NUMFASHINA
Sahibata ‘yar baiwa,
A gare ni kin zarce kowa.
Numfashina ya yi ƙaura,
Yau ke kaɗai zai tunkara.
Tun sa’adda na hango ki,
Ki ka sace Numfashina.
Ƙaunarki ta bi jikina,
Kin zamo sashen raina.
A ƙaunarki na yo nisa,
Tunaninki ba zan fasa ba.
Ke ce cikin birnina,
Ƙaunarki ce zaɓina.
A ko yaushe nai numfashi,
Ƙamshin ki ne yake tashi.
Akan sonki na zamo kurma,
Kogin sonki na yo kurme.
Begenki ya fi min komai,
Ke ce gyaɗa ni kuma mai.
Na baki numfashina,
Kin fi shi har ma raina.
Mai rini sai ya je marina,
Ke ko kina cikin raina.
A so na zamo hankaka,
Daure ki zamto shirwa.
Gani kan gwiwoyina,
Daure ki ceto raina.
In na same ki na haura,
Matakin biɗa ko nema.