Skip to content
Part 22 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

MACE 

Mace ba saƙago ce ba

Mace ba baiwa ce ba

Mace ba karya ce ba

Mace ba ‘yar tsana ce ba

Mace ba halittar rainawa ba.

Mace na buƙatar ƙauna

Mace na buƙatar kulawa

Mace na son tarairaya

Mace na buƙatar tausayawa

Mace na son kyautatawa.

Mace uwar al’umma ce

Mace sirrin tarbiyya ce

Mace ruhin ahali ce

Mace majinginar duniya ce

Mace kimarta mai girma ce.

Bai kamata a ke dukanta ba

Bai kamata a ke sa ta kuka ba

Bai kamata a zalunce ta ba

Bai dace a barta a damuwa ba

Kuma ba ta cancanci uƙuba ba.

Mace in tana haila ta ji zafi

Mace wurin kwanciya ta ji zafi

In ta samu rabo na ma zafi

Wurin haihuwa ma akwai zafi

Shi ma rainon dai zafi ne.

Wannan ma kaɗai ya ishe ta

Ya isa jarabawar rayuwarta

Daga haihuwa har mutuwarta

Al’umma take yi wa bauta

‘Yan’uwa mu zam girmama mata.

<< Falsafa 21Falsafa 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.