Skip to content
Part 15 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

BEGEN MUHAMMADU 

Begen Muhammadu ya cika min zuciya,

A cikinta ba sauran muhalli ko ɗaya.

Ya shanye ɓargo har ruwan sassan jiki,

Ba ɗai da yai saura wa rai ko zuciya.

Ƙauna da kewa sun wadata a zuciya,

Ga nan tsumayi naka ya sa na tsaya.

Zaƙi na so nasa ya fi saƙaƙƙar zuma,

Wane tufa wane fa ƴaƴan lubiya.

Na so ka ɗaha kamar macijin sauratu,

Da ya so shahada tai gaban siddiƙiya.

Na so in zauna nan gabanka in sunkuya,

Sai ga shi na jinkirta in zo duniya.

Na so ka tamkar wanda yai hijira ya bar,

Son ransa don ƙaunarka sarkin duniya.

Ko so idan ɗan rijiya ya so fita,

So wanda sarƙa tai ta zarge zuciya.

Na so ka tamkar sanda bawa yai nufi,

Ya biya wa fansa tai da so komai wuya.

Misbahu ka faku tun gabanin ni in zo,

Kullum in nema in ganka a gaibiya.

In nai kira ka zo gare ni da sallama,

Raina ya amsa in ji so ya kewaya.

Na roƙi Rabbu ya ƙara ninka buƙatuwa,

Ta ganinka randa ruwa ya toshe idaniya.

Na ya da masu guri a zuci guda takwas,

Na kama zaɓin khaliƙi kuma na tsaya.

Ita zuci in tai gargaɗin gaɓɓan jiki,

Kar ɗai ta kai ta ga inda ba ka tajalliya.

Ta zam nutsattsa wadda Rabbu yake faɗa,

Ta je gare shi a radhiya kuma mardhiya.

Mukhtari ga wani taliki ya raunata,

Kullum da sonka tufar jiki ke kwalliya.

Wataran mafarki yai silar sado da kai,

Wata ran da soyayya yake ta ɗawainiya.

Wataran dare haka za ya ƙare ƙulafuci,

Zance da zuciya sai ya kai har safiya.

In nai bara a kufai fa wai wa za ya ji?

Sai dai in kai kuka gidan ta’aziyya.

Wa za ya nunan kai ya ce min zo ka ga-

Zo ga masoyin naka nai ma inkiya.

Na san da jinƙai nasa to zai tausaya.

Zai ce da ni ya karɓi saƙon zuciya.

In na bi jika sidi Abdulƙadiri,

Ya kai ni har fada ta Nana Sharifiya.

<< Falsafa 14Falsafa 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×