Skip to content
Part 20 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

KURMAN ZANCE

Da farko sai mu ce Allahu

Wanda ya bi shi ba ya ihu

Sarkina gwani mai mulki

Da Manzona mai kirki

Ku ne kaɗai a cikin ruhina, hakan ya sa ba ni da kaico.

Fura a dage a yi damu

Sannu da aiki malam hannu

Huɗa ta yi kyau sai shanu

Wasu sai dai a sa musu hannu

Kurman zance ne a bakina, mai hikima ne za ya hakaito.

A shanye mai da ƙari sai dambu

‘Yan dambe ne ke ɗaura kambu

Manoman rani kuwa sai lambu

Allah ya jiƙan Malam Shu’aibu

A cikin zancena ku duba, hikimar da na rawaito.

Ingilishi mu dage mu koya

Laraci kar mu barshi baya 

Ko ‘sit down here’ ne in ka iya

Ko ‘fasbir sabran jamilan’ 

In dai har kun bi batuna, to na san ba ku da kaico. 

<< Falsafa 19Falsafa 21 >>

1 thought on “Falsafa 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.