"Ba ni na kashe shi ba! Wallahi ba Ni ba ne! Haka na zo na same shi kwance a ofis din! Sagir ya furta da ƙaraji yana kallon murɗaɗɗen baƙin ɗan sandan da ke tsaye a gabansa. Awansu biyu da zuwa suna ta gwaje-gwajensu, suna ƙoƙarin saka shi ya amsa lefin da bai ji ba, bai gani ba."
"Babu mai lefin da ke amsa lefinsa a karon farko..." Ya furta yana ɗora karan sigari a saman manyan laɓɓansa, ya kunna ya mata kyakkyawar zuƙa, ya ɗago yana mai fesar da hayaƙin a. . .