M akarfi
"Yayan Ammy ni ma ka fesa mini turaren irin naka."
Murmushi ya yi ya rage tsawonsa daidai shi, ya ɗaga hannunsa ya fesa masa turaren gurin hammata, suka kyalkyale da dariya a tare.
"Gashi nan duka na baka shi, maza kaiwa Umma ta saka maka cikin kayan ka."
"Me za a kawo mini?"
Ta furta tana yaye labulen ɗakin. Sai kuma ta yi turus tana kallon yaron, ya yi kyau sosai cikin Uniform ɗinsa Ja da Fari, a sanyaye ta ƙarasa shigowa ɗakin.
"Ni kam banga dalilin da za a ce yaro kamar wannan da ko. . .