Tawa
Sai tawa! Sai tawa!!
Kana da taka
Ina da tawa
Amma tawa ce ke burge ka
Ga mata nan kala-kala
Me ya sa tawa kawai ka gani?
Me ya sa tawa ka ke son aure?
Kuɗi ka zo ka nuna ne?
Ko matsayi za ka nuna ne?
Kana kallona kana dariya
Bayan na san ita ka ke so
So ka ke ka raba ni da ita
Me ya sa ba za ka riƙe taka ba?
Abin mamaki ba ya ƙarewa
Aboki ne ko kuma ƙawa
Da sun ganka da abin ƙauna
Suma sai su hau ƙauna
Ba sa jin ko kunya ma
Balle su yi maka alfarma.
Ko da tawa ta fi taka
Ai ka fi hakka
Jeka ga naka
Ka tsaya ga taka
Ka kare kanka
Kada ka yi hauka.
Abun da kamar hauka
Cin amana ba lura
Yaudara da me tai kama?
Cuta ba fa ta kyautu ba
Haƙuri ba sakarci ba
Murmushi ba so ne ba.