ZAGI A KASUWA
Murmushin kare ba cizo ba
Dariyar kura bamurna ce ba,
Zagi a kasuwa ba kuwwa ba,
Surutan banza ba labari ba.
Fashin baƙi sai Malamai
Bajintar yaƙi sai jarumai
Kwarkwasa je ka ga karuwai
Iskancin ƙwarai sai kawalai.
Sanin baiti na ga mawaƙa
Sanin zare je ka masaƙa
Malami darajar gafaƙa
Rugum jugum Allah shi sauƙaƙa.
Sanin gulma ka nemi kurma
Rashin sabo nemi kunama
Sanin hatsi nemi manoma
Matowaci ya fi kowa loma.
Faɗan zakuna sai kallo
Gardi shi ne abokin allo
Malami baban allo
Zirga-zirga sai ‘yan ƙwallo.
Mata su suka yin danki
Mazaje ke yin mulki
Gardama kuma sai jaki
Tela shi ne gwanin ɗinki.
Sata tana wurin ɓera
Rashin kan gado sai bera
Wuya ke sa a yi ƙara
Tufka kenan da warwara.
Zantukan ga su a dunƙule
Da kubar hikima nak kulle
Ƙofar ina ko ta ɓulle?
Zanen zabuwa ko bille?