ABIN LURA
Bari in yi dogon gani
Da zai wa idona magani
Abinda ya dameni tuntuni
Yana ɗora min damuwa.
Neman sa’a a cikin dare
Na zaɓi tumu na tintsire
Ta yaya ne za na warware
Ɗaurin da ya sa ni kururuwa.
Ganin hadari zai yo ruwa
Na rungumi dauɗa nai ƙawa
Ashe ya sauya wurin zuwa
Jiki ya bushe ba ruwa.
Batunmu nake yi ‘yan ƙasa
Yau mun faɗi daga can bisa
Kamar sabbin ƙyanƙyasa
Ba ma gane nisan hawa.
Gari ya ƙone sai ƙishi
Muna kallo mun san da shi
Ta yaya za mu ji armashi
Idan mun nannaɗe hannuwa.
Mu daina jira gun gwamnati
Ganin ta bar mu karabiti
Ta ƙera gada tayi kwalbati
Ba ta inganta rayuwa.
Yawan da ranmu ya ja mana
Ake dukanmu da sanduna
Mun nace su za su yi mana
Ya sa ba ma iya shan ruwa.
Mun zauna ba ma moruwa
Sannan kuma ba ma damuwa
Amma ni na ga tururuwa
Tana ba kanta gudummawa.
Ran nan na hango zanzaro
Ya tsara gini ya tsantsaro
Yanzun ya zarce gidan aro
Cikar burinsa a rayuwa.
Me za ya hana mu tsayin daka?
Mu taimaki kanmu kamar haka,
Mu bar saurin yin sau jika
Bare a saka mu cikin ruwa.
Mu zamto tamkar albasa
A ganmu a cure a kan ƙasa
Mu sa hannunmu mu daddasa
Iri mai haskaka rayuwa.
Idan mun samo arziƙi
Mu ja ƙannenmu cikin jiki
Idan mun barsu da jan ciki
Garina zai shiga ɗimuwa.
Da wannan nai muku sallama
Ina tausar ku da lalama
Mu tashi mu ɗauko harama
Mu sami aminci mai yawa.
Masha Allah