ZARAR BUNU
01.
Duk kyau na ɗan maciji, in ya ji takura yana kai sara.
02.
Kogon zuma kana sa kanka, cikinsa wuya ta sa ka yi ƙara.
03.
Abun baƙin ciki ga idanu, yin karo da babbar ƙura.
04.
Ai tanadin rufin shuci, don killace hatsi yai saura.
05.
A lallaɓa a ɗan tottoshe, duk kwari da ramin ɓera.
06.
Kururuwar maza a fagen daga, yayin kokawa suke kai bara.
07.
Irin bugun maza na sanya jiri, har ya kada shagon bara.
08.
Wuya da ta yi wuya, nan za ka ga yadda ke gudunsa na bara.
09.
Kirayi jarumai in za’a kara, da masu ƙarfin kura.
10.
A ƙyale dogarai su yi gadi, na lafiyar ƙananan yara.
11.
Ashe baƙin ciki ciwo ne, mai fusata sarki yai ƙara.
12.
Ya sa shi yunƙura da nufin kai martani, don ba ya jure kyara.
13.
Hakan ya sa a gyara zubin tafiyar, don ciki akwai ƴar ƙwara.
14.
Mutuntaka idan ta yawaita, ana yawan zama da yin hira.
15.
A dinga kau da kai daga ɓacin rai, domin a kawo gyara.
16.
A bar munafuki da hali nai, Allah wadai a kai can shara.
17.
A talitse tsaka don kan jama’a, take saka ya yi wara.
18.
A zahiri idan ka ganta, da murmushi da yaƙe haƙora.
19.
Amma hassada ta saka, ka yi kuskure a ƙi ma gyara.
20.
Ku cewa ɗan kada ta ƙare mai, ya je ya taro saura.
21.
Komai yawan muzurai ko shaho, a bar ni sai nai cara.
22.
Idan da rabbana na san zai bani, kariya har in tsira.
23.
Ƙarfi na jakuna sai dai ɗaukar, tumu domin a kai can saura.
24.
Domin ka gane saƙon kukan, kurciya sai ka ɗan saurara.
25.
Akwai batutuwan amfana, yanzu-yanzu ma aka fara.
26.
A yanzu duniya na gane, babu wanda zai ce gyara.
27.
Ana ganin kana aikin banza, kawai sai a yaƙe haƙora.
28.
Ga kunnuwa da tsabar burin, son su jika ka yo ƙara.
29.
A sa’adda ko ka faɗi, a ce Allah wandanka ka yi asara.
30.
Ka zam kamar mugunyar ƙwai, baragurbi mai ɗabi’un ɓera.
31.
Ro ka ga sai ka dage, ka yi aikin da za’a ce ma gwara .
32.
Ka kauce duk abinda gurin, ƙimarka zai zamanna tijara.
33.
Ƙarya, riya da girman kai, kar duk su sa ka dinga fitsara.
34.
Balle kuwa cin mutuncin, dattijai da cin zalin ‘yan yara.
35.
Na san da kai hakan a gaba, kai ne za’a dinga kai wa ƙara.
36.
Ruɗi na zamani kar ya sa ka, kai ta rayuwa da gadara.
37.
Domin zama a nan zai ƙare, duniyar ga wasan yara.
38.
Akwai hawan ƙiyama ranar, babu mai tsimi da dabara.
39.
Idan ka shuka khairi ranar, za ka sami damar tsira.
40.
Ka kyautatawa kowa a nan duniyar, tabbas za ka sarara.
41.
Komai muƙaddari ne tuntuni, an riga da an tsatstsara.
42.
Idan har ka riski khairi, to godewa rabbana zai ƙara.
43.
Idan ka riski sharri to laifinka ने, ka jeka ka gyara.
44.
Yarda da ƙaddara shi ke sa, a yi ganin ruwa a sahara.
45.
Idan ka yarda Alalh ne mai yi, a yanzu kam ka wuce tsara.
46.
A kwan a tashi zan ƙarar da dami, matuƙar ina yin zara.
47.
Kaɗan kaɗan idan na samu, sai na bisu in tattara.
48.
In je in sai hatsi in sa turmi, in daddaka da taɓarya.
49.
Domin a duniya sai ka dage, kamar kana cin taura.
50.
A nan gabanka kwai babban tafkin, da dole ne sai ka haura.
51.
Saurin fushi nadama ke sawa, ya sa a tafka asara.
52.
Ya sa ka ayyuka tamkar mai cin, baƙar gyaɗa ba ɓara.
53.
To danne zuciyarka ka zamto, jarumi ka sauke gaɓara.
54.
Samo wuri ka zauna, ka huce ka buɗe shafin hira.
55.
Ka dinga yin yawan haƙuri, in kayi gamo da ‘ya’yan yara.
56.
Ku sani, me tafiya shi yai kama, da ɗaukar gora.
57.
Laƙani, ƙarshen sallar nafila, cika ta da mara.