɗe, kana ta sauke idanuwanta kan Faɗime da wani ƙayataccen murmushi.
“Ba ke kaɗai kika yi bankwana da talauci ba, har ni da duk wani da ya dangance ni ba shi ba talauci har abada. Me ya sa ba ki haihu da shi ba? Kin san da kin haɗa jini da shi da har tattaɓa kunnenki ba su da rabon talauci? Kodayake, akwai wani tunani da ya shige ni, sassauƙan tunani da ko ke za ki iya saƙa shi. Mu yi amfani da Abbati a matsayin jikan wannan tsohon gurgun …”
“Ban iya cin amana ba, ban iya ƙarya ba…”
Ta furta tana ƙarasowa gabanta a gaggauce.
“Ban gane gurgu ba? Me ya faru da shi?”
“Ki tattara dukkan tambayoyinki zuwa gare shi. Kodayake wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa anan cikin unguwar tasa wata Tanker ta bi ta kan ƙafafunsa ta yi sanadin zamar da shi gurgu. In da yanzu yana kwance a gidansa yana cin dukiyarsa da aka tabbatar shi kansa bai san adadinta ba. Karki damu, ko da kuturu ne babu abinda ni Linda zai hanani ɗaukar wankan mutuwa ko zan iya burge shi. Saka zoben hannunki, yanzu za mu tafi, a cikin satin nan zan tafi Belgium, a kaf rayuwata ita ce ƙasar da nake fatan takawa kafin mutuwata. Ashe ba mafarki nake yi ba, zan shige ta tun ina ficiciyata a dalilinki Ammy.”
“Linda!”
Ta furta a kausashe tana mata tafi, gani take kamar ba a cikin hankalinta take ba, tana magana fa tana kwaɓe kayan jikinta tamkar mahaukaci sabon samu.
“Da hankalina fa, karki damu, kuɗi ba abinda baya sakawa. Mu tafi kafin na fara hango ni a Jerusalem.”
“Wa ya ce miki kuɗi zan je karɓowa gurinsa? Zuwa za mu yi na ba shi tabbacin mutuwar ɗansa, na kuma roƙe shi da ya ci gaba da nema masa gafarar Allah, ba na son ko sisinsa, ko ya ba ni ba zan karɓa ba.”
“Kar ki yi sanadin da hankalina zai bar jikina, please!”
Ta furta tana dafe kan ta, har yanzu gumi bai bar tsattsafowa daga goshinta ba.
“Ba ki da hankali, an taɓa faɗa miki haka ko? Idan har za a baki arziƙi ki sa ƙafa ki shure, to lalle ne ba ki kyautawa Mijinki ba. Mamuda ya san waye mahaifinsa, ya san tarin dukiyarsa, shi ya sa ya roƙe ki da ki taho nan ki je ga mahaifin nasa ki amshi rabonki. Mamuda na son ki da alheri baya kuma so bayanki ya tozarta, shi ya sa bai miki baƙin ciki ba ya ce a mallaka miki duk wani abu da yake nasa. Ammy, wannan ba lokaci ba ne na baki son wannan, kina son wannan, lokaci ne da za ki gina rayuwarki da ta ɗan ki, lokaci ne da za ki nunawa maƙiyanki alherin da Allah ya tanadar miki, lokaci ne kuma da za ki aikata kome da ƙarfin ki, kuɗi na iya siyo miki daraja fiye da ta sarki a wannan duniyar. Idan har ba ki so ki koma bara, idan har ba ki so ki saɓawa Allah, to kuwa ki yi amfani da abinda Masoyinki ya mallaka miki. Mamuda mutum ne, irin wanda ban yi zaton akwai irinsu a yanzu ba. Mugunta ɗaya ya miki da bai miki ciki ba, you know what I mean, huh?”
Ta furta tana kanne mata ido.
“Da wahala ki yi magana ba ki ci mutuncin mutum ba. Ba lefinsa ba ne, Allah ne bai kawo ba.”
“Ko kuma ba ki da rabon mallakar duka dukiyar Murad ba. Bari ki ga, wani wankan zan sake, kayan da zansa ma bashin su zanje na ciyo, daga gobe na zama millionaire, so ba zansa rigar ƙasa da Dubu Dari Biyu ba. Ke fa sani ne baki yi ba, da ace zai ɗauke ni aikin me yi masa wanka da tsarkin kashi, da gudu zan karɓa, na tabbata albashina zai fi na wani Farfesan.”
“Sai gashi kuma idan aka shiga, babu fita.”
Ta furta tana mata wani ɓoyayyen murmushi.
Laƙwas ta yi ta zame a hankali ta zauna hannun kujerar idanuwanta a rufe.
“Ban san zan haɗu da ke ba, da a ce bawa na sanin gabansa da kai tsaye ba ma nan zan yo ba. Gurin Imam zan tafi na haɗu da Mamuda na aure shi kafin ke.”
Ta furta tana sauke idanuwanta cikin nata, sai kuma suka tuntsire da dariya a tare.
“Ba ki da rabo.”
“Sai na haɗuwa da ke.”
***** *****
Bayan shekara biyu
Rayuwar ta canja mata ta inda bata zata ba. A yanzu da take kan hanyarta ta zuwa ɗauko Abbati daga makaranta, ji take babu wanda ya kai ta kwanciyar hankali a duniya. Babu abinda ta nema ta rasa, ba ta kuma tunanin ko Abbati zai nemi wani abin ya rasa. Mahmuda ya mata gata, haka Dattijo Murad, ya karɓe ta ta inda bata zata ba, ya mayarta makwafin ɗansa, ya mallaka mata duk wani abu da ya san haƙƙin ɗansa ne, ya ƙara mata da na shi. Ta ga nadamarsa, ya yi nadama irin wacce kullum duniya sai ya zubar da kwalla, sai ya yiwa ɗansa Addu’a. Ita ta saka shi ya gina masallatai da sunan ɗansa, ita ma ta rarraba kwatar abin da ta samu ga mabuƙata. A yau gashi wai ita Faɗime ce ke da gida a cikin garin lagos a unguwar wane da wance, take da manyan kamfanonuwa har biyu, ɗaya ta barwa Linda ke kula da shi, ɗaya kuma ta bawa mutumin da ta tabbata ba wayonta ne ya saka shi sake wanzuwa gare ta ba, wata ƙaddarar ce mai girma da ba ta san mafarinta ba. Sai dai ko menene a yanzu tana jinta cikakkiyar mutum, tana rayuwa da wani makusancinta da koda ba sa muhalli ɗaya, to fa dukkan idanuwansa na kanta, da wani burinsa da ita kanta bata san dalilinta na ƙin amince masa ya gabatar da shi ba.”
“Hmm!” Ta sauke numfashi tana taka burki daidai gate ɗin makarantar.
“Ki kai Abbati Cyprus ya yi duka karantunsa a can. Ya girmi zaman Naija fa Ammy.”
Ta tuna kalaman Linda a wanshegarin da suka zama Attijarai.
Murmushi kawai ta yi ta fito daga motar. Idan da za ta samu gida mai kallon makarantar ma so take. Ko kaɗan ba ta fatan Abbati ya yi nesa da ita. Kai ita ba har haka ma take son rayuwar ƙarya ba. A yanzu haka da take sakata yawan canja mota abin na damunta, sai dai ba yadda za ta yi. Linda wata halitta ce guda da ba za ta taɓa manta kirkinta ba. Koda tana da manufar jawo ta rayuwarta, to ita fa kirkinta kawai take gani. Tana tuna sa’adda Abbati ke jin yunwa ta ɗau abincinta ta ba shi ba tare da nuna ƙyanƙyami. Kayya! Wannan wani abu ne da bai taɓa gushe mata ba. Tana son duk mai son Abbati, bata taɓa ma jin so irin wannan ba, ita fa ko tunawa ta yi wataran za ta mutu ta bar shi hawaye take ji, daga haka sai ciwon kai, wata irin ƙauna take wa yaron da bata ƙi ace ta maida shi ciki ba, ko haka duk Uwa ke ji kan Ɗan ta?
A jikinta take jin yadda idanuwan mutane ke lissafa kowane takunta, sharewa ta yi, inda sabo ya ci ace ta saba. In dai za ta fito daga mota mai tsada sai an zuba mata ido. Ta yiwu suna mamakin ganinta ƙarama, ba ta dace da irin ta ba. ‘Ta yiwu kuma suna mamakin kyawun ki ba.’ Wata zuciyar ta bata amsa.
“Ammy! Kin ji Uncle Slim ya ce na kusa mutuwa ko?”
Zantukan suka zarce cikin kunnuwanta da wani irin shiru, tamkar ɗaukewar ruwan sama cikin talatainin dare haka ta ji bugun zuciyarta ya dakata.
“Ammy wai idan na ƙara ƙarya ya ce zan mutu ne.”
Su suka fisgota daga inda ta shilla ta kafe shi da idanuwana tamkar me son hango wani ciwo a jikinsa.
“Shige mu tafi, ba za ka mutu yanzu ba. Dole ne gobe in ga Uncle ɗin nan naka. Ba na so yana yiwa yara kamar ka batun mutuwa.”
“Yauwa Ammy sai ki masa CupCakes ko? Kinga kullum yana cewa yana son Momin da ke mini cake.”
“Ina wanda na baka yau ka kai masa? “
“La na manta, gashi a jakata.”
“Okay, yau duka ba ka ma buɗe jakar ba ko, zan fa cire ka daga makarantar nan.”
“Sorry Ammy, an ba mu wasu Tbooks ɗin ne da su aka yi karatun.”
Ya furta yana riƙe kunnuwansa.
Zaro cake ɗin ta yi daga jakar, har za ta juya sai kuma ta riƙe hannunsa.
“Muje a kaiwa Uncle ɗin cake, Kar ya ce Ammynka ba ta cika alƙawari.”
“Yauwa Ammy, ya ce ma zai zo ya faɗa miki wai ba na iya drawing, ki nemo mini Lesson Teacher.”
“Bai da hankali, duk abin da ake biyansa a ce ya kasa koya maka zane?”
Ta furta ƙasa-ƙasa.
“Yauwa ga Uncle Slim ɗin can, kawo CupCakes din nasa na ba shi.” Ya furta yana zurawa da gudu ya riƙe hannun mutumin.
Ta ɗago da murmushi sa’ilin da tattausan gashin kan nata da ya daɗe da daina ganin ɗankwali ya rufe mata rabin fuskarta. A hankali tasa hannu ta janye gashin, manyan idanuwanta suka sauka akan fuskar da ba za ta taɓa mantawa ba kome nisan zamani. Murmushin ya tarwatse a saman fuskarta ya maye gurbi da wani irin tashin hankali da ba ta hango ƙarshensa.
Ji take kamar jijiyar da ke bada sakon tunani cikin kwalwalwarta ta katse, dan ita kanta Idan ta ce ga kalar tunanin da take yi to ta yi ƙarya. Gabaɗaya kanta ya gama ɗaurewa da ɗumbin mamaki maɗauɗaki. Dama wannan shi ne Uncle Slim ɗin da Abbati ke yawan ba ta labarinsa, shi ne mayen cake dinta, Shi ne me yawan cewa Abbati yana son Mum ɗinsa. Shi ne me koyawa Abbati karatun da duk bai gane ba, shi ne idan ba ta fito da wuri ba ke ɗaukar Abbatin ya kai mata har gida. Shi ne Abbati ke so har ranta ke ɓaci, saboda sometimes ko barci yake yana hirar Uncle Slim. Shekara biyu? Shekara biyu kwarara ba ta taɓa saninsa ba sai yau. A yau ɗin ma gashi ya zo mata a halittar da tafi tsana sama da Uwale a duka duniyarta. Halittar da idan za ta yi rantsuwa ta maya shi ne silar kome da ke faruwa da ita a yanzu da kuma wanda zai faru da ita a gaba. Bata taɓa zato ba, bata taɓa zaton akwai wata ƙaddara mai girman da za ta ƙara haɗa su ba. Ta ɗauka abin ya ƙare a tun ranar da Abbati ya buɗi ido da Mamuda a matsayin mahaifinsa, ta ɗauka abin ya ƙare a tun ranar da ya fatattake ta daga rayuwarsa. Ta ɗauka abin ya ƙare a tun ranar da zuciyarta ta azalzaleta da zaman Lagos maimakon Kano kusa da su inda zasu iya haɗuwa. Ta ɗauka abin ya ƙare a tun ranar da ta juyawa babu baya, ta juyawa duk wani ƙasƙanci baya. Ta manta girman mahaifi, ta manta darajar jininsa da ke kewaye da Abbati ta yiwu ma harda ita.
Ta nutsu tana kallon hanunsu da ke sakale da na juna, ta nutsu cikin idanuwan Abbati da bata hango kome sai ɗumbin soyayyarsa ga wannan mutumin da bai san mahaifinsa ba ne. Zuciyarta ta buga, bugun da idan da ƙarar kwana sai dai a ga gawarta. Ba za ta bari ba, ba za ta taɓa bari ya yi tasiri a rayuwar Abbati ba, ba zai ƙazanta mata yaro ba ko a yanzu ko a lokacin girmansa. Mummunan halinsa ba zai gogi ɗanta ba, haka ɗanta ba zai taɓa aikata irin kuskuren da mahaifinsa ya yi ba. Dan ba za ma ta bari su kusunci juna, ba za ta taɓa bari ba, sai dai har idan ba ta raye, kai wallahi! Da girman wanda ya busa mata rai ta yi rantsuwa, ko bayan ranta za ta bar wasiyya kar Abbati ya kusanci Sagir.
Dan haka ta taka da dukkan sauran ƙarfin da ya rage mata, ta miƙa zara-zaran yatsunta ta warto hannun Abbati daga sandararren hannunsa. Ta juya akan takunta mai ƙarfi tana barinsa, tana barinsa a daskare da buɗaɗɗen baki a hangame.
Saitin zuciyarsa ya dafe jin kamar za ta fasa kirjinsa ta fito. Ji ya yi kamar ba hannun yaron ta warce ba harda zuciyarsa ta haɗa ta tafi. Fati ce fa a gabansa a yanzu cikin sakannin da ba su fice hamsin ba, yarinyar da gabaɗaya tunaninsa ya ƙare a har abada ba zai ƙara ganinta ba. Ita ce ya ma lefin da bai taba gushewa cikin tunaninsa ba. Ita ce ta saka shi barin garin haihuwarsa da duk wani gatansa ya taho nan Lagos yana aikin koyar da yara, kawai dan ya samu nishaɗi. Ita ce a yau ta fito a uwar yaron da tun shigowarsa makarantar babu yaron da yake faranta masa ya manta dukkan damuwarsa ta duniya irinsa. Buɗe idanuwansa ya yi yana ƙara kallon yaron da ke ta waigensa yana masa dariya, wani hotansa a sa’adda yake ɗan shekara bakwai ya wanzu a bangon kwakwalwarsa zuwa cikin idanuwansa. A karo na farko ke nan da wani tunani ya ruga da gudu cikin kansa yana saita kansa a inda za a kula da shi.
‘Idan har ita ce uwar yaron to ina mahaifinsa, me ya sa yake kama da ni?’
“Uncle, Abba na ya mutu gurin yaƙi. Mamma ta ce babban Soja ne me riƙe ƙaton gun.”
Ya tuna kalaman yaron watarana da ya tsaya kansa saboda Assingment ɗinsu na drawing.
‘Abba Mamuda Murad.’
Ya jinjina sunan yana ƙara nazarin yadda Abba zai zama sunan yanka.
“Idan ka koma gida yau ka tambayi Mamanka real name ɗinka, me ya sa ta ɓoye maka har a makaranta?”
Aunty Juwy ta taɓa tura ni. Ammy ta ce banda wani suna sai Abba. Abbati ma take ce mini ana mini dariya sai na hana.”
Akwai wata alama mai girma anan. Akwai wani tunani da ke zauna masa.
Akwai wani abu a duhu.
Akwai wani aiki da ke gabansa.
Me ya haɗa Fati da Murad? Murad fa? Wani Attajiri da jaridar sati ba ta fita sai da sunansa a shafin Farko ko na Biyu. Kodayake ba zai tsaya yaudarar kansa ba, ko makaho ya shafa fuskarsa ya shafa ta yaron zai gane kamanninsa da shi.
Amma me ya sa da ta ganshi ta ja hannunsa suka tafi? Me take nufi? Ba dai za ta ce ba na shi ba ne tunda ko watannin cikin aka lissafa zuwa shekarun nan za su ba da daidai da na yaron.
“Wai shi Sagir ne ke da yaro, ko ya Hajiya za ta ji wannan daɗin.n “
Ya furta a fili yana shafa sumar kansa. Wata ƙaunar yaron ke ƙara mamayarsa, ga Fati ya gani. Yau duka daɗin duniyar kansa ya juyo. Dole gobe ya je ya ganta. Ya sani ba zai ƙara samun wata nutsuwa ba kuma har sai sun zama mallakinsa.
*
“Ya isa haka Ammy, ina ce ke kike cewa in bar sha, gashi ke yanzu tunda kika shigo kike bankawa kanki hayaƙin, shi ne maganin me ?”
“Linda ki gane me nake ji. Da zan iya canja fuskar Sagir da ke jikin ta Abbati da yanzu zan sa wuƙa na kankare shegiya. Yanzu nake nadamar zama na a Nijeriya, yanzu nake nadamar da ban yarda na ji zancenki mun koma Cyprus ɗin ba. Ko kinsan duk gudu na a duniya dan kar Abbati ya ga mahaifinsa ne ? Na taɓa faɗa miki babu daɗin duniyar da zai kankare tabon Sagir da ke gare ni? Na tsane shi, fiye da duk wani abu da kika sani mai muni a duniyar nan. Yadda nake jin tuƙuƙin zuciyata zan iya kashe shi, zan iya kashe shi idan ya ce yaro na nasa ne. Linda ki samar mini mafita kafin na ɗau mummunan matakin da nadama za ta biyo bayansa.” Ta furta tana cukurkuɗa gashin kanta kafin kuma ta rushe da kuka.”
A hankali ta dafa kafaɗunta tana jinjina kalmar kisa a ranta. Lalle abin ba ƙarami ba ne tunda har take iya furta kalmar nan.
“Ni banga abin tashin hankali anan ba. Sagir fa ba zai miki dole ba, kina wauta ne kawai, abinda ma bai san ɗan sa ba ne. Idan ma ya sanin shin yana da ikon karɓa ne? Har yanzu kin ƙi sakawa ranki cewar kuɗi babu irin darajar da ba za su siyo miki ba. Za ki iya siye Sagir da shi da danginsa kaf a cikin yini gud…”
“Kuɗi dai kuɗi dai, na ce miki Sagir dan ya gane Abbati ɗansa ne ko ya ce a ba shi Abbati shi ne tashin hankalina? A’a, ba Sagir nake tsoro ba, mahaifiyarsa nake tsoro. Kuɗi ba su sayen mutunci Linda, ba zan taɓa siyan Hajiya da su ba. Haka ba za ta roƙe ni abu ba na sa ƙafa na shure ba. Tunda Abbati ya haɗa mu ya riga ya haɗa, haka ita ce mace ta farko da na fara riƙewa a matsayin uwa. Ita ce wacce ta mai da ni mutum a lokacin da nake hali na ciwon hauka. A lokacin da har gudan jininta gudu na yake. To na tabbata Sagir ya rasa yadda zai yi da ni Hajiyar tasa zai dosa, kira ɗaya kuma za ta yi mini zan tattara na koma gabanta daga ni har Abbatin, shi ke nan mun zama ƙasan Sagir. Wannan ne ba na fata har abada, wannan ne dukkan damuwata da shi, ina roƙon Allah ya sa na iya butulci, da wallahi Hajiya zan fara butulcewa. Karki manta kuma, a yanzu babu ta hanyar da zan hukunta Sagir sai ta raba shi da gudan jininsa, irin wannan ranar nake fatan ta zo, sai dai ba na so ta zo da sigar da za ta raba ni da yaro na. Ba zan yafe ba Linda.”
“Finally! Nan nake so ki zo dama. Revenge za ki yi da Abbati ko? Kina so ki musguna masa yadda zai yi fatan da ma bai sanki ba ko? In dai wannan ne ina da hanya, ba sai an kashe kowa ba, sai dai rayuwaka su ɓaci. Yanzu dai ki dage kan ba ɗansa ba ne kome zai yi. In da hali ma Abbatin ya bar makarantar dan zuwan zai iya ƙara musu kusanci, haka shi ma zai iya ɗaukar yaron ya biyo mana ta inda ba mu za ta ba.
“Da kuwa ya yi kuskuren da sai ya gwammace bai zo duniya ba. Ba kuma har haka ba nake, so nake ya ƙare rayuwarsa a bakin ciki, ya tozarta a idanun duniya. So nake ɗan cikinsa ya sauke yatsunsa biyar a fuskarsa watarana!”
A tsorace ta kalli cikin idanuwanta. A karon farko da ta ji tsoron Faɗime ya mamayeta. Ba ta yafiya.