WAKAR BAKANDAMIYA
Da sunan sarki rabbana mai duniya
Al-kaliƙu wanda ya yo duniya
Ya yi ƙorama har da teku na maliya
Al-maliku kai ke mulkin duka duniya
Sunanka ne farkon faɗi kowace safiya
Kuma kai nake kira da yamma sakaliya.
*****
Na yi yabo gurin Annabi Muhammadu
Da ya fi kowa bauta Annabi Hamidu
Ma'aikin Allah Sahibinmu Mahmudu
Shalelen Ubangijina ya Ahmadu
Allah ka ninka salatai a wurin Ahidu
Manzonmu sha-kundum Mahmudu.
*****
Waƙa ce zan rera wa Bakandamiya
Shafin yanar gizon ga na duniya
Da ya zamo abin son mutanen Ifirikiyya
Kuma sha ziyartar. . .
Gaskiya Bakandamiya ta sha waƙa kam.
Na gode sosai. #haimanraees
Yayi
Na gode sosai. #haimanraees