Skip to content
Part 2 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

ALLAH NA NAN

Bismillah na sa Ubangijina

Rabbi sarki, wato Allah kenan

Shi ke da kowa, shi ke da komai

Jallah sarki, wato Allah kenan

Gaisuwa gare shi ɗan Amina

Malamina, Manzon Allah kenan

Cikamakin duka Annabawa

Baban Fatima Manzon Allah kenan.

*****

Baka da kowa, baka da komai

Kada ka damu domin Allah na nan

Baka da aiki, ba makama

Kada ka damu domin Allah na nan

Ga makaranta, ba kuɗin biya

Kada ka damu domin Allah na nan 

Kana son aure, babu hali

Kada ka damu domin Allah na nan.

*****

Baki da mahaifi, ko mahaifiya

Kada ki damu domin Allah na nan

‘Yan uwanki duk sun tsane ki

Kada ki damu domin Allah na nan

Baki da sana’a ga buƙatu

Kada ki damu domin Allah na nan

Duka samarin ki ba na kirki

Kada ki damu domin Allah na nan.

*****

Baka da kuɗi, ga iyali

Kada ka damu domin Allah na nan

Sana’a kake yi, babu kasuwa

Kada ka damu domin Allah na nan

A gidan haya kake, ba kuɗin biya

Kada ka damu domin Allah na nan

Maƙiya ne suka ishe ka

Kada ka damu domin Allah na nan.

*****

Mijinki ne yake zaluntarki

Kada ki damu domin Allah na nan

‘Ya’yanki ne suke baki matsala

Kada ki damu domin Allah na nan

Dangin mijinki ne basu son ki

Kada ki damu domin Allah na nan

Kishiyar ki ce take baki matsala

Kada ki damu domin Allah na nan.

*****

Kuna wani hali na ha’ula’i

Kada ku damu domin Allah na nan

Haihuwa kuke nema ba ku samu ba

Kada ku damu domin Allah na nan

Abokai, ƙawaye sun guje ku

Ya ɗan uwana da ‘yar uwata

Kada ku damu domin Allah na nan.

<< Fasaha Haimaniyya 1Fasaha Haimaniyya 3 >>

5 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×