Skip to content
Part 16 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

SOYAYYA TA SAUKA DA KANTA 

Ga wani haske nan ya doso,

Yai zango kan dutsen Dala.

Ya yi buruzi ya nannashe,

Ya rarratso har ta Makwalla,

Sanda na gan shi a sa’in farko,

Tamkar taurarin Angola.

Ni ko na ce ga goshin rana,

Wanda ya ƙoshi da hasken salla.

Sai da ta zo daf to fa na gane,

Hasken fuskar kyau ne zalla.

Ga ta jikinta kamar na mutane,

Amma fatar ta fi tagulla.

Nai duba i zuwa goshinta,

Tamkar taurari na talla.

Ga jerin gashi na girarta,

Sun yi ruku’i sala-sala.

Malam ko da na hangi idonta,

Sai na ji ta jefa ni a mala.

Don a cikinsa a kwai wani kwarmi,

Kai ka ce an adana ƙwalla.

In ta ɗaga su ta kalli sama’u,

Har malakai sa ce la hula.

Sanda ta lumshe sai na tsugunna,

Nai ta kirarin sunan Laila.

Tabbas wannan in ta rutsa ni,

Yawu ya cika babbar kwalla.

In ko ta ƙyale gyalenta ya faɗi,

Du azumina sai na ɓalla.

Kafin hudowar almuru,

Sai ta kwance abin da na ƙulla.

Ko igiya ce ko ko mazagi,

Ba su tsare yaro amalala.

<< Falsafa 15Falsafa 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×