Skip to content
Part 30 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Ƙwarewar da ya yi ya sakata tashi da gaggawa ta miƙa masa ruwa. Allah ya sani ita ta kwarar da shi, ji ya yi tana magana kamar an shaƙe Ɓera. Ban da ƙeta ya yana cin Dambu za ta maƙe masa murya, ai dole ya shaƙe shi.

“Haba Zuby yau muke tare? Dan ALLAH ki yi magana yadda zan fahimta.”

Taɓe baki ta yi tana gyara zaman gilashin fuskarta. Kallonsa ta yi cikin ido ta lumshe nata idanuwan tana imaging gashi yana bata abinci a baki da hannunsa mai albarka. Ya ilahi! Yadda yake tauna Dambun ƙara tafiya da imaninta ya yi. Bakinsa ɗan madaidaici ba irin nata kamar an yanka da Adda ba, duk da duhun da ya yi na bala’in da yake ciki hakan bai hana fuskarsa sheƙi ba, idanuwansa sun ƙara girma sakamakon ramar da ya yi.

“Kai! Allah Sagir ina sonka fiye da kome.”

“Zuby! Are You Okay?”

Ya furta yana ɗan bubbuga tebur ɗin dake tsakaninsu.

“Eh, kawai dai ina son ka haddace cewar Ina Son Ka.”

“Nasan kina so na, kin faɗa mini tun kina ‘yar tatsitsiyarki, ban kuma manta hakan ba. Fatan ba kin zo takanas nan ba ne dan ki faɗa mini waɗannan kalmomin? Yanzu mene kike tambayata ɗazu?”

“Okay…” Ta furta tana haɗe yatsun hannunta.

“So nake in ji ko ka tuna waɗanda ka haɗu da su a washegarin ranar da yaron ya mutu?”

Ture cooler Dambun ya yi gefe, ya goge hannunwansa a rigarsa, kafin kuma ya haɗe yatsunsa yadda yaga ta yi yana ƙarewa gajerun hannayenta da suka sha agogon gwal kallo.

“Na tuna kome. Bari na fara faɗa miki tun daga lokacin da na tashi daga barci duk da ban ga amfanin da hakan zai miki ba…”

Ya numfasa.

“A safiyar ranar da na fito daga gida kai tsaye Bingel& Daughters Petroleum na yi na sha mai, daga nan kuma na taho Victoria Island gidan Fati. Na baro unguwar da misalin ƙarfe 11:30am, daga nan ne kuma na tafi Stadium akwai ball da za a buga da tsakar rana. Na zauna a stadium har 4:00pm sakamakon hira da na yi ta yi da wasu ‘yan team ɗin da nake. Sai da muka yi sallah, tukunna na fito na tafi Shisha Joint, na sha shisha da Coffee, na zauna anan har ƙarfe 6:30, daga nan kuma na tafi inda na saba cin abinci QURAISHA RESTAURANT. Anan na zauna hira da Waiters ɗin da na saba da su, har zuwa 9:00pm na taho gida…

“To dawa ka haɗu da shi kenan? Ni ba abin da na fahimta a wannan labarin naka. Ni wallahi gyangyaɗima ya sakani.”

Ɗaga kafaɗarsa ya yi yana watsa hannu, “ai dama na faɗa miki babu abin da za ki ƙaru da shi.”

“Look Sagir, kawa Allah ka tuna wani abun, dole fa a ranar ne aka yi wani abin, ni tambayata duk a yawon naka baka haɗu da wani ba ko wata baƙuwar fuska haka, ko a gidan abincin ba wani ko wata da ya shiga sabgarka…”

“Wata…Yes, wata doguwa fara mai kyau Zuby, oh! Wai wannan dama kike buƙatar ji? Ni ban ɗauke shi wani abu ba ai, na saba ganin mata irin haka na bi na in dai zan zauna a iren wuraren nan, amma wannan ba baƙuwa ce a gurina ba, ina ɗan ganinta jefi da jefi a Little Angels.”

“Ya rabbi! ” Ta furta da ƙarfi har tana ɗora hannunta a kan nasa hannun. Ya mata wani irin duba, ta yi saurin janye hannunta tana washe masa fararen Rabbit Teeth ɗin ta.

“Ko za ka iya tuna me take yi a makarantar?”

“Ya za ai na sani? Na fi zaton dai akwai yaron da take kawowa.”

“Zama ta yi tare da kai ko?”

“Kamar kina gurin, ita ce ma ta mana order abinci, ganin na san fuskarta ya sakani bata lokaci na. Sannan bata yi kama da Hausa ba, sai dai na yi mamaki da na ji har Hausar ta fi zama a bakinta fiye da ni. Ke na tuna, kamar fa Abbati ya taɓa nuna mini ita, ko tare ma na gansu? Kai na manta. Ta yiwuwa ko maƙociyarsu ce ko sister Abokinsa yake min bayani, na manta gaskiya.”

“Sai aka yi yaya da ta zauna kusa da kai?”

“Shi ke nan fa, hira kawai muka yi, hirar ma mai amfani, kan taɓarɓarewar Harkokin Tsaro.

“Abincin kawo muku aka yi, ko ita ce ta karɓo?”

“Kawowa aka yi, sai dai drinks na mutum ɗaya ne, ita taje ta karɓo sauran.”

“Wow! This thought never came to my head”.

“Kuma ki ke zata?”

Sai kawai ta kanne masa ido ɗaya.

“Kana ji ko, a wannan tashin da ta yi dan kawo muku drinks kome ya faru, wannan din da ba mu san wacece ba ita ce dai silar mutuwar yaron, wa ma ya sani ko ita ta kashe shi. A cikin lemo ko ruwa ta zuba maka abinda zai gusar da hankalinka. Idan kuma baka yarda ba faɗa mini ta yadda aka yi ka zo gida?”

“Da wani irin ciyon kai na zo gida, kasancewar tun safe nake ji kaɗan-kaɗan ya sa ban damu ba.”

“Yauwa! To na san ka tuna kai ne ka buɗe ƙofar gidanka. Ko za ka iya tuna ka rufe ƙofar?”

Dafe kansa ya yi yana mirza tsakiyar goshinsa. Ya gaza tuna kome kuma. Dan haka kawai ya ɗago idanuwansa har sun kaɗa yana kallonta.

“Gaskiya na manta.”

“Ka manta na nufin baka rufe ba, da kuma takalmanka ka wuce har cikin bedroom ɗin ka. Haka baka yi sallar isha ba ranar kawai zubewa ka yi a gado ko?”

Kallonta kawai ya yi ya gaza maganar. A cikin idanuwansa ta gane me yake son tambaya.

“Okay, na gane hakan ne a jiya da na je gidanka. Akwai ƙasa- ƙasa kan gadonka, wannan ya tabbatar mini da takalmanka ka hau gadon ka kwanta cikin goshewar hankali.”

‘Tabbas hakane, sai da ya tashi da safe ya cire takalmansa, ya kuma rama sallar ishar da ciwon kai ya hana shi yi. Amma kuma duk ya akai wannan da kaɗan tafi Wadar tasan bai yi sallah isha ba.’

“Zuby Are You Human?”

Murmushi ta masa cikin jin daɗin yanayin tana murza tuwon hancinta.

“Ka bar musu gida a buɗe shi ya sa suka iya shiga. Babu mamaki ma idan na ce maka ƙila tare da ita ko su kuka zo gidan, ko kuma da sassafe suka zo suka ɗauki mukullin motar suka tafi suka aikata abinda suka yi, suka dawo maka da shi duk kana barcin rashin hayyaci. Ɗaya a cikinsu kuma ya yi mantuwa, sanin ƴan sanda za su iya zuwa gidan ya saka shi komawa jiya domin ɗaukar abinda ya manta. Anan ne kuma ya bar shaidar da ta tabbatar mini da mace a cikin shirin. Samun mukullin gidan kuma ba zai musu wuya ba, tunda har suka shiga a karon farko, kenan satar taswirar mukullin su kai a musu irinsa ba zai yi wuya ba.”

“Amma wace macece a rayuwata da za ta yi mini haka?”

“WHO knows?”

Ta furta tana cije laɓɓanta. Sai kuma ta yi baya kaɗan tana yin ƙasa da muryarta kamar mai jin tsoron faɗa.

“Waya sani ko wacce ka ji daɗin dare ɗaya da ita ce?”

Dishi-dishi ya fara ganinta saboda dukan da maganar ta masa. Gumi har ya fara tsattsafowa a goshinsa haka ya ɗago da huci yana dubanta.

“Get Out Of My Sight! Fati ba za ta taɓa yi mini haka ba, stupid kawai, ki zargi kowa amma banda ita. Kika sako ta cikin shirmen nan babu abinda hakan zai nuna mini sai jahilcinki a kishi.”

Taɓe baki ta yi da ya gama zame mata ɗabi’a ta miƙe tsaye tana rataya jakarta.

“Romeo haƙuri za ka yi, ko Dattijona na Sokoto za ka kira sunansa ka zaga ba zai dame Ni ba. Saboda ba na taɓa hasashe ba daidai ba. A tun ranar da muka fito daga court ta bi ni da wani banzar kallo me gauraye da tsoro na dasa mata ayar tambaya. Saboda akan idona wata doguwa fara ta mata raɗa a kunne ta waigo tana kallona kamar ta ga baƙin kumurci. Karka damu zato kawai nake yi, kasan dai babu hankalin da zai yarda uwa za ta iya kashe ɗanta saboda dalili irin naku. Dan haka ban ce ita ba, amma na ce ma makusanta za su iya aikata hakan. Ta yiwu dan su saukaka mata damuwar yaron, ko kuma dan su rama mata abinda ka yi mata sai su kashe shi su ɗora maka alhakin kisan. Koma dai menene ita da duk wani nata, ko da mai yi mata cefane ne to ya shiga cikin littafina. Ba kuma zan taɓa hutawa ba sai na isa in da nake son isar.

“Zuby ba na so! Bar shi kawai ba na son taimakon idan har za ki saka Fati a ciki. Wallahi kin ji na rantse na gwammace na dawwama nan a prison a kan dai kisa wasu ƙattin mazaje na tuhumarta kan mutuwar ɗan ta. Ban da zafin kishi da jaraba irin taki da kuma rashin sanin ciwon haihuwa ta ya ya za ki je ki kama tuhumar Uwa? Uwar da ɗan ta bai fi sati da mutuwa ba. Ki barta ta ji da raɗaɗin zuciya da na rashi.”

“Hmm! Jahila ko?”

Ta furta tana zare gilashin idanuwanta ta goge kwallar da ta taru a lokon idon. Ta maida glass ɗin a sanyaye tana jan hanci.

“Da wannan jahilcin nawa da yardar Allah zan tabbatar maka da zatona. Fatin da kake karewa sai ta zo gabana akan idonka tana roƙarka da ka sa a tsaida shari’ar nan. Na tafi, ka kuma shiryawa wasu tambayoyin nawa zan dawo.”

Ta furta tana miƙa hannunta ta ɗauke cooler dambunta ta juya.

“Zuby, Zuby! Na ce miki ba na so ko?”

Ko tsayawa bata yi ba ballantana ya saka ran za ta juyo haka ta yi ficewarta.

Komawa ya yi sharaf yana zubewa kan kujeran.

“Kai! Innalillahi wa inna ilahhir raji’un raji’un! Ni wai me na yi ne?”

Ya furta yana buga hannunsa kan tebur ɗin. A sannan ne kuma yaji an cika hannu da shi ana jansa zuwa muhallinsa na gado.

B I L I S C O

Zoben ya damƙe a tafin hannunsa idanuwansa a lumshe ya dukan ƙirjinsa da hannun a hankali.

Wani daɗi yake ji yana ratsa shi, daɗin da rabon da ya ji irinsa shekara guda kenan. Tun ranar da ya tarwatsa Ƙaryar Imam ta hanyar sakawa Imam wata matsiyaciyar guba me fara aikinta tun daga harshe. Ba kuma dan kowa ya yi haka ba sai dan Mace, macen da saboda ita babban Amininsa ya koma maƙiyi gare shi. Saboda ita kuma ya rasa hannunsa guda ɗaya.

Yana son Mahmuda! Bai taɓa haɗuwa da wata halitta mai halacci irin sa ba. Yana tuna lokacin da aka kama shi za a sare masa kai, Mahmuda shi ya sai da ransa ya riƙe kaifin takobin da tafin hannunsa

Yana son Mahmuda! Bai taɓa haɗuwa da wata halitta mai halacci irin sa ba. Yana tuna lokacin da aka kama shi za a sare masa kai, Mahmuda shi ya sai da ransa ya riƙe kaifin takobin da tafin hannunsa yana roƙar Imam da ya kashe su tare. A saboda Mamuda ya tsira da ransa, aka saka shi cikin yara aka basu horo tare. Sai gashi shi shi ne ya yi sanadin mutuwarsa saboda mace ta shiga tsakaninsu. Shin ta yaya zai yafe wannan? Sai dai fa wani abin mamakin shi ne sam baya jin nadamar hakan, saboda dole mutuwarsa ita ce tsani na farko da zai taka dan ya isa ga Faɗime. Duk da a wani ɓangare na zuciyarsa baya jin daɗi ko kaɗan, musamman idan ya tuna lokacin da yake masa wani kallo a lokacin da ake ƙoƙarin sare ransa. Ko da bai furta ba ya sani yana tuna masa amanar iyalinsa daya ba shi kwanaki uku kafin mutuwarsa.

“Na sani kana jin haushi na saboda na auri macen da kake so, na kuma fi ka samun kwanciyar da ita duk da kuwa tarin matan da kake aure. Na sani idan da za ka samu wata dama ko yaya take da za ka iya kashe ni, za ka aikata hakan saboda ka same ta. Na yarda kana son Fati da gaske! Saboda abinda nake gani cikin idanuwanka na tsanata bantaɓa ganin ka yiwa wata halittar ba. To kar ka yi mamaki dan yau ni da kaina zan danƙa maka amanar Fati da Yaronta a bayan a raina. Jabiru, na gwammace Fati ta dawwama da kai akan dai ta ci gaba da rayuwa da Imam, ko kuma a tura ta Jihadin da zai zama asara ga rayuwarta har bayan ranta ta tadda azabar Ubangiji. Na roƙe ka da Allah da ka riƙe mini amanar Fati a bayan raina!”

<< Fadime 29Fadime 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×