Skip to content
Part 25 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

A cikin kwana biyu kawai Sagir ya yi wani irin mugun ɗashewa da figewa. Babu abin da ke cikin idanuwansa sai mummunan tashin hankalin da ke gabansa. Ga wani maƙoƙon baƙin cikin mutuwar gudan jininsa da ya tsaya masa a maƙogwaro. Yanzu har ta kai ko ya ya, ya rufe idanuwansa yaron yake gani yana masa dariya.

Numfashi ya ja mai zafi yana daɗa ƙare masa kallo, mamaki yake, kamar yadda Oga da duk wani da ke gun bai yarda da shi ba. Haka yake ganin rashin yardar ɓaro-ɓaro a fuskar Yayansa. Kamar ba zai daɗa magana ba sai kuma ya nisa. 

“Da ciwo, da ciwo a ce kai kaɗai ɗinma da ka rage mini ka gaza yarda da ni. Ta ya ya zan sakawa raina Hajiya ma za ta yarda da ni?  Amma zan maka rantsuwa, rantsuwa irin wacce ko zan mutu ba zan ƙara maimaita irinta ba kan wannan batun. Wallahi summa tallahi, na rantse da sarkin da ya busa mini rai ba ni na kashe yaron da ake ikirarin ɗa na ba ne, ba ni ba ne! Ban san shi ba sai a makarantar, ban taɓa ganinsa a cikin Ofis ɗi na ba sai ranar da na tarda gawarsa a gun!”  Ya furta, a saman fuskarsa zahirin ɓacin ran da yake ciki ke daɗa bayyana.

“To me ya sa hoton yatsunka ya fito a sirinjin da aka masa Allurar? Ta ya ya haka za ta faru idan har ba ka taɓa shi ba? Na’ura ba ta ƙarya Sagiru.”

“Amma ai tana karɓar makirci ko, ana iya siye masu gwajin su canja, ana iya siyan kome Yaya…”

Ya furta yana danne abin da ke daɗa ta so masa.

“Ban sani ba, ni ma tambayar da na yi musu kenan. Ta ya ya ni da nake gida, zan  taso takanas, na zo makaranta na samu yaro, na kai shi cikin ofis ɗi na na kashe, na bar abinda na yi kisan a gun, na kuma kira ‘Yan Sanda na sanar musu da hakan? Shin Yaya wane hankali ne wai zai ɗauki wannan? Ko ka san a bayan makarantar, ɗan nesa kaɗan, akwai ƙaton rami me cike da ruwan da baya gudana (kududdufi)? To da ace ni ne na kashe shi, ina da wayon da zan ƙudundune shi na je na jefa shi a cikin ramin nan,  ko na kai shi in da ba zai taɓa bayyana ba har abada, kai ina da wayon da zan iya ƙona gawar na zuba tokar a masan gidana. Amma ban yi hakan ba, ba dan yaron yana jinina ba, ba dan ban kashe ba, ba kuma dan ba zan iya ɓoye gawar ba gudun a zargeni, sai domin ni ma ina son sanin wanda ya yi kisan, ina son sanin wanda ya datse guntuwar alaƙar da ke tsakanina da Fati. Wallahi Ya…”

“Ya isa haka Sagir, ya isa, na yarda!”

Yaya ya furta yana dafa hannuwansa da ke jikin ƙarfen.

“Na yarda da kai, tun a karon farko na yarda da kai. Sai dai abin ne da ɗaure kai, matuƙar ɗaurewa. Wane irin maƙiyi gare ka a duniya da zai maka wannan tozarcin, ya zama silar ɓata ran rayuka da yawa. Kasan tun ranar Hajiya ke kwance asibiti musamman da ta ji cewar Fatiman ta ce uwar yaron. Jininta ne.  Ta ya ya za mu goge wannan lamarin? Wannan batun da kake kawowa mu a idon mu ne yake karɓaɓɓe, a idon ‘Yan Sanda duk gani suke hakan zai iya faruwa idan kana son ɓoye lefinka…”

“Amma ko giyar wake na sha ba zan kashe yaro ƙarami ba. Ba har haka zaman Turan ya ɓata ni ba, ba har haka zan tozarta su Hajiya ba. Ina son Fati, ina son ku, ina son yaron a tun ranar da na fara ɗora ido na a kansa, shin me zai sa na kashe gudan jinina? Me zai sa ina son kasancewa da uwarsa zan burmawa kaina wuƙa irin haka? Kai! Ba zan yafe ba, ko waye silar tozartani, ba zan taɓa yafe masa ba. Yaya, dan ALLAH ka taimaka mini, kai kaɗai gare ni da za ka iya tsayawa kan wannan lamarin. Ka fi kowa sanin babu a abinda na taka na matakin rayuwa, babu abinda zan barwa baya. Ba na so ƙarshen ya zama haka, ba na so!”

Shiru ya yi yana jin sanyin abin a ransa. A karon farko da ya ji ruwan hawayen na ambaliya a fuskarsa har cikin bakinsa. Ba kowa ne zai gane  ciwonsa ba. Ko kai ne ka dafa abincin da ya yi silar saka yaranka ciwo, za ka ɗanɗana kuɗarka a yayin da ka fara ganinsu suna rera kukan ciwon. Balle shi da mutuwa ce gabaɗaya ta raba su a lokacin da yake da burin ba shi dukkan kulawarsa da bai samu ba, ta kuma bar masa alhakin zuwanta. Shin ina zai saka ransa?

“Zan yi, zan yi duk abinda nasan zan iya. Ko kai ne ka aikata sai inda ƙarfina ya ƙare, balle kuma ba kai ba ne. Ba yadda zan yi da kai Sagir, dole kai nawa ne.”

“Yaya ina su Fat…”

Sai kuma ya yi  shiru kamar yana jin nauyin tambayar. Sai dai azahiri idanuwansa na kan ɗan sandan da ke gefensu, motsi kaɗan yana duba agogo.

“An sallame ta daga asibitin tana gida, sai dai, sai ka yi magana sau goma ba ta amsa guda ɗaya ba. Ni kam tana gani na ma ta bar gurin, da ƙyar abokiyar zamanta ta sakata amsa gaisuwata. Sai munyi haƙuri, lefin da yawa Sagir, bantaɓa jin ina kunyar wata halitta ba irin yadda nake jin nauyinta a yanzun.”

“Yaron fa?”

“An binne shi tun jiya, ban…”

“What! Me ya sa za su ba da shi da wuri haka?”

Ya furta muryarsa na rawa.

“Ban gane ba, to aje gawar za su yi da suna ado da ita? Ni na ji daɗi da aka ba da shi ai, yaro fa ya mutu Sagir, me kake tunani kuma?”

Shiru ya yi yana daɗa jin abin bai kwanta masa ba, me ya sa za a ba da gawar da wuri daga yin bincike ɗaya, me suke nufi da hakan? Ai bai amsa ba, ya san kuwa kaf duniya babu Alƙalin da zai ɗaure shi idan ba amsa lefin ya yi ba ko kuwa wasu hujjojin su tabbatar da lefin.

“Lokaci ya yi fa, dan dai fa Ni ne, ban da haka ba a yarda a daɗe haka ana zantawa da masu irin wannan lefin. Yaronsa fa ya kashe.”

Ji ya yi kamar ya ƙudundumo ashar ya narka masa. Bai ga dalilin da za ai ta nanata masa ya yi kisa ba. Sai dai ga mamakinsa ya gaza tuna da wane yare ashar din ya kamata ya fito.

“Two minute kawai officer! Zan ƙara maka wani abun.”

“Ɗaya da Zero huɗu idan ka gane, Ka yi sauri kuma  Oga ya kusa shigowa.”

“Shi kenan Sagir Allah yana tare da mu. Da yardar Allah kome zai ƙare, babu abinda bai da ƙarshe, in sha Allahu ƙarshen wannan alkhairi ne. Zan bincika duk wani lawyer da ya amsa sunansa lawyer don ya tsaya kan wannan lamarin. Ko ka na da wani da ka sani, ka ga fa gobe ne shiga kotun, ban san me ya sa suke ta gaggawa ba.”

Zahiri ta bayyana a bangon zuciyarsa. Zuby Cingam. Barista ce da ta amsa sunanta. Ita ce halitta ta biyu da ba zai taɓa mantata ba. Ba dan yana jinta a rai ba, sai dan ƙaunar da ta gwada masa ta ƙarshen hauka. Saboda shi  ta tafi America karatu, saboda shi ta bar garinta Sokoto, ta taho nan Lagos ta buɗe Chamber ɗinta. Shegen na ci gare ta irin wanda tun suna makaranta aka saka mata Cingam ɗinsa, har sunan ya bita. Da duk satin duniya sai ta zo makarantar da yake, ko ta je gidansa. Bai taɓa tsanar wata halitta irinta ba, ita kuma ba ta taɓa san wani irinsa ba. Wulaƙancin duniyar nan ba wanda bai mata ba. Akwai ranar da ta kamo hannunsa zuciya ta kwashe shi ya yarfa mata mari ya tofa mata yawu a gajeriyar fuskarta, amma ta ɗau gyalenta ta goge, a ranar ya fara ganin kwallarta, daga ranar kuma bai ƙara ganinta ba. Yau wata biyu kenan. Ashe dai akwai ranar da za ta zo da zai hango amfaninta, ashe dai kowane bawa yana da ranarsa. Allah shaidarsa, ko fuskarta baya son gani, ba wai don muninta ba, ko tsayinta da ya fi na wada da kaɗan. A’a, shi kawai ya tsaneta, tsana ta haƙiƙa, dan haka da gaggawa ya kauda tunanin ya ma san wata lawyer, kai baya ma tunanin za ta iya da wannan case ɗin. Dan haka kawai ya kaɗawa Yaya kai, alamun babu.

***** *****

Tun ƙarfe goma na safe da ya baro gurin Sagir bai zauna ba, duk inda ya san akwai wani babban Lawyer can ya nufa. Sai dai fa kamar sun haɗa ba ki. Mutum uku da ya gani kai tsaye suka ce ba za su yi ba, ba cin lokaci ya ƙure, an riga da an fitar da shaidar shi ya aikata. To me ake so su ce? Mutum biyu kuwa da ya gani sun yanka masa farashin da idan ba gidansu za su tada ba, ba su da wannan kuɗin a ajiye. Million Goma? A tashin farko sai ya ba da kafin alƙalami na Million Bakwai. Shin lawyer hauka ne? To a cewarsu dai case ɗin mai tsauri ne duk ta inda ba a za ta ba, saboda shaidar farko ta riga da ta fita. Idan ana son murɗa wannan lamarin dole ne a aje maƙudan kuɗaɗen da zai iya jirkita sakamakon da mutanen da suka fidda sakamakon. Na ƙarshen kuwa da yake da dukkan wani buri kansa, kasancewarsa abokin karatunsa, yana jin sa’adda yake sanarwa Sakateriyarsa ace masa baya nan. Hmm! Bai ga lefinsa ba, duk wanda ya karanta shafin farko na jaridar da ta fita ranar zai ga abinda zai hana shi shiga lamarin ko da yana da niyya. WANI FUSATACCEN UBA YA KASHE ƊAN SA A MAKARANTA SABODA SHEGE NE. Bai ga lefinsa ba!

Zuwa ƙarfe goman dare duk wani fatansa ya ƙare. Abin kuma ya daina ba shi mamaki ya koma ba shi tsoro. Har hangowa yake gobe shi ke nan za a raba su da Sagir, za a kai shi gurin da ba zai taɓa dawowa gare su ba. Dafe kansa ya yi yana mai tsirawa yatsun ƙafarsa ido kamar mai lissafa jiyoyin da ke kewaye da su. A zahiri da baɗini mafita ɗaya ce yake ganin za ta fisshe su. Ita ce ya je ya samu Fati ya roƙe ta arziƙin ta ara musu kuɗin da za su ɗau lawyer tunda ya san ta daɗe da fin ƙarfinsu. Tun isowarsa cikin garin ya samu labarin kome game da ita. Sai dai fa ba kwakwalwarsa ce kaɗai ba ta gamsu da hakan ba, hatta fatar jikinsa rawa take tana nuna masa wannan ba mafita ba ce, wannan rashin hankali ne. Ta ya ya za ka je gurin wacce a ka kashewa yaro(uwa), ka roƙe ta wai ta ara maka kuɗin da za ka kare wanda ake zargin ya yi kisan? Ai daidai yake da ka je ka samu riƙaƙƙen mahaukaci, ka tsaya a tsayinsa da ya ƙere naka, ka tambaye shi shin ko sunansa mahaukaci? Hmm! Danƙe katifar ya yi da ƙarfi yana runtse idanuwansa. Ji yake kamar yana zaune a saman dutse mai tsini. Sagir yake tunowa a duk wani bugun zuciyarsa, yana can cikin duhu, a dandaryar ƙasa da ko albarkar tabarma babu, cikin zafi matsananci da yunwa. Tuna hakan ya saka shi miƙewa da sauri yana kallon fankar da ke juyawa a ɗakin, da kuma ACn da ke ba shi sanyi. A hankali ya ƙarasa gare su ya kashe, ya ƙarasa ga daddumar da ke gefe, ya shimfiɗe ta ya kwanta yana mai matashi da hannunsa. Ya ƙara runtse idanuwansa a karo na ba adadi yana mai ji a cikin ransa tunda har Sagir ke cikin wancan yanayin, to shi ma kuwa ba zai ƙara kwanciya da fanka ba balle AC, ba zai ƙara kwanciya a kan gado ko katifa ba, ba zai ƙara matashi da kome ba sai hannunsa. Daga nan har zuwa abinda Allah ya yi!

<< Fadime 24Fadime 26 >>

1 thought on “Fadime 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×