Skip to content
Part 12 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

HAUSA DA HAUSAWA 

 1. 

Da sunan Allah nake farawa, Jalla wanda ya yo Hausawa.

 2. 

Tsira da aminci mai yawa, gare shi shugaban Annabawa.

 3. 

Zan yi kira gare mu ‘yan’uwa, ma’ana al’ummar Hausawa.

 4. 

Domin mu zan dagewa, bisa al’adarmu ta Hausawa.

 5. 

Kada mu zan sarewa, da ruɗin ra’ayin Turawa.

 6. 

Halinmu mu zan gyarawa, kar mu bari ya zan lalacewa.

 7. 

Kada mu zamo abin nunawa, cikin ‘yan’uwa abin yasarwa. 

 8. 

Yau mun bar noman maiwa, sai shinkafa muke nomawa.

 9. 

Ba ma sa ko da taguwa, sai kayan Ingilishi muke sanyawa.

10.

Ba ma cin tuwo ko ƙwaya, Indomie muke girkawa.

11.

Ba ma shan kunu ko koko, sai ƙwaya muke ta afawa.

12.

Wasunmu sai zaman banza, aikin yi ba ma dubawa.

13.

Kai wannan abu dai kwai ciwo, ka ga naka yana lalacewa.

14. 

Ya kamata mu zan miƙewa, domin gyaran dukkan rayuwa.

15.

Rayuwar dukkan Hausawa, waɗanda su ne fuskar Afirkawa.

16.

Allah ya taimake mu ‘yan’uwa, ya cika burikan duka Hausawa.

17.

Na gida ne ko na dawa, naka naka ne ko a ruwa. 

<< Falsafa 11Falsafa 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×