Falsafa
Na fara da sunan Rabbana
Allahu Kai ne ɗaya sarkina
Kai ka zaɓa mini komaina
Na gode wa Ilahu maƙagina.
Yabo da yawan dubunnai
Ga Habibu kawai mu yi mai
Manzonmu da Sarki yai mai
Dukkan ni’ima da maimai.
Ga falsafa da bakinta
Tana ta yaɗa muradanta
Cikin kasuwa, makaranta
Fatan kowa yana jinta.
Falsafa ilimi ne faffaɗa
Rijiyar in har kaf faɗa
A wurin ilimi ka zama ɗa
Ka haure duk tirgaɗa.
Ko Baba ma yana da Baba
Uban wani ba na wani ba
Ɗan mutum ya fi na dabba
Ba a samu mai tantama ba.
Ɓarawo shi ya san lunguna
Ɗan daba shi ya san adduna
Mata ne sirrin adana
Taguwa sarauniyar riguna.
Mata ne ni’imar duniya
Kuma su ne rigimar duniya
Soyayya daɗin zuciya
Nasarar rayuwa ƙarfin zuciya.
Cin hakin sama sai dai raƙumi
Makaho ko me dundumi
Ba ya wasa da kandami
Ɗanɗanon ya yi fa galmi.
Lulluɓi darajar mata
Zubar jini ai sai kwata
Mugun sarki ke mugunta
Baƙin kishi sai mata.
Zantukan kurman baituka
Baitukan ɓoyon zantuka
Haushi ku sani sai karnuka
Haiman ke jawo baituka.