Skip to content
Part 9 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

JIYA IYAU 

01.

Akwai dare a safiya, 

Kamar tudu a rijiya, 

Buhun ƙaya, a ragaya, na rataya, in antaya?

02.

Bari in haskake duhu, 

Da ni da ku mu hau sahu, 

Ku ji ni ko ku barni zan taƙarƙare kamar duhhu. 

03.

A shekaru aru-aru, 

Mazanmu sun ka tattaru, 

Cikin salo da laluma da dandazon dabarbaru.

04.

Guri guda ya albasa, 

Su kai shirin riƙon ƙasa, 

Da ƙoƙari da haƙuri da jinkirin hawa bisa.

05.

A ture masu mallaka, 

A kai ƙasa ga daukaka, 

Ta sami kai, ta ‘yantaka, ta mulkin kai kamar haka. 

06.

Aka zama daban-daban, 

A san ta yadda za’a zan, 

Ƙasa guda da shugaba da gwamnati iri daban.

07.

A ƙarshe uwa Ingila, 

Ta yassare cikin kula, 

Ta tsara tsarika a constitutional ta kammala.

08.

Wata na goma ɗai ga shi, 

Akai biki me armashi, 

A yanzu ko meye da kanmu zamu aiwatar da shi.

09.

Muna zaton mu murmusa, 

Ashe akwai manaƙisa, 

Ya sa sukai zugun, idanuwa garemu sun ka sa.

10.

Akwai abinda su ka zuba, 

Da zai hana mu ci gaba, 

Idan na ambata a yanzu ba su barni in yi gaba.

11.

Ku ɗan tsaya a sannu tsaf, 

Ku ɗan matso ku ji ni kaf, 

In ba ku sirrikan da za su sa ku binciko ƙwaƙwaf.

12.

To shugaba guda nawa, 

Ya hau, ya sau, ya kuma hawa,

Da ba ya son a sake son ya zo a ce ya kuma hawa?

13.

Abin yana ta zagaye, 

Su hau a soji kai tsaye, 

Yo har a yanzu su suke hawa, suna ta kewaye.

14.

Ƙasa da arziƙi tsibi, 

Kasa guda ta zama riɓi, 

Ya sa ake ta kokawar a shugabanci galibi. 

15.

Kafin ka zamma shugaba, 

Ƙasa ta sa ka kan gaba, 

A ƙalla dai a shekarunka arba’in ka sa gaba.

16.

Amma idan su kai ƙasa, 

A hantare ka, ka isa!

Ta yaya zamu ƙyale ɗan ƙararrami ya ja ƙasa?

17.

Wanda bai da ilimi, 

Anya a kira shi malami?

Ina gwagwarmayar da yai da ta mayar da shi jarumi?

18.

Tunanuka irin haka, 

Cikinsu babu mutuntaka, 

Ta ya ba za a ƙyale saurayin jini ya haskaka?

19.

Duk da ba a bamu ci, 

Da sha, tsaro da tabbaci, 

Amma a ƙalla a bari mu rayu cikin hayyaci.

20.

Guda fa ne a cikin ɗari, 

Idan na sami sarari, 

Za na wassafo su har da kanku za ku ce bari

21.

Mu tashi ni da kai tsaye, 

Ko da kuwa za a rataye, 

Mu nuna inda duk kurakurai suke, a zaizaye.

<< Falsafa 8Falsafa 10 >>

2 thoughts on “Falsafa 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×