Skip to content
Part 9 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Tana fice wa daga gidan ta ji gaba ɗaya duniyar ta mata zafi, shi ke nan ita yanzu ba ta da kowa ba ta da kome a duniya. Haka ta dinga jin taje ta yi zamanta ita kaɗai babu kowa cikin rayuwarta. Tafiya kawai take bata san inda za ta je ba. Ko kaɗan ba ta sama ranta za ta koma gidan Uwale ba, ba ta gama amfanin komawar  ba a yanzu da take cikin bala’in da ya datse mata dukkan farin ciki da cikar burinta, ya kuma illata rayuwata gaba ɗaya ya kassara. Haka ta dinga tafiya daga wannan gurin zuwa wancan guri cikin farar asubar da babu mutane balle abin hawa. Sai da garin ya yi shaa ta isa bakin titi ta tsaida ɗan Taxi.

“Tasha nake so ka kai ni.” Ta samu kanta da furtawa ba tare da ta san sa’adda kalmomin suka samar da kansu ba. Sai da ya ƙare mata daga ƙasa har sama tukunna ya ce ; “Ɗari biyar !” Ba ta ko kalle shi ba ta buɗe motar ta shige.

Sanda suka isa ya yi daidai da sanda wani karan mota ya buɗe bakinsa da dukkanin muryar da Allah ya masa yana cewa. “Ina na Maiduguri, sauran mutum guda ta tashi.” Jin haka ya sa da sauri ta warci guntun canjinta ta doshi karan motar. Ba ta san garin ba, kai ita ba ma inda ta sani. Sai dai Maidugurin da ya ambata ta tabbata ta sha jin sunan a TV da kuma Radio. 

Shi ma ganin ta taho ya saka shi yin shiru yana ƙare mata kallo, tana isa ya karɓe jekar hannunta gami da bata hanya ta shige cikin motar.  Shigowar yayi ya zauna a mazauninsa yana mai tattara kuɗin motar har ya isa kan ‘yar Faɗime da tunda taga ana miƙa kuɗi ta fara neman abin faɗa, cikin sanyin jiki ta mika masa sauran ɗari biyar din dake hannunta. Kallonta ya yi sheƙeƙe sai kuma ya buɗe motar da gaggawa.

“Zo ki fi ce cikin rufin asirinki.”

“Dan Allah ka yi hakuri ka kai ni, suke nan gare ni wallahi.”

“Ai nasan su kaɗai din gareki, shi ya sa ma na ce ki fita , tun kafin ki fara mini magiyar da ire-irenku ke yi.”

Shiru ta yi cikin fidda tsammani, sai kuma ta miƙe tana kokarin fitar.

“Bara na ba si , idan yaso idan muka isa Tashan Kano sai ki karɓa gun yan uwanki ki ba ni.”

Wata jibgegiyar mata mai zubin yan ogbomosho ta faɗi. Kafin ta hana ta harta miƙa masa, shi kuma ya warce. Dan haka ta zauna tana ƙarewa zanen dake fuskar matan kallo, a hankali kuma sai ta ce “Na gode.”

“Sunana Maama Rizban. ” Matan ta faɗi mata fuskanta ɗauke da murmushin dake ƙara mata muni. 

“Faɗima.” Ita ma ta ba ta amsa ta na mata yaƙe.

Da yake barci ba shi da zuciya, kuma ba a ɗaukan bashin sa, kamar yadda babu ruwansa da wani tashin hankali ko rashin nutsuwa, haka nan ya saɗaɗo ya sace Fadime ta fara sheƙa shi kamar wacce karya da Farfesun  Naman Ɗawisu. 

Fasi! Fasi!! Tasi mun iso Borno, gamu cikin Tashan Kano, fito ki karɓar mini kuɗi na. Firgit ta farka daga nannauyan barcin  tana kallon Maama Rizban dake tsaye kanta. A tare suka fito daga motar, nan kuma fa ta tsaya tana neman abin faɗa. Ita ɗinma kallonta take yi ganin ta ja tsaya.

“Mama ni fa ba ni da kowa nan gurin, kawai na zo ne.”

“La ku kuji munafukin yaro, sine ka bari na bada kuɗi na baka faɗi mini ba? “

“Ina garinku, mai ya fito da kai daga gidanku ka zo inda baka sani ba?”

Shiru tayi kanta na kallon ƙasa rashin abin cewa. Ganin ya hakan Maman.

ta hau kallonta daga sama zuwa ƙasa.

“Ayya na gane, sai ka ce mini ciki kayo, yarenku da basu karɓar ƙaddara suka kore ka, so ni ba ruwana da koma mene ne, ka saki jikinka muje gidana sai ka dinga taya ni aikin da nake yi, ka biya ni kuɗina, kai ma ka tarawa kanka yadda zaka kula da Babynka.” 

Da sauri ta ɗago tana kallonta cikin murmushi jin zancenta.

“Shi ke nan Mama na yarda, na kuma gode sosai.”

“Ba komi Fasi ai yiwa kaine, ka ga dama ba ni da ɗiya mace fa, Rizban kaɗai gare ni shi kuma baya son aiki sam-sam. Babansa ma dake taya ni yau shekararsa biyu da mutuwa boko haram suka kashesi. To ɗauki wancan ƙullin a kanki mu tafi.” 

Ta furta tana mai nuna mata wani ƙaton buhu da ta cika rabinsa da kaya. Faɗime ko kallon buhun ta yi ta dawo ga kallonta ga Maama Rizban ɗin. Wai ! ita kam ba ta iya tuna rabonta da aikin wahala, balle ɗaga wanann nannauyan buhun.

‘UHUM! Faɗime duniya fa kika shigo, dan haka dole ki jure duk abinda zaki tarar cikinta. Abubuwan mamaki baki fara ganinsu ba ma.’ Wata zuciyarta ta ankararta hakan.

Ba su daɗe da hawa Napep ba suka iso unguwarsu Mama Rizban ɗin, Madganary. Madganary unguwa ce da ta haɗa zallan ƙabilu mabanbanta nan cikin Barnon. Gidan haya ne inda Maama take da ɗakinta falle guda tal, dan girki ma sai a kofar ɗaki suke yi, idan lokacin damina ne kuma su yi daga bakin ƙofar  ta ciki. 

Haka nan ta buɗe ɗakin Faɗime ta shige ciki. Ita kuma ta hau sanar da makwaftanta ga ɗiyar ƙanwarta ta ɗauko, sunanta Fasi. Riƙe baki suka yi gaba daya suna mamakin wanann iko na lillahi azza wa jallah. Yo banda abin Maama Rizban ai ko Makaho ya shafa fuskartà gurin ɗima-ɗiman zanenta, ya kuma shafa fuskar kyakkyawar Faɗime, zai san babu wata alaƙa ta jini a nan gurin. Amman sanin wacece Maama da kata’inta sai suka hau taya ta murna. Sun san indai ana tare da kanta zata tonama kanta asiri. Bari dai ta haɗosu da yar budurwar.

<< Fadime 8Fadime 10 >>

1 thought on “Fadime 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×