SHAIƊANIYA
Ashe nan cikin so kwai jidali laya-laya,
Kamar ke a suffar ƙi da yanayi na kwalliya.
Halittarki tamkar rijiya mai bakan gizo,
A zo gunki kau da ƙishi ki tattatse jijiya,
A fuskarki ga haske da ke jan samartaka,
Da an so a kalla sai ta ƙone idaniya.
Magananki rana ma tana so su wulƙina,
Turakunsu ɗauka ɗai suke kama zuciya.
Da hanci kike shaƙar furanni da sun fita,
Ki maishe su bayi kin kasa sun ji sun siya.
Kumatunki lallausa kamar an yi shimfiɗa,
Na ce sai ka ce ɗanyen ɗiyoyi na lubiya.
Da sauti tsakanin leɓukan nan ya kanari,
Da an so a sumbata a tsotso baƙar wuya.
Ina son ki tamkar son mayafin baturiya,
Kamar son jiran asuba ta bijiro da safiya.
Ina ƙin ki tamkar ƙin tabo gun macijiya,
Gubar sonki kam ta saka na ce kin fi mujiya.
Idan kuma na ce shaiɗaniya sai a ce da ni,
Ka duba irinta guda da ka bar ta sai tsiya.
A guna kamar fadamar taɓo ce in tsallaka,
Ta ya zan tsaya wanka da soson farar ƙaya?
Na ce mai biyar bayanki ɗin bai da hanakali,
Ina nan, kina can, so tsakaninmu ya tsaya.
Makafin idanu naki sun gan ni cif da ni,
Suke so su cicciɓa zuciya kan hasumiya.
Ki ɗauken a ranata ki ɗora ni can bisa,
Ki sauke ni sanda dare ya zon babu walƙiya.