DAGA ZUCIYATA
Da sunan Allah Rabba
Ba wa’azi zan yi muku ba
Ba nasiha zan muku ba
Ba damunku nake son yi ba
Zance ne daga zuciyata zan furta.
*****
Damuwa ta aure ni
Damuwa ta kama ni
Damuwa ta dame ni
Damuwa ta kayar da ni
Ta bi duk ta dagule zuciyata.
*****
Ban san fa me ya sa haka ba
Ban san fa me na yi musu ba
Ban san ya suke so ba
Ban san ya suke so na yi ba
Ban san menene yasa suke ƙina ba.
*****
Wai ni ba dogo ne ba
Wai ni ba siriri ba
Wai ni ai ban waye ba
Wai ni ban san komai ba
Wai shin sai yaushe ne za ku bar gaba?
*****
So suke wai in yi kaza
So suke wai in bar kaza
So suke in je wuri kaza
So suke in bar gu kaza
So suke dai in zamo kamar banza.
*****
Sun ce min ɓarawon kaza
Sun ce wai na saci reza
Sun ce wai ai na yi kaza
Sun ce wai ai na ce kaza
Sun ce wai ni na zamo kamar geza.
*****
Saboda na ƙi zama wawa
Saboda na gaza duƙawa
Saboda na gaza dainawa
Saboda na gaza kasawa
Saboda na zama wanda ya ƙi lalacewa.
*****
Shi yasa basa sona
Shi yasa fa suke ƙina
Shi yasa suke tsorona
Shi yasa suke ta guduna
Shi yasa suke min hassada a aikina.
*****
Ko da dai kun cuce ni
Ko da dai kun zalunce ni
Ko da dai kun tauye ni
Ko da dai kun fa tsane ni
Ko da ba kwa son ganina dai gani.
*****
Komai na yi ban burge ba
Komai na yi ban fa iya ba
Ko na yi ma ba za a yaba ba
Kuma ba za a koya min ba
Komai in dai nawa ne ba a so ba.
*****
Ya kuke so ne wai na yi?
Me kuke so ne wai na yi?
Ta yaya zan iya canja yanayi?
Shin ta yaya zan canja ra’ayi?
Bayan na san ni ne akan gaskiya?
*****
‘Yan uwa wasu na ƙina
Duk da dai wasu na sona
Abokai na ta guduna
‘Yan mata na shakka na
Duk kawai saboda wai ina son gaskiya.
*****
Jama’a sun sani gaba
Jama’a sun tasa ni gaba
Jama’a na nuna min gaba
Jama’a sun hanani ci gaba
Jama’a kar ku manta Allah ba zai ƙyale ku ba.
*****
Na zamo kamar mujiya
Wacce ta faɗa rijiya
Tana faman ninƙaya
Amma ta gaza kufcewa
Kuma an gaza cetonta wai don ana tsammanin ba ta da gaskiya.
*****
Duk wanda shi bai da ra’ayi
Wannan ku kira shi gawayi
Girki da shi kawai za’a yi
Bayan nan ba shi da amfani
Wannan shi ne zance na gaskiya.
*****
Ka zamo mai tausayi
Zalunci sam kar da ka yi
Hassada ita ma kar ka yi
Mugunta ma sam kar ka yi
In ko ka yi su tabbas ka kauce gaskiya.
*****
Kada ka yawaita inkari
Ka zamo mai yin nazari
Ka zamo mai yawan uzuri
Ka zamo mai kuzari
Idan har ka yi hakan kana kan hanyar gaskiya.
*****
Ka zamo jajirtacce
Ka zamo nagartacce
Ka zamo ingantacce
Ka zamo abin kwatance
In har ka yi hakan tabbas kana kan gaskiya.
*****
Ba lallai sai ka soni ba
Ba lallai sai kin soni ba
Ba lallai sai kun soni ba
Kuma ba lallai sai kun ƙini ba
Amma kun gaza fahimtata shi ya sa kuka kasa gano wa ke da gaskiya.
*****
Na san ni mai laifi ne
Ka san ni mai laifi ne
Kin san ni mai laifi ne
Kun san ni mai laifi ne
Kuma kowa na duniya yana laifi.
*****
Na san ni mai zunubi ne
Ka san kai mai zunubi ne
Kin san ke mai zunubi ne
Kun san ni mai zunubi ne
Kuma kowa na duniya yana zunubi.
*****
Na san na yi kuskure
Ka san ka yi kuskure
Kin san na yi kuskure
Kun san na yi kuskure
Kuma kowa na duniya yana kuskure.
*****
Kada duniya ta ruɗe ka
Kada abokai su ruɗe ka
Kada kuɗi su ruɗe ka
Kada zuciya ta ruɗe ka
Idan ko har ka yi hakan ka bar hanyar gaskiya.
*****
Ka yarda wani ya fi ka
Ki yarda wata ta fi ki
Ka yarda wasu sun fi ka
Ka bi duk wanda ya fi ka
Idan har ka yi hakan kana kan gaskiya.
*****
In har ba ka son kanka
Ta yaya za ka so waninka?
In har ba kya son kanki
Ta yaya za ki so wanin ki?
In har ba son kanmu ta yaya za mu so wasunmu?
*****
In kace ban fa iya ba
To ai sai ko ka koya min
In ko ba za ka iya ba
Ka ga dole ka ƙyale ni
Tun dai ita rayuwa sai da gwadawa.
*****
In kika ce ba kya sona
Sai ki bar ni da mai sona
In ko sam ba ki iyawa
Sai ki kuma daina to bina
Domin ita rayuwa sai da soyayya.
*****
Kowa dai na da ra’ayi
Na san kana da ra’ayi
Ke ma kina da ra’ayi
Kowa ma na da ra’ayi
To akan me za a ce kada in zamo mai ra’ayi?
*****
Nima jini ne a jikina
Jini ne ba ƙarfe ba
Zuciya ce a ƙirjina
Zuciya ba dalma ba
Domin nima ɗan Adam ne ba ƙarfe ba.
*****
Ko na yi ko kuma ban yo ba
Za ace ban yi dai-dai ba
Komai na yi wai na yi ƙwaɓa
Komai na yi wai ban caɓa ba
Sai kace ni ne na auri asara.
*****
Nima fa ɗa na Adam ne
Nima fa ina da idanu ne
Nima ina fa da hanci ne
Nima ina fa da ai kunne
Nima ina da duk abin da kowa yake taƙama da shi.
*****
Kamar yadda kake son kanka
Haka nima nake son kaina
Kamar yadda kike son kanki
Haka nima nake son kaina
Kamar kowa ni ma ina son kaina.
*****
Kana so kai ka ji daɗi
Kina so ke ki ji daɗi
Ku sha madara mai garɗi
Da ɗanɗanon duk wani daɗi
To menene yasa ni ban cancanci hakan ba?
*****
In har ma laifi ne na yi
Me ya sa za ku kyare ni?
Madadin ku nusar da ni
Shi ne sai kuma ku tsane ni
To menene ribar hakan don Allah?
*****
Iyaye duk ku yi nazari
Shugabanni ku yi nazari
Malamai ku yi nazari
Manyanmu duk ku yi nazari
Shin matsalar ta ina take a sassan mu?
*****
In Allah ya maka ni’ima
Burinka ka guji al’umma
In Allah ya jarrabe ka
Sai ka nufo gun Al’umma
Ta yaya ita al’ummar za ta ci gaba?
*****
Ka ce ni wai yaro ne
Aikin ga wai na manya ne
Manya a cikin dukka mutane
Wai ni na gaza in gane
Bayan kuma kullum duniya ni ake cuta.
*****
Ku sani Allah na nan
Ku sani tsufa na nan
Ku sani mutuwa na nan
Ku sani lahira na nan
Ku sani ranar tsayuwa ita ma na nan.
*****
Rabbana ka yafe mu
Rabbana ka kare mu
Rabbana ka shirye mu
Rabbana ka cece mu
Rabbana ka kawo mana ɗauki da gaggawa.
Wannan kamar don ni ka yi rubutun nan, abubuwan da nake son fada ne duk ka fada. Allah ya ƙara basira.
Amin. Jazakallah Khair
Saƙo ya fita. Allah ya ƙara basira.