TA’AL
Wani lambu ya yi,
gayyata
Yiriri! Ciki dausayi,
nata
Ƙwace, satar samartaka ƴar yarinya ki rausaya.
Ki ga,
A ciki na ga mangwaro,
Ɓaro
Hannuwa biyu na taro,
Ciro
Muka binne ɗan tsiro fatan ƴaƴa ambaliya.
Tumɓur!
Wasan tashen dare,
da ke
Rowar ƙamshin fure,
Kike
Ki tsaya ni in tad da ke mu keta dare mu ga safiya.
Ki sha,
Ɓaure a ƙasan ruwa,
Batso
Goro da bagaruwa,
gatso
Tauna, tono ciki, matso in ciɓa ki taɓo hasumiya.
Taɓo,
Ƙwaryar sama ta cika,
tsi-tsir,
Kadara a cikin jaka,
titir
Luddai ya tsallaka ya sha garar wata sufiya.
Tsaya,
Hancin kwiɓin zani,
ware
Tsifar saƙar sani,
zare
Jigida ɗamarar gini, cire ki haɗa ta faɗa da zariya.
Uhm!
Kin damƙe kwari cikin,
baka
Don adana so cikin,
Ɗaka
Kin hure wutar cikin dare, kwanan guga a rijiya.
Jira,
Mu yi zance durƙuso,
Raɗa
Zancen jiya ne na so,
Daɗa
In faɗa miki na iso, tsarabar saukar kogin samaniya.