DAULAR ƘYALE-ƘYALE
Bari in kai caffa ga mai gini
A’a dai, cafka cikin sani
Warwarar tufka da martani
Don rabe tsoro da razani.
Ga maƙaloli kamar ruwa
Ga shi harshe na ta yekuwa
Sai ka ce mai kama ƙaguwa
In ya jefa fatsa ya kewaya.
Don tsari aka ce da kai bari!
Kar ka doshi gadar ga, kai biri
Kwai dubun rassa cikin gari
Kama dai hau kai ka kwan ɗari.
Baba mai gadi da zolaya
Sai ya ce kai zo ka ɗan siya
Zan yi ma sauƙi wajen biya
Wa ya kai ya hana ka wataya?
Babu laifi tara tarkace
Kai, tare hanya ka sa ice
Ko fatake zasu yo ice
To su juya ko su karkace.
Sai ka yarda ka bashi ɗan sule
Shi ko ya san gobe zai cale
Sabuwar daular ƙyale-ƙyale
Za ta zo komai ta ƙalƙale.
Ga ta nan gaf-gaf ku gafara!
Ta baje hanyar ga ba jira
Har kadarkon ma ta kassara
Ta kashe, ta tada gobara
A’a ba mai gun ba, rayuwar
Ba fa wai ta wuta ba, damuwar
Ta zamo tushe na ƙaruwar
‘Yan zuwa sata da yin dabar.
Da a ce da ka je da kanka gun
Ce a rushe can a rushe can,
Ƙara yin wata ‘yar gada a nan
Don marayu, ƙyale nan da can.
Duk da na taro abin faɗi,
Gomiya zan bar ta ba daɗi
Ba maɗi a cikinta ba kiɗi
Zan wuce, mu haɗe a nan baɗi.