Skip to content
Part 13 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

WAKAR FYADE

Bismillahi sarkina da babu mai taɓa masa ikonSa

Salatinka a wajen manzo Aminu har da sahabbansa

Baban Fati da babu wani manzo bayansa

Masu yin fyaɗe a gareku nake kira ku bar yinsa

Ba shi da wata riba sai asara a cikinsa

Ita rayuwa kowa na da ikon yin nasa.

*****

Menene yasa ku ke cutar da ‘yar uwata?

Shin menene yasa ku ke cutar da ƙanwata?

Menene yasa ku ke cutar da yayata?

Shin menene yasa ku ke cutar da ‘yata?

Wai menene ya sa ku ke fyaɗe wa mata?

Lallai dabbanci ya tabbata ga duk mai fyaɗe ga mata.

*****

Ku sani matan nan fa su ba haja ce ba

Kuma matan nan su ba wasu kaya ne ba

Su matan nan ba litattafai ne ba

Su ma fa mutane ne ko ba ku gane ba?

Su ma fa suna da rai shin wai ko ba hakane ba?

To me yasa za ku tauye mu su abin da ba su tauye wa kowa ba?

*****

Shi mai fyaɗe ya fi kama da jaki a gani na

Ga shi da ƙarfi kuma ba wayo a tunanina

Ba nazari babu tunani sai halin ɓauna

Shi yasa ko da yaushe nakan kira shi sauna

Ba shi da amfani sai dai isar da ɓarna

A duk sa’adda na ganshi nakan ji zuciyata na ƙuna.

*****

Mai yin fyaɗe ka tuba ka daina ɓarna

Ka ji tsoron rabbbana Mahaliccina

Ka tuna da ranar tsayuwa a cikin rana

Ranar da za ka yi nadama bisa kan ɓarna

Da ka aikata yau a cikin rana

Wallahi ranar ba sauƙi ga duk wani mai ɓarna.

*****

Rabbana Ubangiji ka kare ɗiyanmu

Sarkina Ubangiji ka kare ahalinmu

Ya Mannanu ka tsare duk ‘yan uwanmu

Al’alimu kai ne masanin duk lamuranmu

Ka yaye mana musifar da ta same mu

Ka shiryar da mu da duk al’ummar mu.

<< Fasaha Haimaniyya 12Fasaha Haimaniyya 14 >>

4 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×