MARUBUCIYA
Duk da ƙauna gaibu ce ba ta ɓulla kan jiki,
Daf da ke na gane so ya riƙe hantar ciki.
Babu so in ba sila wadda ruhi zai riƙa,
Ba jira, ke ce silar sanya zuciya tai tiƙa.
Mintuna biyu ni da ke sun fi sa’o’i ɗari,
Murmushinki ko sai ka ce hurul-aini a ƙabari.
Duniyar hangenki kan kalli bayan duniya,
Dole masu gwaji da ke su yi jira sai kin tsaya.
Kaifafar nazarinki na tsoratar da matambayi,
Kan faɗin furucinki fuskarsa kan shiga laulayi.
Yunƙurin sukuwa da harshenki kan yi na lokaci,
Yai kama da ɓarin ƙasa mai niƙe tsauni ta ci.
Tawwadar iliminki kin ɗiɗɗisa na ɗosana,
Ta lazamta jiƙar faƙon maƙoshi da idanduna.
Tun da alƙalaminki ke zana zanen ƙaddara
To ki yarda da nawa in zantuka a ƙaburbura.
Nan ga ke kalma take ya da zango duk dare,
Nan fa mai waƙa yana ta hushin so i na kare.
Kar ki ce kin bar garina kina neman gida,
Ko ina kika je cikin tunanina ne: gida.
So da gigitarsa, ƙauna, kulawa, shaƙuwa,
Su suke sa ba ni so in ga ga ki a damuwa.
Kar ki manta ni da ke babu so(n) rai fatima,
Sai kawai so wanda mu ɗai biyun muka tsunduma.