Skip to content
Part 23 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Da tsiwa ta buɗe ƙofar da zummar ko wane ya dame ta da matsa bell ɗin sai ta zuba masa rashin mutunci kafin ta saurare shi. Sai dai turus ta yi ganin mutumin da zuciyarta ba ta taɓa kuskuren tuna mata ba zai bibiyeta ba.

Ɗaure fuskar ta ƙara yi tana kallonsa a yatsine kafin ta buɗe baki.

“Mutum dai ko iya karatun Firamare gare shi ai ya kyautu a ce ya koyi latsa kararrawa sau ɗaya ya saurara Idan ba a buɗe ba ya ƙara. Amma kai garjejen ƙato da kai ka zo kana zuba mini yarinta a ƙofar gida. Idan ƙarar ke burgeka ka roƙe ni idan na fita kasuwa na siyo ma kacau-kacau ka dinga kaɗawa amma ba ƙofa ta. Ya aka yi? Me kake buƙata. Waye ma kai?”

“WHO is he!”

Ya furta da sigar da ya tabbatar a buɗe bakinta na farko zai gano duk wani abu da yake son ganowar. Sai dai ga mamakinsa ta shanye girman tambayar har tana haɗawa da murmushi tamkar wacce ta gama shiryawa hakan.

“Amma dai ban yi maka kalar turawa ba. Ko ka manta ko Primary ban yi ba balle ka ce zan koya a makaranta. Me kake so? Idan babu zan koma barcina ya fiye mini tsayuwa da kai anan kana baza mini warin rana.”

Ta furta da dakewar da ke ba shi mamaki har ya fara tunanin ko ba wannan mahaukaciyar yarinyar ba ce da ya sani wasu shekaru da suka gabata.

Sai dai shi ma shanye mamakinsa ya yi ya rungume hannuwansa a ƙirji yana kallon ɗan ƙaramin bakinta da ke ce masa yana warin rana. Dole ya shirya, dole ne ya shirya duk wani cin kashi da za ta yi masa kafin ya samu haɗin kanta. Laifi dai shi ya yi, shi kuma zai gyara kayansa.

“Kin ga dan Allah ki yi hakuri. Ban san me zance miki bayan haka ba. Amma ina so ki yarda na yi nadama, nadama irin wacce ba na fatan sake maimaita lefin. Ki yi hakuri dan Allah Fatima. Ki yafe mini. Wallahi kan hakan har yanzu ban dawo daidai da Hajiya ba. Saboda ciwon abinda na miki na baro can na dawo nan sai gashi kuma wani abin ya ƙara haɗa mu. Ki yarda da ni, ba zan ƙara ɓata miki ba ko ta wace siga.”

Ya ɗan yi shiru ganin ta nutsu tana saurararsa. Fuskarta na nuna kamar tausayinsa ya mamayeta. Dan haka ya ci gaba cike da kwarin gwiwa.

“Ina cikin da muka rabu kina ɗauke da….”

“Ka kore ni dai ina ɗauke da shi.”

Ta furta da murmushi tana tauna farcenta.

Wani maƙoƙo ne ya tsaya masa a makogwaro da ya tuna hakan. Ta ya ma zai manta ranar nan. Da ƙyar ya haɗiye yawu ya ɗora.

“Idan har shi ne wannan yaron da muke tare da shi a makaranta, Fati kiwa Allah ki faɗa mini. Na yi duk binciken da zanyi an tabbatar mini da ga ke sai shi kuke rayuwa anan. Babu wani da ya haɗa alaƙa da ku balle ki ce mini ga kakanninsa ko wasu danginsa. Murad kuma ance ɗansa ne ya haɗa ki da shi, kun yi zaman aminci shi ne kike amfani da sunansa a matsayin kariya ga ɗan ki. Ki faɗa mini ɗan mu ne shi banda wani iko kansa bare ki za ci zan karɓe shi ne. Karki hukunta ni ta hanyar nesanta ni da gudan jinina. Ko a zahiri ina ganin kamannina a jikin…”

Wata dariya da ta kwashe da ita ne tana rufe baki shi ya saka shi yin shiru yana kallonta.

“Oh Ni Teemah! In dai kana raye ba ka ƙare ganin abubuwan mamaki ba.” Ta furta cikin dariya idanuwanta na taruwa da ruwan hawaye.

“Ina cikin barci na ka zo ka saka ni nishaɗi. Yanzu kai saboda Allah aka ce ma na baro cikin unguwarku da wannan cikin ma sai ka yarda? Yo ai tun a bakin gate ɗin gidanku na yi tuntuɓe da wani ƙaton dutse da ya haddasa zubewar cikin. Ka tambayi Ilu maigadinku ta yiwu shi ya tsaftace gurin ba ka ankara da jinin ɗan naka da ya malale ba. Wannan yaron da kake gani shi ne ɗan mutumin da ya dubi maraici na ya ɗauke Ni a lokacin da nake kan ganiyar azabar fitar cikinka. Ya kuma aure ni ba tare da ya duba wacece Ni ba. Ya aure Ni a matsayin jahila marar kwalin Primary, Mamuda Murad.”

“Aure kuma?”

Ya furta ba tare da sanin sa’ar da kalmomin suka samar da kansu. Da alama a cikin labarin nata babu abin da ya da ke shi irin batun auren.

“Oh a binciken naka ba a faɗa maka ɗan Murad ɗin na aura ba? Eh aure fa, ko kana buƙatar ganin shaidar ɗaurin auren ?”

Ta furta a dake tana luma manyan idanuwanta cikin nasa.

“Sunansa Mamuda, sunan kuma ya maidawa ɗansa dan haka muke ce masa Abbati. Ya rasu bayan Shekaru biyar da haihuwar yaron. Dan haka ka bar tunanin Abbati na da wata alaƙa da kai. Ɗanka ba ka son shi ba ka ƙaunarsa tun yana ciki, ba kama fatan ya zo duniya. To Allah ya ji fatanka ya ɓare tun a ƙofar gidanku. Sai kuma me kake son ji?”

Wani yawu ya haɗiya da ƙyar yana lalubar idanuwanta. Ga mamakinsa cikin labarin banda kalmar aure babu wani abu da ya ji ya zauna masa.

“But me ya sa ranar da kika ganni da shi kika tsorata. Ƙarshe ma kika janye shi daga gare ni tamkar kina tsoron in gane wani abun, kuma daga ranar bai ƙara zuwa makarantar ba ?.”

Ba wannan tambayar ya so yi ba. Wacce ya so ɗin ta nutse a in da ya gaza tuna ta.

“Ni fa kasan me?”

Ta furta tana sosa tsinin hancinta.

“Yanzu haka sunanka ma ba lalle in iya tunawa ba, ka san mutum idan aka ce ma yana da taɓin hankali ko kuma ya taɓa taɓin hankali sai a hankali. Ka gode Allah ma da har na iya shaida fuskarka. To, ta yiwu ranar da kake zaton na janye yaron ciwon ne ya motsa. Wa ya sani ma ko wannan zungureriyar ƙeyar taka ce ta firgita ni har ka ga tsoron a fuskata. Amma karka damu, in dai Abbati ne jibi ma za ka ganshi a makarantar.”

Ta furta tana shigewa ciki ta buga masa ƙofar a fuskarsa. Sai dai kafin yasan abin yi ƙofar ta ƙara buɗewa, wannan karon fuskarta ɗauke da gargaɗi.

“Abu na ƙarshe karka kuskura ka ƙara takowa ƙofar gidan nan da sunan tambayata jininka. Alaƙar da ta haɗa Ni da kai ta mutu tun a matattakalar benen gidanku. Ina da damar da zansa a ɓatar mini da rayuwarka yanzu, a kuma rama mini duk wani abu da ka mini, amma ban yi hakan ba saboda darajar mutum biyun da ka fini saninsu. Dan haka kar ka ƙara tsayawa a gabana daga yau har gaban abada, tun kafin zuciya ta kwashe ni na aikata maka abinda za kai nadamar sani na!”

Ta furta tana juyawa, ta sake buga masa ƙofar da ƙarfinta ya saka shi yin baya taga-taga baki buɗe.

Ga mamakinsa sai yanzu tambayar da yake son yi mata ta dawo cikin tunaninsa.

‘Me ya sa yaron ke kama da shi?’

Ransa ya fara ɓaci yadda ‘yar tatsitsiya da ita ta tsaya gabansa tana karta masa gargaɗi. Ba zai gaji ba. Yanzu ne ma zai fara bibiyarta. Gabaɗayanta bai yarda da ita ba, ina ma ta samu wannan maƙudan kuɗaɗen da take facaka da su har ta iya zama a wannan unguwar da tafi kowacce unguwa tsada a Lagos. Yanzu ba wannan ne gabansa ba. Wannan yaron mai idanuwa irin nasa yake son sanin wanene shi?Ya kula so take ta yi kuskuren da idan ya gano gaskiya zai iya raba ta da shi har abada ya kai shi in da ba za ta ƙara ganinsa ba. Sai dai ba ya son ta kai su ga haka, ba ya son ya sake ɓata mata. Yana sonta, yana son ƙarasa sauran rayuwarsa da ita.

***** *****
A jikin ƙofar ta jingina bayanta tana dafe zuciyarta da ke ƙoƙarin fasa ƙirjinta ta fito. Ba ƙaramin mamakin ƙoƙarinta ta yi ba. Sai yanzu take jin sassanyan gumin na kwarara har cikin ɗan banten ta. Sagir da duk wani ƙarfinsa ya zo, ashe kwana biyun da ta ji shiru bincike yake yi a kanta. A cikin idanuwansa take hango rashin yardarsa da ita. Ba duka zantukanta ba ne suka shige sa. Dole ne ta ɗau mataki idan ba haka ba ƙwabarta za ta yi ruwa. Idan ta kai shi ƙarshe ya sace mata yaro ita ce a ciki. Ba da wannan salon za ta yaƙe shi ba. Gobe Abbati zai je makaranta, za ta tabbatar masa ba tsoro ya hana ta tura shi ba.

Agogo falon ta duba, ƙarfe tara da rabi na safe yanzu. Da hanzari ta ƙarasa ga wayarta ta ɗauko tana kiran Kamfaninsu na Kaduna, ana ɗagawa ta fara magana.

“Ammy na yi mafarki na mutu.”

Wayar ta suɓuce daga hannunta zuwa ƙasa, ta waigo tana sauke idanuwanta a kansa, yana tsaye sai mutstsika ido yake alamun sannan ya tashi daga barci.

“Abbati! Ban hana ka maganar mutuwa ba?”

“Allah ko Ammy ai kin hanani ƙarya ko? Harda ma Uncle Slim a mafarkin yana mini bye-bye.”

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel! Abbati yaushe kasan mafarki? Yaushe shekarun ka suka isa sanin mafarki? Da Allah catoon din jiya da ka kalla ne kake gani kamar mafarki.”

“Ammy amma ai ana mutuwa ko? Kince Abbana ma mutuwa ya tafi, ni ma gunsa zanje ko? Ammy jiya ma a MBC 3 aka ce mini zan mutu.”

Ai sai ta zabura zuwa gabansa ta finciki hannunsa suka yi Toilet. Gabanta ke wani irin matsanancin bugu. Shin me ke faruwa ne?

***** *****
Ƙarfe Tara Da Rabi daidai ya wanzu a bakin gate ɗin. Har tuntuɓe yake yi tsabar sauri. So yake kawai ya isa ga yaron ya ɗauke shi zuwa ga Likitansa a gwada DNA nasu. Zai dai kawo ƙarshen ƙaryar Fati yau.

“Idan aka tabbatar mini da jinina ne shi daga nan Kano zan yi da shi. Idan ta matsu na san za ta zo. Tana zuwa sai na roƙe ta ta aure ni. Mu yi rayuwarmu cikin amin…”

Kalaman suka watse a iska sa’ilin da ya gama tura ƙofar office ɗin, idanuwansa suka sauka kan Abbati da ke sandare a saman teburinsa, gefensa tarin takardun yara ne.

“Abba! Ya furta da ƙaraji yana ƙarasawa jikin yaron bayan ya yi watsi da kayan hannunsa. Jijjiga shi ya hau yi babu wani alamun rai a jikinsa. Cikin rashin hayyaci ya fara waige-waigen neman ruwa, can gefe ya ga gorar ruwan ya ɗauko yana yayyafa masa amma ba ko gizau. Watsi ya yi da tarkacen teburin yana ƙoƙarin ɗaga yaron a sannan idanuwansa suka yi arba da sirinjin. Injecting yaron aka yi, Allurar guba aka yi masa dan a kashe shi, an kuma ci nasara. Ai da baya da baya ya fara yi kamar wanda ya ga baƙin kumurci har sai da ya haɗu da bangon office din. Sai yanzu ya kula da kumfar da ke fita ta bakinsa.

‘Kar ka taɓa kome, this is a murder case.’

Wata zuciyar ta ankarar da shi.

‘Call The Police!’

Ya ji kuwwar hakan a cikin kansa.

Da hanzari ya isa ga wayar cikin office ɗin. Rinni biyu suka ɗaga.

“Yanzu na tarda gawar yaro a office ɗi na.”

Idan za a yanka shi ba zai ce ga yadda ya tsara jumlar ba.

“Eh, anan makarantar Little Angels.”

“Ina zan sani, zuwa na ke nan fa.”

“To Allah ya sa ba kai ka kashe shi ba ka kira mu don ka raina mana hankali.”

Zantukan da suka afka cikin kunnuwansa ke nan Ya rufe idanuwansa da ƙarfi sa’ilin da ya tuna bai haɗu da kowa ba a yayin da zai shigo cikin makarantar, hatta Maigadi kuwa ba zai bada shaidar ganinsa ba.
‘Tirƙashi!’

<< Fadime 22Fadime 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.