Skip to content
Part 31 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

A lokacin da ya masa wannan maganar zafin kishi ya hana shi fahimtar kome, sai ma janye kafaɗarsa da ya yi daga hannunsa ya bar masa gurin. Amma a ranar da zai mutun, a cikin idanuwansa ya gane da gaske Mahmuda amanar Iyalinsa ya bar masa, shi ɗin da ya san babu wanda ya ƙi jini irinsa. Tabbas ya yi ƙoƙarin riƙe amanar tasa duk da kuwa domin kansa ya yi, tunda kuwa a washegarin da Mahmuda ya mutu Imam ya buƙaci a kawo Fati a mata hukuncin Riddah, yaronta kuwa a binne shi da ransa. Shi ya yi ruwa ya yi tsaki ya hana ta hanyar bawa Imam shawarar a barta ta gama Idda sai a sama mata wani hukuncin. Ke nan da Fati za ta kula ta kuma yi nazari, za ta gane ba fa dabararta ba ce ta ƙwace ta, shi ɗin dai shi ya bata wannan ƙafar. Saboda da ace irin dabarar Fati na aiki ga Imam, da kuwa kafatanin matan da suke kamowa ba suyi Jihadin ba, zasu dinga yaudarar mazanne suna guduwa. A ƙa’ida shi da kansa zai ɗaura mata bomb ɗin a jikinta, sannan me haɗe da riga zai saka mata ba wanda za ta iya kwancewa ba. Amma bai yi hakan ba. Har suka isa cikin Kano bomb ɗin na ƙasan kujera, koda suka isa shi da kansa ya ce ta ɗaura. Yana cikin hankalinsa, yana kuma ankare da sa’adda ta aje bomb ɗin bata saka ba ta yi kamar za ta yi kissing ɗinsa.

Yana sane ya biyo bayanta da sauri har tsakiyar kasuwar kafin ya tashi. A wannan lokacin ne ya rasa yatsan ƙafarsa garin gudun ceton rai. Hakan bai masa ciwo ba sai da ya koma Imam ya turke shi da tabbas yana sane ya barta ta gudu. Bai saka a kashe shi ba, amma fa ya sa a datse masa hannunsa tun daga gwiwar hannun. Ba kuma dan kome ya yi hakan ba sai dan tsoron kar ya rasa Jabirun yadda ya rasa Mahmuda, manyan kwamandodinsa ne da baya da kamarsu. Sai dai fa ya kashe maciji ne bai sare kansa ba. Dan kuwa bayan shekara ɗaya ya kawo ƙarshensa ta hanyar poisoning ɗinsa domin kawai ya isa ga Fati, yarinyar da saboda ita ya rasa hannunsa ɗaya ya zama nakasasshe. Ya sani idan har Imam na raye ba zai taɓa barinsa ya mallaki Fati ba.

Daga nan ya yo Lagos inda ya san tana rayuwa. Dan kuwa ya daɗe da sanin waye Mahmuda me kuma zai iya sadaukarwa ga Fatin. Kenan shekara biyu da ta yi duk a tafin hannunsa ta yi su, ya san dukkan motsinta, harta lokacin da take kwanciya barci take farkawa yana da labarinsa. A yanzun da ya bayyana gareta ya yi ne dan ganin wani yaje mata duk da an tabbatar masa da cewar shi ne Baban yaronta. Kenan zai iya zame masa matsala. To shi fa yaron yake hari. Yana sane da cewar Fati ba za ta taɓa saurararsa ba sai idan iko ya mata da ɗan ta. Wannan ko, ko za ta mutu za ta yarda ta aure shi idan taga zai illata mata yaron. Wannan zoben da ya ƙarɓe kuwa ya yi ne saboda raɗaɗin da yake ji a duk lokacin da ya gan shi a hannunta. Zoben da zai iya cewa nasa ne, dan kuwa shi ya fara ganinsa ya ɗauka yana juya shi yana ƙiyasta shi da hannunta, Mamuda ya yi sauri ya warce yana masa dariya, ƙarshe shi ne ya saye shi ya kuma danƙa shi a hannun wacce shi ma ita ya rayawa shi. Saboda babu lefi dan ya sha alwashin sai ya rabata da shi, baya son ganinta da duk wani abu da ya danganci Abokinsa. Kai ko aurenta zai yi sai ya rabata da wannan dukiyar. Tik dinta yake son ganinta, shi zai wadatata da duk abinda yake nasa.

Shigowar yaronsa ne ya saka shi ɗagowa daga tunaninsa yana dubansa.

“Oga, na Maƙarfi fa zai iya ba mu matsala, mun daina samun kowane irin bayani game da shi. Yanzu KM baya iya bibiyarsa, saboda yana mugun kula, ko tafiya yake yi, baya sakan biyu bai duba bayansa ba.”

“Kar ka damu, ka jaddada masa kar ya ɗauke idonsa daga gidan. Ko yaya ya yi kuskuren fitowa da yaron, a nuna masa ƙarshensa!”

“Angama Oga.”

F A Ɗ I M E

“Ko kin kula yau kusan sati kome daidai yake tafiya, babu wata matsala ta kowanne ɓangare. Ga Yaya ma can ɓangarensa ya ce kome lafiya. Anya shirun nan da alheri, jibi ne fa lokacin da kotu ta ɗiba mana zai cika.”

Linda da ke gefe tana shafa jan farce a ƙafarta cikinta ya bada wani ɗan sauti, sai kuma ta yi saurin aza murmushi a fuskarta tana kallonta.

“Ban jin da wani abu gaskiya. Dan ko Barr. Jagazi ya gama haɗa dukkan bayanansa. Haka ya samu ƙarin shaidu waɗanda suke maƙota ga Sagir ɗin, sun ga kuma lokacin da ya fita a time ɗin. Kin ga ko wannan kaɗai ya isa idan ya haɗa da shaidar yatsun Sagir da aka samu a jikin sirinjin.”

Faɗime ta miƙe ta isa ga window tana kallon farfajiyar gidan. Ita ba Sagir ba ne damuwarta yanzu, wancan mutumin da bata san kowaye ba, amma shi ya san nasu shi ne damuwarta. Shirunsu ya ba ta tsoro. ‘To ko dama kawai Zoben yake so?’ kai! Ita kam ta kasa gane kome. Amma dai kowaye Allah ya fishi. In SHA Allah ba zai samu damar munana musu ba. Daidai nan ta ji ƙarar mota ana buɗe gate, ta sauke idanuwanta a hankali tana tuna in da ta san motar, kamar dai ta Sagir. Zuciyarta bata tarwatse ba sai da ta ga Hajiyar Sagir ta fito ita da Babban Mutum.

Dafe ƙirjin ta yi tana zare manyan idanuwanta da suka fara cika da ruwan hawaye. Ƙare mata kallo take yi, ta rame sosai, alamun tasha jinya. ‘Me Hajiya ta zo yi gidanta yanzu? Ba dai ta’aziyya ba? A’a, ko roƙonta za ta yi ta yafewa Sagir?Kai! Ita ko ɗaya bata buƙata. Ba har haka ta lalace ba, ba ta yi riƙar da za ta iya tsayawa gaban Hajiya da wannan ƙaryar ba. Uwa ce me kowacce irin daraja a gurinta. Haka Abbati jikanta ne, ta yaya za ta iya murzawa idonta kwallin Audi ta karɓi ta’aziyyarsa alhalin kome ƙarya ne. Ta sani Hajiya na shigowa ta yi tozali da ita duk wani ƙarfinta kuma zai ƙare, Allah shaidarta ba za ta iya haɗa ido da ita ba, ba za ta iya ba, yadda take jin Abbati a ranta, ta tabbata haka Hajiya ke jin Sagir, ita kuma ta silarta Sagir ɗin ke firsin a yanzu. Kenan da wane irin ido za ta kalleta? Matar da ta mata riƙon da ko iyayenta ba za su mata irin sa ba. Dan haka da sauri ta cika labulen ta zura da gudu gurin Landline ɗin su ta kira Maigadi.

“Waɗannan mutanen kar ka bar su su hawo sama, ka ce musu bana nan na yi tafiya mai nisa.”

“Madam naga wannan da kika ce Uncle din ki ne da Mamansa, kuma na faɗa musu kina nan.”

“Ya ilahil! To maza ka ce musu bana nan mantawa ka yi na yi tafiya.”

Ta kashe wayar tana zurawa ƙofar shigowar ido.

Tana jin sanda suka latsa ƙararrawa, suka ƙara latsawa kafin Maigadi ya iso ya faɗa musu saƙonta su juya. Ƙara komawa ta yi jikin tagar tana leƙensu kome na daɗa kwance mata. Tana ganin lokacin da Babban Mutum ya ɗago yana kallon saitin tagar da take kamar wanda ya ji a jikinsa ana kallonsa. Sauke labulan ta yi da sauri ta durƙushe a gurin tana sakin gunjin kuka. Kome ya dawo mata sabo, ta rasa gane irin rayuwarta, me ma ta zo yi cikin duniyar. Mamanta take so ta gani da Babanta, so take ta jita a jikinsu suna rarrashinta. Tunda ta taso take rasa kome, tunda ta fara mallakar hanlalinta ba ta taɓa shafe mako guda cikin kwanciyar hankali ba. A duk lokacin da rayuwa ta fara mata daidai wani abin zai zo ya rusa kome. Hala ita kaɗaice marainiya a duniya? Ko kuma ita a haka za ta ƙare? Ba za ta yafe ba, ba za ta taɓa yafewa Uwale da bata barta ta mori ƙuriciyarta ba. Miƙewa ta yi a hankali ta bi bango jin juwa na ɗibarta, ta faɗa ɗakinta tana doko ƙofar.

Linda da ke gefe rungume da hannayenta ta girgiza kanta cikin jimami. A lokaci guda wayarta ta ɗau ƙara tare da cikinta, kallon wayar ta yi, ganin me kiran ya sakata sakin fuska ta kai wayar kunne.

“Wai hala takaba kika fara ne da ba ki son fitowa? Sau uku fa Oboy na zuwa nan saboda ke kina shanya Shi. Ki fito da Allah shi da Shazy ne”

“Okay Baby, zan zo!”

Aje wayar ta yi ta faɗa wanka zuciyarta cike da tunanin Zuby. Tabbas saboda ita ne ba ta son fita ko nan da can, kai ko ƙasan gate za ta fita da hankici take fita duk inda ta kama sai ta goge a fakaice, haka nan hankalinta ya ƙi kwanciya, ba ta so ta sake kuskure ko yaya yake. A yanzun ma da za ta fita dan dai ita ma tana ƙishirwar ganinsa ne. Tun lokacin da ta tuna da Lesbian, Oboy ne kaɗai namijin da ya burgeta, take jin za ta iya aura. Babban Actor ne a Nollywood.

Fitowa ta yi ta shirya cikin mini skirt dinta na ɗabi’a ta fice bayan ta ɗauki hankicinta da yafi wayar hannunta a yanzu. Motarta ta kalla, haka kawai ta ji ita ma ba za ta fita da ita ba, bare ayi amfani da ita asirinta ya tono. Dan haka ta taka da ƙafafuwanta zuwa bakin titi ta hau Taxi, ko handle din da ta riƙe sai da ta fakaici idonsa ta goge, haka a cikin motar banda ɗuwawunta da ta ɗosana kan kujerar, bata yarda ta taɓa kome ba har ya kaita Park ɗin ta sauka ta sallame shi. Ba tare da ta ankara da wata koriyar mota da ke biye da ita ba.

Ƙarasawa ta yi ƙasan lemar da suke inda suke jiranta, suka ɗau sowa kowa na murnan ganinta. Tasowa ya yi shi ma ya cirata yana juyi da ita, kafin ya dire ta ya lalubi bakinta. Sai da ya tsotseta san ransa kafin ya cikata yana kallon yanayinta. Baya jin Hausa, dan haka da yarensa yake tambayarta lafiya take. Murmushi ta masa a sanyaye ta zauna a gefensa tana ƙara ƙankame hankicin hannunta. Hira suka yi sama-sama kafin a zo a jere musu lemuna da Samosas. Ɗauko glass cup biyu ya yi da ke cike da tataccen Lemon ya mika mata domin su yi cheers, sai kawai ta girgiza kai alamar ba ta so, abin ya ba shi mamaki dan haka ya aje a sanyaye ya ɗaga nasa yana sha. Ganin kamar bai ji daɗi ba ya sakata miƙa hannu ta ɗauki na gwangwani. Ita fa na cup ɗin ne ba ta so, ba ta san inda zai je ba, kar taje Barista ta samu dalili. Dan haka na gwangwanin ma tana gama sha ta mammule Shi ta danna cikin jakarta. Oboy ya bita da kallon ƙalau kike kuwa?

Murmushi ta masa mai sanyi, a hankali ta ce.

“Kar ka damu, wasa zan yi da shi idan na je gida.”

Buɗe baki ya yi yana dariya ya buƙaci ta jefar da Shi su je a sai katon ɗinsa.

Cewar da ta yi bata buƙata ya saka shi fincikar jakar Yana ƙoƙarin fiddo da mulallen gwagwanin. Hankalinta ya tashi, gani take yana jefar da gwangwanin za a ɗauke, gani take Zuby kawai ta san ita ce ta je gidan Sagir ta sha wannan Lemon, ta manta sam basu bar wata ƙafa da za a zarge su ba. Dan haka ta bishi suka kama kokawa kan jakar, shi tsokanarta yake yi, ita kuwa da gaske take yi kan gwangwanin nan za ta iya manta kome duk kuwa girmansa gareta. Ya yi nan ta bishi, ya yi nan ta bishi, ƙarshe dai ya samu nasarar zuge jakar ya zura hannu kenan zai zaro gwangwani ya ji saukar yatsunta a fuskarsa. Gabaɗaya gurin aka yi tsit! Har waɗanda hankalinsu bai kawo gun ba ya kawo, abin ka da Cele har an yanyame shi, shi kam ta saka shi a wani irin shiru, wani abu ta masa da ya sani gobe jaridar farko a shafin farko za ta fito da sunansa ne, ƙila ma harda hotansa a lokacin da aka yi marin.

Jikinta na rawa cikin hawaye ta sunkuya ta ɗauke jakarta ta ƙanƙame. Juyawa ta yi da gudu ta keta tarin mutanen ta fice daga gurin. Taxi ta tsayar ta shige da hanzari suka yi gida.

Minti biyar da ɓacewarta ‘yar gajeruwar Barr. ta bayyana a kan dogon takalminta me tsayin zira’i tara da ɗigo tara. Sunkuyawa ta yi a daidai inda ta shiga Taxi ɗin ta ɗauke hankacif ɗin da ta jefar lokacin da jikinta ke rawa za ta shiga motar. Murmushi ta yi me kyau bayan ta gama ƙare masa kallon dabbare-dabbaren jambakin da ke jiki. Naɗe shi ta yi a leda ta zura a jakarta.

A ranta take jin tunda zuciyarta ta kafe da zargin waɗannan matan biyu dole ta fara gwajinta kan ɗaya a ciki. Dole kuma da wannan farar doguwa za ta fara. Ko a yanzu tana jin ƙamshin turaren Pink a jikin hankacif ɗin. Dan haka ta juya a kan takunta na Agwagwa ta isa ga motarta da zummar zuwa inda za a gwada mata gwangwanin Shanin da ta gani gidan Sagir da kuma wannan hankacif ɗin. 

<< Fadime 30Fadime 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×