Ƙaƙƙarfan kiran Sallar da ladanin masallacin gidan nasu ya daddage ya zabga haɗe da na wayar da ke yashe a ƙasa ne, suka haɗu suka farkar da Sagir dake barci sadidan hannunsa bisa gashin Faɗime da kanta ke saman ƙirjinsa.
Da fari kasa gane yanayin da yake ciki ya yi, a hankali kuma kiran sallar na ƙara tsawo, tunaninsa na komawa baya. Tar! Ya hango lamarin cikin idanuwansa. “Innalillahi wa inna ilahhir raji’un, Allahumma Ajirni fi musibatin wa akhlifni khairan minha. Astaghfirullah! Astaghfirullah!!” Ya furta a gigice yana tashi zaune, hannunsa bisa fuskarsa yana shafawa kamar wanda ke son tabbatar da abin da ya aikata ba zahiri ba ne. Nutsuwarsa ta gagara saituwa, sai ma wani zulumi da firgici dake shigarsa a duk ɗora idon da zai yi kan Faɗime. Me ke faruwa da shi ne ? Me ya kai shi aikata abinda duk zamansa cikin masu jajayen kunne da manyan yahudawa bai taɓa kwantatawa ba sai yanzu.
A yanzun ma da wacce ya tsana fiye da kome nan duniyar. Nutsa hannunwansa ya yi cikin gashin kansa sa’ilin da zafafan hawayen suka fara sauka saman kuncinsa suna zarcewa can cikin bakinsa, cikin nadama da da na sanin da ta zame masa ƙeya. Babban tashin hankalinsa yarinyar da ya ɓatawa rayuwa, sai kuma uwa uba Hajiya, ya tabbata ba karamin gagarumin tashin hankali ne ya kusanto rayuwarsa ba. A saninsa ko kowa ya yarda ba fyaɗe ya ma ta ba, asali ba ma cikin hankalinsa ya yi ba. To kuwa Hajiya da Yaya ba za su taɓa yarda ba, duba tsanar da yake gwada mata a kan idanuwansu. Da yawa ya sani za a ɗauka ya yi hakanne dan ya fanshe takaicinsa. Ƙila ma a bi shi da tambayar. “Ka na shan barasa ne da zaka ce ka aikata zina cikin maye?” Inaaa! Shi Sagir ba haka yake ba, bai yi lalacewar da zai haiƙewa ɗiyar mutane da sanin ba. Inda yana cikin nutsuwarsa babu ta yadda za ai ya ɗaga ido ya kalli wanann yarinyar da manufar haka, balle har akai ga ya aikata hakan. Sai dai shi kansa ya rasa gane abinda ya kai shi ga aikatawa. Abu ɗaya ya yarda da shi a yanzu, ya ke kuma mamakin gushewarsa a dare ɗaya. Wannan dunƙulallen abun da ya dunƙule masa a rai ya hana shi dukkan wani sukuni da walwala, a yanzu ya shafe kamar zanen baƙar tawada jikin farar takaddar da aka jefa ruwa!
Rashin sanin madafa ne ya saka shi juyawa yana mai tashin Faɗime wadda shi kansa bai san me zai mata idan ta tashin ba. Shirun da ya ji ne ya saka shi matsawa sosai yana mai kara kunnensa jikin hancinta dan ya tabbatar da abinda yake zargi. Jan numfashin da ta yi da ƙarfine ya saka shi ɗagowa da sauri idanuwansu sunka harɗe cikin na juna. Da dukkan ƙarfin da ya rage mata ta tashi zaune tana mai ƙare masa kallo, sai kuma ta riƙe kanta sa’alin da launin idanuwanta suka canja. A hankali kuma sai ta koma yarab saman katifar babu alamar numfashi.
A ruɗe ya shiga jijjigata amma ina! Babu wani sauran numfashi a jikinta. A ɗimauce ya ci gaba da jijjigata tare da kiran sunanta amman ina! Babu wani motsi a tare da ita. Hakan ya saka shi tashi da gudu ya yi toilet, kamfato ruwa yayi a hannunsa ya shiga shafa mata yana kiran sunanta amma ina! Babu fa wani alamar za ta dawo daga inda ta tafi. Tsoro ne ya kama shi, tsoro mai yawa. Idan ta mutu ya zai yi da haƙƙinta da rayuwar sa gaba ɗaya? Tabbas da ya san zai jefa kansa cikin wannan mummunan tashin hankalin da bai yadda ya dawo Nijeriya gaba daya bama, gwara ya dawwama can zai fiye masa kwanciyar hankali. Amman idan aka ce ƙaddara ta riga fata, babu yadda za ayi, illah a karɓeta a duk yadda ta zo. Ganin tunani ba zai kai shi ba, sai ya miƙe yana safa da marwar neman mafita. Kande, Kande kawai zuciyarsa ta tuno masa. Tabbas yasan ita kaɗai ce za ta taimaka masa kan wannan lamarin kafin su Hajiya su farga. Tuna hakan ya saka shi buɗe ƙofar da sauri ya dinga haɗa step uku uku na matattakalar benen nasu, kafin ka ce me ne wannan ya isa ɓangaren da Kande take. Ita ɗinma jin kwankwasan ƙofar ya ɗan tsorata ta sanin Hajiya ba ta fitowa sai karfe tara na safe. To wa ke buga mata ƙofa asubar fari haka? Haka dai ta tashi ta buɗe a ɗarare ta yi tozali da wanda ba tayi tsammani ba, ɗauke da labarin da ya kaɗa mata ƴaƴan hanji.”Anya Auta rashin sanar da Hajiya ba zai zama kuskuren da zaka sake nadamarsa a gaba ba? Me zai sa a ƙi faɗa mat tunda uwa ce, yadda na fahimce ka mai yiwuwa ita ma hakan zai zama. Ba fa karamin abu bane da za a ɓoye. Gaskiya bazan iya cin amanar Hajiya ba, kayi hakuri kawai a sanar mata.”
Har ƙasa ya zube bisa gwiwowinsa ya na roƙanta ta rufa masa asiri, matuƙar Hajiya ta ji zancen nan babu wani uzuri da za ta masa, ƙila ma ta yi fushi da shi, fushin da zai jefa rayuwarsa cikin halaka. Ta taimake shi ta gyara Faɗime shi kuma zai kira wani abokinsa Dr ya duba ta, dan idan ya ce za su tafi Asibiti su Hajiya za su iya jiyo tashin motarsa. Haka dole Maigadi zai gansu. Shi kuwa wannan sirri ne mai girman da yake son a rufe shi tsakaninsu su huɗu har likita. Haka nan dai ya dinga rokon Yar dattijuwa Kande har ta yadda ta bi shi saman cike da tausayawa rayuwar Faɗime ganin dai 6ata lokacin babu inda zai kai su.
Ƙasa da minti Talatin Dr. ya iso gidan. Bakin Ilu Maigadi fal tsegumi ya buɗe gate ganin Auta ne da kansa ya tare shi. Nan da nan ya hau aune-aune jikin sandararriyar Faɗimen har ya gano abinda ke faruwa.
“Dama tana da matsalan kwakwalwa ne?”
Da sauri ya amsa masa da eh. Dan murmushi ya yi.
“To ai ba wani abu ba ne ɗan shock ɗin da ta shiga ne ya sa ma’adanar tunaninta har bawa da ƙarfi wanda ya haddasa mata tafiya wannan dogon hutun. Karka damu, in sha Allah akwai yiwuwar ta warke gabaɗaya ke nan. Nan da awa biyu za ta farfado. Duk yadda ake ciki sai ka kirani na ji.”
“To shi ke nan Dr na gode sosai.”
“Ba komi’e ai yiwa kai ne. Allah ya ƙara rufa mansa asiri.” Ya furta yana mai sunkutar jakar aikinsa.
A gogon ɗakin nasa na nuna ƙarfe 8:00 daidai, Faɗime na buɗe idanuwanta tar! Tana bin saman ɗakin da kallo. Kande ce ta fara kula da ita, da saurinta ta isa gareta tana kwarara mata sannu. Bin ta take da ido kafin kuma ta saukesu kan Sagir da ke gefe ya dafe kansa da hannu. Da sauri ta runtse idanuwanta. Abubuwa da yawa ta tuna na rayuwarta. Abubuwa da yawa kuma ta gaza tunawar. Mafarkin da take gani na daren jiya ya saka ta ƙara gintse idon da ƙarfi dan sam ba ta son tuna mafarkin. Sai dai zafin da taji na ratsata ta ƙasanta ne ya fara daidaita mata tunaninta warto hannun Kande da dukkan ƙarfin da ya rage ma ta. “Kande, ki ce mibi mafarki nake da abinda nake gani, ki ce ban aikata abin da Hajiya ke kwaɓata kansa ba, abinda Allah ke kona mutum kansa, abinda Jummalar ƙauyenmu ta mutu tana yi Maigari ya hana a mata sallah, Kande ce mini mafar…”
Hawayen da taga Kanden na yi ne ya saka ta yin shiru tana kallonta. Miƙewa take ƙoƙarin yi ta yi saurin tare ta tana faɗin.
“Hankali dai ! Hakuri za ki yi Faɗima, mai afkuwa kam ta riga ta afku sai dai gaba a kiyaye faruwar kwatankwacin hakan.”
Kallonta ta tsaya yi da mamaki idanuwanta cike da zafin ciwo.
“Haƙuri fa kika ce? Haƙuri ga wanann azzalumin, macucin? Me na tsare masa da zai zalunci ne har haka? Na rantse da girman Allah ba zan taɓa yafe masa abinda ya mini ba. Ya je in sha Allahu sai ya ɗanɗana ƙuncin da ya fi wanda ya jefa ni ciki.”
Ta ƙarashe tana mai rushewa da kuka.
Cikin ƙunur rai yake dubanta, lalle kam yarinyar nan yadda take a haukanta haka take a zahiri ! Idan ba rainin hankali ba shi ya kawo ta ɗakin ko kuwa jawo ta ya yi ta karfi, ko kuwa zato take ta kai Macen da za a kalla ayi sha’awa. Idan ba azal ba har akwai abin kallo da yarinyar da ko gama sanin ciwomn kanta ba ta yi ba? Dole ma ya yiwa tufkar hanci.
“Kande ɗauketa ku wuce Toilet ɗi na ki gyara mata jikin yadda za ta warware da wuri, ke kuma.”
Ya kallo Faɗime cike da tsana.
“Ba ni na jawo ki ba , ke kika kawo kanki cikin haukanki. Dan haka ko da wasa kika bari Hajiya ko Yaya Abdallah suka san wannan lamari wallahi sai na miki abinda har ki koma ga mahallaccinki ba za ki manta ba. Dan haka ki kiyaye…”
“Har akwai abin da zaka mini wanda ya fi wanann? Wallahi ƙarya kake baka isa kasa na rufa maka asiri dan ina tsoronka ba, sai dai na yi sabida martabar kaina, idan ba ma baƙar zuciya irin taka ba, ba ka yi tunanin ba ni haƙuri kan zaluntata da ka yi ba, sai ƙoƙarin rufa ma kanka asiri? To ban yafe maka ba. Macuci, Azzalumi. “
Ta furta a tsiwace idon ta na kwararar hawaye cike da tsana.
Mamakin tsiwarta da ƙarfin zuciyarta ya daskarar shi gurin. Yarinya tana cikin zafin ciwo amman bakinta bai mutu ba. Lalle kam wanan ya faye matsawa sai tace zata haɗa kwanji da shi dan haka bari ya sarara mata.
A daddafe Kande ta kai ta Toilet ɗin nasa ta gasata sosai yadda za ta ji dadi. Daga inda yake zaunen yana iya jiyo wash! Wash!! Ɗin da take ta ambato.
*****
Tun daga lokacin da wannan abin ya faru Faɗime ta zama wata shiru-shiru cikin ilahirin zuri’ar, daidai da Babban Mutum ta bar sakewa da shi kamar lokutan baya kafin ta warke daga larurarta. Banda Sagir da Kande, ko Hajiya bata san Faɗime ta warke gaba ɗaya daga ciwon ta ba. To, ina ma ta ganta da har za ta fahimci hakan. Kusan kullum tana ɗaki, kuka kuwa shi ne babban amininta da ta ƙulla kyakkyawar alaƙa da shi. Wai ma a hakan dan Kande na fisgar jiki ne ta zo ta yi ta rarrashinta da daɗaɗan kalaman da za su sa ta murmusa. Ga Hajiya kam rashin sukunin Faɗime bai wani shiga jikinta sosai ba dan kuwa inda sabo ai ya ci ace ta saba shekara ba kwana ba. Dan haka tafi aje lamarin a yanayin jikin ne. To, ga Babban Mutum ma hakan ya ɗauka, har ya fara tunanin su koma asibiti ko za a sake dacewa walwalarta ta dawo kamar baya.
Ta ɓangaren Kande kuwa. Kwana biyun nan cikin rashin nutsuwa take da tunane-tunane a duk lokacin da ta ɗora idanuwanta kan Faɗime. sosai take kokawa da zargin da ke zuciyarta, duk da sau da yawa ita kanta tana ƙaryata kanta. To yau ma take a duniyar nan da za ta yaudari kanta? Duk wasu alamomin shigar ciki ta gama karantarsu jikin ƴar Faɗime. Gudun zato ya sakata tafiya ɗakin Faɗime in da ta yi kyakkyawan gani kuwa. Tana ƙoƙarin zira riga a jikinta ta tadda ta, idanuwanta basu sauka ko ina ba sai bisa cikinta da a watanni huɗu baya can kafin wannan azal ɗin ta hau rayuwarta, a shafe yake, shafewar da ke kokarin haɗewar da bayanta, duk kuwa cin abincin da za ta yi hakan ba zai saka shi ɗagowa ba. Maimakon yanzu da ko makahone ya shafa zai ji tudun da ya yi. Sai dai kuma ba ta ƙi tabbatarwa ba dan haka ta hau mata tambayoyi.
“Ni kuwa watan baya kinga baƙon ki, na ga kamar ko yaushe cikin sallah ki ke ciki?”
“Yauwa Baba Kande abinda nake son tambayar Hajiya ke nan sai na manta. Na kusa fin wata huɗu rabo na da shi, ko dai banda lafiya ne dan sanda muna karatu da Hajiyar tana faɗa mini inda yake zama cuta, mutum ya daɗe bai yi ba ko, to duka ma ni yaushe na fara? ” Ta furta tana mai kafa mata idanuwa.
“Shi ke nan kuwa! Yau baragurbin kwan da aka daɗe da binnewa na gabda cika hancin ilahirin mutan gidan da warinsa. Ai kawai sai ta juya tana mai faɗin.
“Ina zuwa Faɗi, bari na sauke miya.”
Kasa zama ta yi, ta dinga safa da marwa tsakar ɗakin nata har zuwa ƙarfe takwas na daren ranar da ta ji shigowar Mai Gayya Mai Aikin. Da sauri ta fita ta ya fito shi, ya kuwa taho yana mai ƙarewa ruɗaɗɗar fuskarta kallo da tun kan ya ji kiran da ake masa daga shigowarsa, har ƙirjinsa ya fara luguden tara-tara. Babban fatansa ya zamana kiran na Alheri ne.
“Lafiya Kande, na ganki kamar ba cikin nutsuwarki ba ?”
“Ai cire kalmar ‘kamar’ ɗin Auta. Da gaske nutsuwar tawa ta ɗauke a tun ranar da na fara fahimtar Faɗima na da shigar ciki. Wanda a yau zargi na ya gama tabbata, ciki gareta har na tsawon wata huɗu. Dan haka zancen ɓoyo ya ƙare, dole yanzu aje a sanar da Hajiyar tunda ga yadda lamarin ya juye…”
“Auta!”
Ta furta da ƙarfi ganin idanuwansa sun kafe kanta, ilai kuwa tun sa’adda ta furta kalmar ciki numfashinsa ya yi fitar daƙiƙu.
“Auta magana fa nake maka!!”
Da ƙarfi ya jawo ɗan wanda ya rage masa yana kallonta, ganin hakan ita ma ta ɗora zancenta.
“Na ce maka sai muje a yiwa Hajiya bayani ta yadda za ta fahimce ka!”
Riƙe kansa ya yi (out of idea) yanzu ina zai samu maganin wannan gagarumar matsalar? Inaa! Sam! Wallahi saboda wata can da har yanzu ba ya sakata a sahun mutane girmansa ba zai zube ba a idon duniya ba. Idan ana cewa iskanci da wani banɗaranci ga Ɗa Namiji ado ne, to gare shi kam ya fi na Mace muni. Saboda haka ko da fitar da ciki na nufin mutuwa gare ta, to sai fa an fitar da shi, kai shi gwara ma ta mutun dan kuwa hutu ce gareta, da dai a ce girmansa ya zube idon Hajiyarsa da ɗumbin jama’ar da yake mu’amala. Shi Sagir ace har yaron gaba da Fatiha gare shi?
“A’a Kande! A zubar dashi kawai!!”
Ya samu bakinsa na furtawa a tsawace.
Hannu bisa ƙirji take kallonsa kafin kuma ta doka salallami.
“Yanzu Sagiru akan rufuwar asirinka kake son kashe ɗiyar mutane? Yo kisa mana, ko baka ji me na ce ba ne? cikin wata huɗu fa na ce ma tana ɗauke da shi. Ta ina za a zubar da abinda a likitancin naku ma haɗari ne, ballan tana irin namu na gargajiya. To wallahi ahir ka sake furta kalmar nan kai tsaye zan je na samu Hajiyar. Wannan ai rashin hankali ne da Imani. “
Yadda maganganunta ke dukan kunnuwansa haka gumi ke tsiyaya a ilahirin fuskarsa suna jiƙa gaban rigarsa. Shiru ya yi yana kallonta kafin kuma wani tunani ya zo masa, da sauri ya daidaita nutsuwarsa yana dubanta a marairaice.
“To shi ke nan Baba Kande, ba za ayi abinda ba ki so ba, amman a yau na sake haɗaki da girman Allah ki rufa mini asiri kar Hajiya ta ji zancen cikin nan. Ni kuma zan ɗau Fatiman can garinsu gaban danginta a hankali sai ina zuwa dubo su harta haifu. Idan ya so bayan na yi aure sai in ɗauko abinda aka samun in rike shi gurina da sigar tsintarshi na yi. Su Hajiya ko idan naga hankalinsu ya tashi da ɓatan Fatiman. Cikin hankali ni kuma sai in gwada musu ƙila ta gudu garinsu ne, nasan Hajiya za ta so ganinta. To da kaina ma zan kaita harke dan ki tabbatar ban fada miki hakan dan na siyar da Fati ba!”
Aka ce Ɓakauye idan ya shigo birni sai ya yi shekara Arba’in zai manta abinda ya haɗiya na ƙauyancin. To, ina ga Baba Kande da ke da shekara goma kacal? Ai nan da nan ta sakar masa murmushi har da gode wa Allah.
“Shi ke nan kuwa Auta, har na ji hankalina ya kwanta. Ka ga shi ke nan kai ma ba ka bar Yarinya da wahala ba yadda za ta rasa mijin aure. Ai cikin shege a ƙauye, daidai yake da ka tarkata kayanka kaf! Ka faɗa duniyar kowa yasan ita ka fito ci. Jifan yara kaɗai ya isa ya hanaka zama lafiya. Kaga kuwa hakan da zaka yi yafi kome adalci gurin yarinyar tunda kowa ya ga ubansa yana zuwa. In dai wannan ne to sirrinka ba zai taɓa fita ba daga baki na. Fatana kaji tsoron Allah ka yi abinda ka ce.”
A daren ranar Sagir kasa barci ya yi saboda tsantsan tashin hankalin da yake ciki. Ƙarfe huɗu da rabi daidai ya miƙe gami da dosar ɗakin Faɗimen. A hankali ya buɗe ɗakin nata yana mai danna kansa ciki. Ga mamakinsa kwan ɗakin a kunne yake tar da wadataccen haske, mamakin bai gama kashe shi ba, sai da ya hangeta tsakiyar gadonta hannunta cike da madara tana lasa a hankali idanuwanta a lumshe alamun tana jin daɗin Madarar. Tsai! Ya yi yana ƙare mata kallo wani irin abu na yawo cikin jininsa zuwa zuciyarsa. Wani irin kyawu ya ga ta masa, kyawun da bai taɓa sanin tana da shi ba, ko kuma duk cikin ne ya sa hakan? masani sai Allah. Shi idan ba yanzu ba, bai taɓa tsayuwar minti biyu ya kalleta ba. Yanzu ko ya shagala sosai cikin wani ruɗaɗɗan tunani da yake ta ƙoƙarin yaƙarsa cikin zuciyarsa.
A jikinta ta ji kamar ana kallonta, dan haka ta buɗe lumsassun idanuwan nata da basu sauka ko’ina ba, sai a fuskar maƙiyin nata dake tsaye bakin ƙofar rungume da hannayensa yana ƙare mata kallo.
Da sauri ta yi fatali da Madarar gami da hantsilowa daga gadon nata tana mai doka masa harara cike da tsiwa.
“Fita! Ka fita wallahi tunkan na maka ihun da Hajiya da za ta fito. Oh wani iskancin kazo ka sake mini ko macuci, to Allah ya kama ka banyi barci ba, kai wanda ka shigo ina barcin ma ban yafe ba, mugu kawai mai son zuciyar…”
Hannun da ya sa ya toshe mata baki da karfi yana mai jingina ta jikin bangon ɗakin ya sakata yin shiru ta fara kokawar ƙwacewa. Cikin huci da masifa yake kallonta yana mamakin yadda kowanne lokaci shi take bawa lefin tsabar raini.
“Ke kika fara ba ni ƙofa, saboda haka ki daina blaming ɗina fault ne dukanmu muna da shi. Ke ni ba ma wannan ne ya kawo ni ba. Faɗa miki zanyi a dalilin shigowarki rayuwata ga babbar riba nan kin samu ta CIKIN SHEGE. Eh! Cikin shege mana, tunda idan sama da ƙasa za ta haɗu babu wanda ya isa ya saka na karɓe shi a matsayin nawa. Ai kin saba jin kalmar CIKIN SHEGEN a ƙauyenku ko? “
Ya furta yana kallon idanuwanta ganin tunda ya ambaci ciki tabar kokawa da hannunsa ta koma da numfashinta da ke ƙoƙarin ficewa.
“To, irin shi nake nufin kina da. Dan haka ki gaggauta biyo ni cikin rufin asiri muje a markaɗe shi ya bi rariya, ko kuma ki yi gaggawar barin gidan nan tun kafin Hajiya ta farga. Ki kuma nema wa abinda za ki haifa ubansa wanda ba ni Sagir Muhammad Makarfi ba.”
Ya ƙarasa yana mai sauke hannunsa daga bakinta.
Zamewa tayi daga bangon a hankali ta zube dabas bisa dandanyar ɗakin. Da ƙarfi ta tsoshe bakinta idanuwanta na kwararan hawayen da maimakon ta ji sanyi, zafinsu take ji. Wai ita ‘yar Faɗimen nan ke da ciki. Kai! Lokuta da yawa ƙaddara ma bata san inda take zuwa ba. Ina za ta kai wannan ɗumbin abin kunyar? Me za ta cewa matar da ta ɗau son duniyar nan ta bata kusan fiye da wanda take gwada ma ‘ya’yanta. Su zubar! Kamar yadda wannan mai baƙar zuciyar ya faɗa. To amman fa ‘yan shekarunta ta san yin hakan ba ƙaramin ganganci ba ne. Ta yiwu ta mutu wurin zubarwar kamar yadda Ramatu ƙawarsu ta mutu gurin zubar da nata, ta yiwu kuma ya ja mata sanadin da ba za ta taɓa wani cikin ba. To ai ita ma haifarta aka yi, dan haka tunda ta haɗiya kam, dole ta yi hakurin amayar shi. Kai! Lefi biyu ma ke nan. Ga zina ga kisan kai ! Tunda dai zubar ciki ai kashe raine. Inaaa! Ita kam ba za ta zubar ba, ba kuma za ta zauna ta haife ma Hajiya jikan gaba da Fatiha ba. Ai ba ta cika mutum ba ma idan ta ma Hajiyar haka duba da irin riƙon da ta mata wanda ko gurin ubanta Mahaifi ba ta samu irinsa ba, ki tafi kawai inda zaki haife shi, ke rene shi, ki ba shi tarbiyya irin wacce Hajiya ta baki, To ina za ta tafi ? Masani kam sai Allah. Sai kawai ta tattaro gaban rigarta gami da ƙara cusawa cikin bakinta tana mai sakin gunjin kuka.
“Yammata ba kuka za ki yi ba, tashi zaki yi mu yi abinda zai fisshemu gaba ɗaya. Idan ba haka ba kuwa kuka baki fara shi ba ma, tukunna dai! “
Wai aka ce idan kaga ƙi gudu, to sa gudu ne bai zo ba. Dan haka ko kallonsa ba ta yi ba bare ya sa ran jin amsa, ta miƙe da gaggawa gami da dosar gurin kayanta ta fara zarowa tana ɗura su cikin ƙaramar jakar da ta ciro cikin (drawer). Ko bai tambaya ba ya san ta zaɓi ta tafin ke nan akan su zubar.
To fine! Shi idan ta shi ne ma hakan zai fi masa daɗi, akan ta zauna yana ganinta koyaushe tana tuna masa da wannan mummunan abun.
Ita kam haɗa kayanta kawai take da duk wanda hannunta ya kai har sai da ta cika jakar yadda za ta iya ɗauka. Garin ta jawo hijabin da zata zira jikinta ne wata ninkakkiyar dubu gudu ta faɗo, wacce idan bata manta ba Babban Mutum ya bata da daɗewa wai ko zata sai wani abin, ita kuwa sanin ba ta buƙatar kome ya sa ta jefata cikin shirginta. A yanzu kuwa jin faɗowarta da sauri ta ɗauketa tana mai cusa ta Aljihun jakar.
Sai da takai bakin ƙofar ɗakin p yana tsaye yana kallonta tukunna ta juyo tana kallonsa da rinannun idanuwanta, kafin kuma ta sakar masa murmushi.
“Zan tafi Sagir kamar yadda ka ba ni zabi. Amman ka sani da yardar mai kowa da komai yadda ƙafata ta fita daga ɗakin nan, haka duk wani jindadi da farin ciki zai fita daga taka rayuwar ka dawwama cikin baƙin ciki da da na sani. Ciki kuwa da kake cewa in nemi ubansa wallahi kayi kaɗan, daga yau na ɗau maka alƙawarin zan dinga sanar masa labarin azzalumin uban nasa tun yana cikin, har zuwa ranar da zai mallaki hankalin kansa da mummunar tsanarka! Tana zuwa nan ta buɗe ƙofar gami da ficewa cikin sassarfa.
Bin ta da ido kawai ya yi ƙirjinsa na luguden kalamanta. A can wani ɓari na zuciyarsa na gargaɗinsa da bai kyauta ba fa! kar ya bari ta tafi. Sai dai maimaikon ya yi abinda ake kwaɓarsa, sai ya samu kansa da buɗe tagar ɗakin nata yana mai kallon farfajiyar cikin gidan. A kan idonsa ta buɗe ƙofaŕ cikin sanɗa tana kallon Ilu da ya zagaya bayan gida. Akan idonsa kuma ta fice daga gidan babu ko waiwaye.
Sauke nannauyan numfashi ya yi yana mai tsirawa (gate) ɗin ido. Ta yiwu watarana ya sake ganinta, ta yiwu kuma ta tafi ke nan har abada! Danshi-danshin da ya ji saman laɓɓansa ya saka shi kallon glass ɗin tagar da hanzari yana mamakin abinda ya haddasa masa zubar hawaye. Maimakon farin ciki da tafiyar Faɗi daga rayuwarsa. Da sauri-da sauri ya hau sharewa yana mai ƙaryata zuciyarsa abinda take saƙa masa kan wanann yarinyar da ko takaddar (Primary) bata mallaka ba! Fatansa ya tafi kan kar ya ƙara tozali da ita daga nan har ƙarshen rayuwarsa. Sai dai bai san cewa akwai ƙaddara mai girman da za ta sake haɗa su ba!