Sagir kam bai san wace rana ce yau a tarihin rayuwarsa haka ba. Da ƙarfi ya runtse idonsa jin abinda yayansa ma fi soyuwa gare shi ke faɗa masa kan wannan ƙasƙantacciyar yarinyar da a cikin ƙasƙantattun ma ita ɗin mahaukaciya ce, mai kwana a bola ta ci ƙazanta. Wai ita ake cewa zai rayu da ita gida guda. Ba zai yiwu ba, idan ko har ta shiga cikin gidansu, to barin gidan ya kama shi. Idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai ƙara awanni huɗu a cikin Kano ba. Da dai ya. . .