Skip to content
Part 8 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

SO DA SOYAYYA 

Na sani a soyayya wasu sun yi nisa, 

Wasu sun wuce tunanina sai gani daga nesa, 

Wasu za su iya haɗe ni tamkar Mesa, 

Amma duk da hakan zan ƙoƙarta, 

In yo ɗan bayani bisa ƙoƙarina. 

Shi so, shi ke haifar da soyayya, 

Shi so, shi ne asali na lobayya, 

A dalilin so ake samun tarayya, 

Saboda so ne ake ƙulla soyayya, 

Har wata rana kaji ana auratayya. 

Da so da soyayya tagwaye ne, 

Da zarar ka kamu da so, 

To kai ma masoyi ne, 

Daga wannan rana ka fara soyayya, 

Ko da wanda ka ke so a cikin mafarki ne. 

Ita soyayya ba a yi mata tilas, 

Ba ta buƙatar hanya a sama ko ƙasa, 

Ba ta da lokacin wanda zai mata cikas, 

Sannan babu mai ce mata kule, 

Face sai ta ce da shi as! 

Wanda duk ya fara soyayya, 

To fa ya zarce yin jayayya, 

Da wanda ba ya soyayya, 

Domin a matakin ƙaunayya,

Ba zai yiwu a haɗa su ba.

Daɗina da so bai san tsoro ba,

Ko da a yaro ne balle kuma babba,

Ko da saurayi ne ko ko budurwa,

Ko da mai basira ne ko wawa,

Bai zarce soyayya ta biyo ta kai nai ba.

Kishi a soyayya wannan wajibi ne,

Kunya a soyayya tamkar magi ne, 

Kyauta a soyayya tamkar gishiri ne,

Mutunci a soyayya shi kuma ruwa ne,

Alƙawari a soyayya wannan shi ne komai.

Kar ka ce ka fi ƙarfin so,

Domin so ya fi ƙarfin ka,

Kar ki ce ba kya yin so,

Ke dai jira lokacin ki,

Domin so halitta ne da game komai.

Kar ka zagi mai haukan so,

Kai ma ba ka zarce shi ba,

Kar ki zargi mai kishi a so,

Zaɓin ba nashi ne ba,

Ke dai yi addu’a da kalami mai taushi.

<< Falsafa 7Falsafa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.