Skip to content
Part 27 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Kwana Biyu Da Suka Gabata

“Surukin naki ne da na yi alƙawarin kawo miki a duk sa’adda na koma. Gashi nan ya zo gare ki yau, zai kuma dawwama a gurinki har mu ga abinda gobe za ta haifar.”

Kallon rashin fahimta ta masa tana kallon ɗan matashin yaron.

“Yanzu wannan jikan Falmata ne? Allah mai iko, ka ga fa babu ta inda ya kwaso dangi.”

“Ikon Allah kenan. Idan kika ga Babansa kuma ance ko yatsansa bai bari ba…”

“Bai jin kwari Umma a masa wanka, ga magungunansa ya sha. Wannan yaron ɗan amana ne, ko fita daga nan ba a so ya yi. Ni ma yanzu fita zanyi na bincika idan da makarantar kwana ta yara can za a kai shi, sai a hankalina ya fi kwanciya.”

“Yaya!” Ta kira shi a kausashe tana kallon cikin idanuwansa.

“Me ke faruwa ne? Me ya sa ka kawo yaro hutu za ka ce kuma kar ya fita ? Ka faɗa mini gaskiya fa na san halinka da ganganci, ina uwar tasa? Wai ma ba neman yardar aurenta ka ce ka tafi ba? Auren ne ba ta yi ta ba ka kyautar yaro ko kuwa?”

Shiru ya yi yana shafa ƙeyarsa. Tambayar da yake jira kenan dama. Fiye da awanni uku da suka gabata ya gama tsara amsarta.

“Babu kome fa Umma! Matsala aka samu ne ita da uban yaron. Yau fin sati yake binta sai ta ba shi yaron, to ƙoƙarin ƙwace shi yake yi da ƙarfin tuwo, ko ma ya sace shi, shi ne ta tsorata, ta kira ni ta ce na kawo shi gurinki ki ajiye shi. Ta dinga zuwa ganinsa jefi-jefi.”

“Kai ka ji ɗan gwafar uban mutum. Da shi yana son ɗan nasa ya bari ta haife shi a titi?Ina ba shi ya kore ta da cikin ba. Kai jama’a! Yanzu dan yarinya ba ta da iyaye da wani tsayayye sai a nemi yi mata ƙarfa-ƙarfa. Kai ma Yaya na ce ka ɗaukota ta dawo nan gabana ta zauna kun ƙi, sai aikin ce mini ai idonka na kanta, ina ido anan ga wani nan yana mata sunturi a gida zai ta da mata da hankali har an zo da ɓoye-ɓoye. To dan gwafar ubansa ka faɗa masa yaro yana nan guri na, ya zo ya ƙwata idan ya haifu cikin uwatai!”

“A’a Umma, ai fa kome ma ya ƙare tunda an kawo miki shi. Daga yau ba zai ƙara jinsa ba kuma. Ita dama burinta kar ma yaron ya san shi a matsayin uba ba. To matsalar shi ne malamin yaron ne ma a makaranta. Har ma ya fara ɗaukar shi yana fita da shi yawo, shaƙuwa ta fara ƙulluwa a tsakaninsu.”

‘Ta isa haka ƙaryar.’

Zuciyarsa ta tunatar da shi. Haka ne kam ya isa. Uwace a gabansa, har kuwa a tsokar da ke tsakanin ƙirjinsa baya jin daɗin ɓoye mata gaskiyar da ya yi. To amma ya zai yi, tunda har ya yadda da wannan ɗanyen aikin, ai kuma ta faru ta ƙare mai Akuya ya sayi Kura, sai dai a yi ƙoƙarin yaƙi da duk wani abu da zai ruguza lamarin. Mamaki ɗaya ne a ransa, har a yanzu da ya baro Lagos ya taho nan Maƙarfi cikin gidansu, baya jin ko ɗigon nadama na mamayarsa kan abin da ya yi. Shi fa kan Fati ya yarda ya sai da ransa, kamar yadda ya siyar a yanzun. Wani abu ne suka aikata da fashewarsa daidai yake da a ɗauki gyatumarsa zuwa ofishin ‘Yan Sanda, a tuhumeta da goyon bayan ƙazafin kisa. Ba ta ji ba, ba ta gani ba. Sai dai baya jin hakan zai faru, tunda kawo i yanzu bai ji nadama ba, bai ji wani abu na damuwa ba, kwakwalwarsa da zuciyarsa sun ba shi tabbacin daidai ya yi, haka taimako ne ya yi. Idan har Fatinsa za ta yi murmushi kan abinda ya yi, to zai roƙi Allah ya kawo wasu hanyoyin irin waɗannan da zai zama silar farin cikinta. Abu ɗaya ne ya saka shi yarda da shirin, abu ɗayan da bai taɓa zaton zai iya irinsa ba, shi ne soyayyarta. Gudun kar ya ƙara rasata a bayan ya shafe shekaru bakwai yana jinyar sonta, yana neman inda zai ganta. To wace wauta ce a yanzu za ta saka shi ƙara yarda da wani ya shiga rayuwarta, wanin da shi ne ya dasa katangar baƙin ƙarfe a tsakaninsu da ta hana shi samunta har kawo i yanzu. Wanin da ya tabbata idan ya matsawa Fati ya san za ta iya manta baya ta ba shi dama ko dan yaronta ya tashi da cikakken gata. Ya santa sarai, ya san kuma burinta na duniya. Ya sani ko dan Abbati ya girma ba tare da wani ya goranta masa rashin uba ba, za ta iya yadda ta aure shi dan su zama a muhalli guda. To shi fa wannan ne ba zai taɓa bari ya faru ba idan har akwai sauran bugu na zuciyarsa a tare da shi.
Ban da ƙaddara, bai ga mahaɗarsa da garin Legas ba da zai je can har ya haɗu da ita, bil aƙas ba fa aiki ya kai shi ba, ɗaurin aure ne suka je na Abokinsu, ba fa bikin ta je ba. A gidan Mai da suka tsaya domin cika motarsu ya ganta. Ba fa fitowa ya yi daga motar ba, murya kawai ya ji irin ta ta tana bada umarnin a cika mata motarta. A jikinsa ya ji ita ce, a cikin mafarkinsa ya sha ganin inuwarta yana shaida ta, ko da ya buɗe motar ya fito zuciyarsa ba ta masa ƙarya ba kamar yadda mafarkinsa bai masa ƙarya kan shaida inuwarta ba. Itan ce dai a gabansa cikin kyakkyawar surar da har gobe ba ta bar fitowa a saman fatar idanuwansa ba tana masa gizo, to har ma ta shaida shi, har ta iso gabansa cikin farin ciki tana mai riƙo hannayensa. Idan har ba wani lamari ne mai girma zai faru a tsakaninsu ba wanda baya tababa aure ne. Shin mene ne haɗin biri da gada? Dan haka kome zai faru ba zai bari ya sake rasata ba ko da kuwa za a bashi zaɓi tsakanin numfashinsa guda ɗaya tal! Da ya rage masa a duniya da talaucin duka duniyar, zai zaɓi talaucin ne a kan dai shi ya rasata. Ba kuma lefi ba ne dan ya yiwa zuciyarsa abinda take so ta hanyar aikata ba daidai ba. Kowane mutum da irin nasa son rai, akwai kuma ta inda yake gazawa. Ya yarda irin tasa gazawar kenan. Akan sonta kuwa a kira shi mahaukaci ma, ko a rigar jikinsa ba zai dame shi ba. Umma ma sai dai ta yi haƙuri. Lefi ne ya riga da ya yi.

Wani yar! Ya ji a jikinsa dan haka da sauri ya waiga jin kamar akwai wani tsaye a zaurensu yana leƙensa. Bai saurari abinda Umma ke cewa ba ya ruga da gudu zuwa zauren sai dai wayam! Bai ga kowa ba, babu ma wata alama da ke nuna wani ya tsaya a gun. Zuciyarsa ta buga da ƙarfi da ta ƙara ba shi tabbacin tabbas akwai wanda ke bibiyarsa. Ba wai wannan ne na farko da ya ji a jikinsa ba. Tun a ranar da ya shiga Lagos ya haɗu da ita kan maganar yaron, har zuwa lokacin da aka ba su yaron a matsayin gawa, har a sa’adda ya tone kabarin ya ɗauko shi ya masa Allurar da ta farfaɗo da shi, yana ji a jikinsa wani na bibiyarsa. Idan kuma ba idanunsa ke zaginsa ba, ya kula da wata jar mota da duk inda ya shiga zai ga irinta sak! A sa’adda ya shigo Maƙarfi ya ɗauka shi kenan kowaye ma zai haƙura, tunda tafiyar da ke tsakanin Lagos da Maƙarfi ba kaɗan ba ce da za a juri binsa, haka yana sane ya dinga caccanja hanya, ya kuma dinga tsayawa a duk wani masallaci ko ‘yar kasuwa da ke kan hanya, sai dai a yanzu tunaninsa ya canja da ya ƙara jin irin wannan yanayin. Tabbas akwai wanda ke bibiyarsu ya kuma san duk sirrinsu, sai dai wanene? Me yake so gare su? Abinda ya kamata ya fara ankara da shi kenan, idan har wani zai gane abinda suka shirya babu amfani fa, daidai yake da ace sunyi shuka a idon makwarwa, tunda dai za ta bi ne duk ta tsattsage abinda aka dasan. Dole ya gano ko waye, dole ya kiyaye duk wani abu da zai rusa musu shiri. Dole ya ɗauke Abbati zuwa inda wani bai isa ya je ya ganshi ba. Tabbas a gobe ma zai kai shi makarantar. Bai yarda da kowa ba anan! Kowa na nufin har ‘yar gyatumarsa.

*****
Tsaya ki ji abinda ya faru.

Tun lokacin da na ji kina cewa Sagir, Abbati zai je makarantar na ƙuduri niyyar hakan. Kuma dama ai na ce miki ina da mafita, to wannan ce kawai hanyar da nake ganin mafitar a cikinta. Sagir zai za ci ɗansa ya mutu, kuma shi ne sanadin mutuwar, shin ko akwai wani tozarci da za a masa da zai ya fi wannan?

To fitar da na ce miki na yi zanje saloon ba can na je ba. Kai tsaye gurin Dr. Peter na je, in da kuma na taki sa’a a ranar zai bar ƙasar nan, ba kuma zai komo cikinta ba sai bayan shekaru biyu. Tambaya guda ce na masa, ko akwai wata Allura ko kwaya da ake bawa yaro da za ta mai da shi matacce. Ya ce da akwai Anesthesia wacce ake yi a kowane irin Surgery. Na tambaye shi ko tana kai wa awa 24, ya ce a’a, sai dai idan ta Neurosurgery (Tiyatar Ƙwaƙwalwa) ita ce za ta kai waɗannan sa’o’in. To a lokacin ne fa na roƙe shi da ya ba ni Allurar wadda ya kira da Xylocaine zan yiwa yaro da bai gaza shekaru 8 ba, shi kuma ya ce a’a, a dokance ba a bada ita. Ya fara lissafo mini illolinta na dakatar da shi da abinda ya ɓata lissafinsa na lokacin. Kamar yadda na ce miki kuɗi na iya samar miki da ko menene, to a lokacin ma ina aje masa check ɗin dubu ɗari Takwas (800) ya tashi ya fita.

Bayan mintuna goma ya dawo mini da duk abinda na buƙata, har da magungunan da za a bawa yaron bayan ya farfaɗo. A bayan na fito ne to na kira Yayanki na nemi da ya zo ya biyo jirgi kawai.

Bayan ya iso ne na masa bayanin duk abinda na shirya, na kuma faɗa masa nasa aikin da zai yi. Da fari ya ce a’a, saboda me za a wahalar da yaron, idan kuma wani abu ya faru da shi fa. To amma da na ƙara jaddada masa halin da kike ciki na tsoron kar Sagir ya sace miki yaro, sai ya amince.

Ammy, Yaya na cikin mutanen da samun kamarsa a masoya sai an shirya. Saboda ƙaunarki ya yarda ya sai da ransa, ya aikata koma menene. Shi da kansa ya je gidan Sagir ya ɗauki motarsa ya shiga cikin makarantar, ya jira ni har na zo na danƙa masa Abbati ya masa Allurar. Da shi aka tafi gurin gwada gangar jikin inda anan ma sai da muka kashe makudai kafin mu samu a ba mu gawar a lokacin. Ba mu so har abin ya kai da binnewa ba, sai dai kasancewar lamarin akwai ‘yan sanda, suna kuma bibiye da mu, dole tasa aka yi jana’iza. In da Yaya ya jira kowa ya bar maƙabarta ya haƙe kabarin ya fito da shi a lokacin da saura mintuna goma awanni 24 su cika. To daga nan ne ya wuce da shi kai tsaye zuwa Maƙarfi, na ce ya danƙa shi hannun Umma ya kuma saka shi makarantar kwana acan har zuwa lokacin da kome zai natsa, za a manta da lamarin Sagir.

Sauke jaridar ta yi daga gaban idanuwanta ta maida su ga Linda.

“Amma ba ki yi dabara ba, ba har haka nake nufi ba. Yana da ‘yan uwa da iyaye da nake ganin girmansu. Da ace babu, da tuni ni na fara aikata irin hakan, kai da tuni ma baki san shi ba. Ba zan so zama silar zubar hawayensu ba tunda suma ba su zama silar nawa ba, kai! Ni kam na shiga uku! Yayansa ya karya mini zuciya. Anya kuwa zan iya?”

“Za ki iya. Sai dai kuma idan akwai wani abu nasa a ranki. Na ɗauka mun ƙare maganar nan. Kamar abin kirki ke shirin zama na tsiya? Na ɗauka haka kawai zan miki ki gane muhimmancinki a rayuwata. Na sha ke kika ce mini kina so ki ga ya tozarta? Na sha ke kika ce mini kina so ki masa abin da har abada ba zai manta ba. “

“Sai na ce miki so nake a kashe shi? Sai na ce miki so nake na zama silar zubar hawayen mahaifiyarsa, sai na ce mi ki so nake na ga rabin familynsu a Asibiti?”

“Ba kashe shi na yi ba ai, idan har bai amsa lefin ba ba za a kashe shi ba, ni na yi ne dan ya ƙarasa rayuwarsa a prison. Akwai yadda zan canja lamuran idan kinso, amma zama gidan kaso dole ne gare shi. Kina da rauni Ammy, ban taɓa zaton za ki ji ciwon abin arzikin da na yi ba. Ni fa dan ki samu sa’ida na yi, dan ki manta da shi da abinda ya miki na yi. Kuma sai da kika tabbatar mini kina son ramawa, kina son a masa abinda zai tozarta, to ai yanzu rage miki hanya na yi.”

“Amma shi na ce ba iyayensa ba ko?”

“To ai shi ɗin aka yiwa, yasan da iyayen nasa ya ƙeta darajarsu ya haiƙe miki ya kuma kore ki, kika haihu a titi? Wai duk kin manta, har haka yake da tasiri a rayuwarki?.”

Runtse ido ta yi da ƙarfi tana tunawa. Saboda Sagir har rayuwa ta yi tsakanin rai da mutuwa, tsakanin bomb da bindigogi. Cikin taraddadin a kowacce daƙiƙa za ta iya zama gawa a bawa ungulu namanta ta yi watanda da shi, da tsohon cikin Sagir ta yi aikin gini, da tsawon cikin Sagir take gudun ceton ranta. To me ya sa yanzu take damuwa dan Linda ta rage mata aiki? ‘Yaya, Hajiya’, wata zuciyar ta ba ta amsa. Tabbas haka ne, saboda su ne take jin ba daɗi ba wai don tana nadamar ba a kyauta masa ba. Kome ya faru da shi da abin da zai faru a gaban shi ne sila. A yanzu kam lokaci ne da za ta ture wasu mutane daga gabanta ta tunkare shi, ta ɗora daga inda Linda ta tsaya, ba za ta taɓa bari wannan kwan ya fashe ba, za ta iya ƙarar da kafatanin abin da ta mallaka gurin ganin Sagir ya wuce Prison an fara bashi aikin fasa dutse da kwasar kashin abokanan zamansa, kwatankwacin abinda ta yi ita ma. Idan riga ɗaya ce ta rage mata a duniya za ta iya cire ta ta bayar in har hakan zai iya ƙarasa ruguza Sagir. Sai dai abu ɗaya ne ya fara dagula mata ranta wannan lauyar me zubin turmi idan ba su yi da gaske ba za ta iya rusa musu kome. Duk da ta san mai gano Abbati na raye a yanzu daidai yake a ce ya fidda Raƙumi ta bakin Allura, amma kam Linda da Yaya sun yi wauta da ba su faɗa mata shirinsu ba. Da ace sun faɗa mata tsarinsu. Da babu abinda zai sa ta ɗauki wuƙa a sa’adda za ta je makarantar, idan har Barr. Zuby ta gane hakan, to fa za ta yi amfani da wannan damar ta saka shakku akan su.

“Tsakanin ke da Yaya waye ya shiga gidan Sagir ɗin?”

“Ni ce, kinsan lamarin sai mace ai.”

Shiru ta yi cike da taraddadi tana dubanta.

“Kin tabbata ban da mukullin ba ki taɓa kome a gidan ba?”

Ita ma tsayawa ta yi tana kallon cikin idanuwanta.

“Kai! Ban taɓa kome ba, toilet kawai na shiga na wanke hannuwa na.”

“Sai kika taɓa handle din ƙofar?”

Zare idanuwa ta yi tana duban ‘yar ƙaramar Fatin da ke zaro mata kuskurenta. Ko da yake ba mamaki idan aka yi duba da shekaru biyu da ta kwashe tana karance-karancen jaridu da mujallu, dole ta samu experience kan kome.

“Tabbas na taɓa, amma ai ba na zaton wani zai kula, sannan na tabbata shi ma ya shiga toilet din, kinga idan ma da yatsu na jiki zai ɗauke.”

“Idan kuma ba shi ya shiga ba fa? Na san dai bai yiwuwa ace banɗaki ɗaya ne a gidan ko? Linda! Abinda kike ganin ƙarami, a gurin ‘Yan sanda shi ne babba. Ki tashi ki je gidan ki samu tsumma ki goge duk wani abu da kika san kin taɓa. Kafin waccar Turmin ta riga ki isa.”

Ta furta tana miƙewa cikin jin zafin kuskuren, a lokacin ne kuma idanuwanta suka sauka kan kunnenta, ta ƙara buɗe su kafin ta isa gareta da hanzari tana taɓa kunnen.

“Kar ki ce mini a can kika yada barimarki ta gwal?”

“A’a gata nan.”

Ta furta tana shafa kunnen, da sauri ta juya ga madubin Falon. Zahiri babu barimarta. Kasancewar huji biyu gare ta ya sa sam ba ta kula ba.

Ai da gudu ta yi ɗakinta saman gadonta ta fara bincikarta, babu ita babu alamarta, ko da take barima, ba ƙanƙanuwa ba ce da za ta kasa ganinta. Goshinta har ya fara tsattsafo da gumin tashin hankali, a haka ta ɗago tana sauke idanuwanta cikin na Faɗime da ke tsaye bakin ƙofa rungume da hannayenta a ƙirji. Da ido ta tabbatar mata da acan ta jefarta, ta tuna lokacin da labule ya naɗe ta, ta yiwu a lokacin ne barimar ta fita, ta yiwu kuma a cikin mota. Tuna mota ya sakata wawurar mukullin ta fice a guje zuwa ƙasan gidan. Babu inda ba ta duba a cikin motar ba amma babu, haka ta taho har step ɗin bene tana haskawa nan ma babu.

“Na shiga uku! Ammy tana can ya zan yi?”

“Tashi za ki yi ki tafi, fatan basirar ta ki ta baki dabarar gwada mukullin gidan?”

“Eh, eh, shi ne ma abinda ya kai ni toilet ɗin, mukullin na gwada a jikin sabulu. Yana cikin jakata, bari na ɗauka na je Thief Market a yanko mini irinsa, sai na je na duba barimata na kuma goge handle din toilet.”

Ta furta tana ƙarasawa jikin jakarta da ta fita da ita ranar. Sai dai, sai da ta fiddo da duk wani abu da ke cikin jakar ba tare da ta ga sabulun ba.

“Kin tabbata da wannan jakar kika fita?”

Fati ta furta tana matsowa kusa da ita. Zuwa yanzu kanta ya fara sarawa.

“Wallahi ita ce, ya za ai na manta.”

“To ina sabulun, kar dai?”

A firgice ta dafe kanta idanuwanta a zare.
“Kar dai shi ma na barshi a toilet ɗin? Kai, ba zai yiwu ba, sai ka ce ‘yar kwaya.”

A daidai lokacin kararrawar falon ta buga da ƙarfi. A tare suka kalli juna tamkar waɗanda ke tunanin Azara’ilu ke jiransu a ƙofar. A haka Linda ta miƙe ta isa ga madubi tana duba fuskarta, yadda ƙarar kararrawar ke daɗa ƙarfi, haka zuciyarta ke shirin narkewa ta nutse a ƙirjinta.

Tana buɗe ƙofar yaron gidansu da ke bawa flowers ruwa ya miƙo mata zungureriyar Ambulan.

“Gashi wani ya ba ni a ƙasa, ya ce a bawa Madam.”

“Yana ina?”

“Yana miƙo mini takardar ya tada motarsa ya wuce.”

“Okay thank you.”

Ta furta tana rufe ƙofar.

Faɗime ta miƙawa takardar, ta mata alamar da ta buɗe.

Farke ambulan din ta yi, ta zaro doguwar takardar ta hau warwarewa.

Wani abu me ɗaure kai shi ne.

Duk girman paper rubutun layi guda ne, sai wani ƙaton zanen zuciya an ciki cikinsa da red pen an zana kibaya a jiki. A can ƙarshen takardar ta karanta abinda ya dakatar da lissafin tunaninta ya sakata zubewa da zaman ‘yan bori.”

“Kar ki damu, sabulunki me hoton mukulli yana amintaccen hannu.”

“JWBilisco.”

<< Fadime 26Fadime 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×