Skip to content
Part 28 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

So Ya Rike Ni

So ya riƙe ni ya saka na ƙame

Ƙaunarki ta sa na bi na sanƙame

Furucin ki ke sa in ji duk na tsime

Ya Sahibata karki barni in ƙume

*****

Kin zamo annuri da ke a zuciya

Kin riga kin mamaye zuciya

Zaƙi na sonki ya fi zaƙin rake

Buri na raina kawai in rayu da ke

Ƙaunarki ta sa na bi na sanƙame

Furucin ki ke sa in ji duk na tsime

*****

Ke ce mafarkina da ya sama zahiri

Ke ce muradin rai da ke tafi da ni

Ki ɗan gane, ki ɗan gane

In babu ke ni dole sai na mace

Don rashin ki dole zana haukace

Don Allah soni karki barni in mace

In kika barni nai asarar mace

*****

Baƙin lamura ne fa suke ta faruwa

Na Gaza tunanin komai sai mantuwa

Ki cece ni, ki cece ni

Allahu yasan ni da gaske nake

Burin auren ki kullum nake

Ya zamo a tare za mu zauna da ke

Har zuwa abada za ni zauna da ke

******

So ya riƙe ni ya saka na ƙame

Ƙaunarki ta sa na bi na sanƙame

Furucin ki ke sa in ji duk na tsime

Ya Sahibata karki barni in ƙume

<< Fasaha Haimaniyya 27Fasaha Haimaniyya 29 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×