HALIN ZUCIYA
Na shaida da ɗaukaka sa’i ce,
Yaro sannu-sannu ke tasawa,
Yin furuci da shirya sabon zance,
Zurfin ilimi yake aunawa,
Yau sabon salon zirin waƙa ce,
Zan yi ga masu kunnuwan ganewa,
Domin inuwa ga mai haskawa,
Mai dattin ido ba zai hango ba.
Aiki na zama bisan niyya ne,
Tushen karsashi yake somawa,
Sa himma kamar gudun doki ne,
Kwai bigiren da ke nufin cimmawa,
Ba tafiya ga wanda ke nan zaune,
Har sai ya yi yunƙurin miƙewa,
Linzami na zuci mai tsinkewa,
In ka sake shi to ba zai dawo ba.
Jigona, abin nufi tushena,
Ya tsinkayi me nake ɓoyewa,
Ƙarfin shaƙuwa a kan burina,
Ya jinkirta samuwar yarjewa,
Ƙarshe gaskiyar cikin ruhina,
Ta rinjayi duk abin kushewa,
Amma na gaza wurin nunawa,
Zimmata ba za ta ban komai ba.
Rayi tawa yanzu ta lalace,
Turbar rayuwa take kamawa,
Har ɗaukantuwa take kai ka ce,
Zatin sonta ne yake dosowa,
Ta ƙyale jikinta ya susuce,
Ya manta a me yake motsawa,
Yanzu ina garen tudun dafawa!
In ba Kai ba ban gano kowa ba.
Haunina da dama in nai hange,
Fuskar walwala nake iskewa,
Don in kwaikwaya nakan daddage,
Fuskar murmushi nake nunawa,
Bai mai ankara da ƙullin zarge,
Wanda ya sa ido yake bushewa,
Sai ɗaiku kaɗan abin irgawa,
Ma su farin ido da saurin tuba.
Mai so bai zama cikin hutawa,
Sai ya sami tabbacin amsawa,
Kullum dai ƙulafucin zantawa,
Ko su haɗe a so ta suffar kewa,
Ko in bi duniya cikin zaucewa,
Sa ran za ta kai ni mui ganawa,
Wannan zuciya abar rainawa,
In ta ɓace a sonKa ban fansa ba.
Ba Ka cikin ido na tsinkayena,
Ba Ka a hankalin da ke aunawa,
Haske naKa ya bice sirrina,
Ko na bi shi gun Ka ban riskewa,
Sai dai laluben duhun ruhina,
Ko zan gan Ka kan zuwan wayewa,
Har asuba ta zan ina runtsawa,
Haka zan tashi ban ishe komi ba.
Ni ɗin ba Kalimi ba mai sanda,
Balle mui mukhaɗaba ba kowa,
Ni ban kai khalili ba na yadda,
Balle in kira Ka yo amsawa,
Ba ni cikin waɗanda Kab ba yarda,
Wanda Ka ba su tabbacin dacewa,
Bawa ne gare Ka mai duƙawa,
Wanda barinKa bai riƙe kowa ba.
Ƙofofi waɗansu na nan buɗe,
Nasara na ciki tana leƙowa,
Igiyar ƙaddara ta kan tattaɗe–
Gwiwa sanda nai nufin miƙewa,
Ko na yunƙura in zo, na harɗe,
Cewar lokaci yana nan zowa,
Sai in addu’a in cikin sarewa,
Allah taimake ni ba don ni ba.
Halin zuciya idan ya cushe,
Ko ya warware ana ganewa,
Hanyoyin fitarsa na nan rashe,
Wani waƙa yake yana rerawa,
Kwai laifi ga wanda ke nan kwance–
Ɗaki wai yana nufin dacewa(?)
Hujjoji waɗansu ke kamawa,
Tsarin rayuwarsu allon duba.
Ni gun Rabbana nake komawa,
Ko ba yai da ni ba zan dawo ba.
Astagfirullah!