Masoyiyata
Ke ce a zuciyata
Na baki rayuwata
Kin fi su dukkan mata
*****
Saboda ƙauna
Har an sa mini suna
Wai ni na zama sauna
Akan ki na zama sauna
*****
Ko da bani da kowa
Ni kin fi mini kowa
Ko babu komai
Ai ni kin fi mini komai
*****
Zuciyata dai kin sace
Akan ki duk na zauce
Na bi na susuce
Gani nan ƙasa kwance
*****
Na bani lalace
Masoyiya ta fece
Ta barni sai yin zance
Ni kaɗai kamar na zauce
*****
A taimaka a ɗan nemota
Idaniya su ganota
Wallahi ko ba. . .
Hmmmmm I love this.