Skip to content
Part 25 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

ZAZZAƁIN TUNKIYA 

Zazzaɓin tunkiya, ba ruwan akuya.

Ciwon cikin mujiya, ba ruwan saniya.

Mutuwar beguwa, dariyar bushiya.

Sarkin yaƙin Nijeriya, Bala ya iya dariya.

Alfarmar taliya, yau ga shi mun yi ɗan wuya.

Zazzaɓin tunkiya, ya jawo mun sha wuya.

Makauniyar tunkiya, ta ja mun zagaye duniya.

Aunty taliya, ki barmu mu wataya.

Talili taliya, an dai haɗa ta da jar miya.

Ga wata baƙar kaza, amma da bindin tunkiya.

Lamarin haurobiya, ya zamo hauragiya.

Ga kuma tunkiya, ta kwanta ba ta da lafiya.

Maganin mura, aka jiƙa a kwatarniya.

Tsohuwar kwatarniya, mai launi koriya.

Aka harhaɗa, har ta koma tamkar miya.

Da ludayin bashi, ake zuba wa tunkiya.

Mugun magani, ta kasa fahimta tunkiya.

<< Falsafa 24Falsafa 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×