Skip to content
Part 11 of 30 in the Series Falsafa by Mujaheed Matashi

11 HUKUNCIN ALLAH

01.

Allahu gwani mai hikima, kai ne a farkon farawa.

02.

Daga ɗan mutum har bishiya, kai ne ka ke fa ba su ruwa.

03.

Aljanu har da Mala’iku, kai ke da ikon halittawa.

04.

Idan mun yi laifi ya Allah, gareka muke neman yafewa.

05.

Don mun riga yi imani, kai ke da ikon shiryarwa.

06.

Tsira da aminci mai yawa, a gare shi jinin Hashimawa.

07.

Ba ya nuna bambanci, a tsakanin ɗa shi da bawa.

08.

Shi ya horas da mu kyauta, kuma yai hani da yin rowa.

09.

Salatinsa ya Allah, nake roƙo Rabbi ka ƙara ninkawa.

10.

Sau ba adadi yawan yashi, da duk wani ɗigo na ruwa.

11.

Daga cikin hukuncin Allah, wasu ga su nan da burgewa. 

12.

Wasu ko da ka yo duba, wallahi ba ka ƙarawa. 

13.

A cikin tsirrai da bishiya, wasu nan muke yin hutawa. 

14.

Wasu da zarar ka gansu, sai ka ji suna da ban sha’awa. 

15.

A cikinsu ɗin dai kuma, mukan samu magani na cutarwa. 

16.

Hatta dabbobi ɗan Adamu, gare su ka yo dubawa. 

17.

Wasu na sama wasu a ƙasa, wasu ko suna ciki na ruwa. 

18.

Wasu har ka aje su gida, don kawai suna da burgewa. 

19.

Wasu kuma an yarje maka, ina ka so kana iya yankawa. 

20.

Wasu ko da zarar sun ganka, sai su yi nufi na cutarwa. 

21

Duk abin da ka so ya Allah, shi ne ka ke zartarwa.

22.

Babu mai fushi ko gunguni, balle ya samu dama ta hanawa.

23.

Kai ne Ar-Razzaƙu Allah, in ka so kai azurtawa.

24.

A cikin ikonKa Mannanu, in ka so kai talautawa.

25.

Roƙon da muke ya Fattahu, a gare mu ka yo buɗuwa.

26.

Lamarin na Al-Mautu, koyaushe nake ta fa tunawa.

27.

Ko na ƙi ko da na so, watarana za na gushewa.

28.

Sai dai ga masoyana, na zamo abin nan na tunawa.

29.

Sai rubutun nan da na yi, wataƙil a zam karantawa.

30.

Ko ‘ya’yana idan na bari, aka gansu a zan kwatantawa.

<< Falsafa 10Falsafa 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×