KAICO
Bissmillah da sunan ilahi
Wanda ya aiko ɗan Abdullahi
Zan yi batu da tambihi
Bani dama sarkina ilahi.
*****
Mu yaran zamani yau
Ba mu jin magana ayau
Iyaye na ta fama
Mu kuma muna ta fankama.
*****
Ba mu tsoron ɓaci na ransu
Ba mu yin ladabi garesu
Ba ma biyayya garesu
Amma in buƙata ta tashi mu je wurinsu.
*****
Ra’ayinmu kawai muke bi
Ko mara kyau ne shi za mu bi
Ra’ayinsu ko ba ma bi
Ko da mai kyau ne ba ma bi.
*****
A hakan muke so wai mu ci gaba
Alhali da uwarmu muke gaba
Mun ce mu ne za mu shige gaba
Wai shugabancin ya fi ƙarfin uba.
*****
To yaya ma za mu ga haske?
Bayan albarkar mun make?
Mun aje uwarmu a gefe
Mun ɓoye ubanmu a shinge.
*****
Kaico! Wannan lamari da gyara
Shi ya sa ma har na ɓara
Ku ka ji ni ina ta ƙara
Sai ka ce wanda sago ya sara.
*****
To wallahi mu yi hankali
An ce duniya ɗamarar jangali
Dole sai an bita a hankali
Ko kuma mu faɗa baƙin hali.
*****
Allah ka ƙara wa iyaye lafiya
Ka sa mu gama da su lafiya
Mu zamo masu ƙaunar tarbiya
Ga manyanmu mu zam masu biyayya.
*****
Sarki ka shiryar da mu
Da abokai da ahalinmu
Da dukkan ‘yan danginmu
Ka sa shiriya a zukatanmu.
Amin. Allah ya ƙara basira.
Amin. Jazakallah Khair.
Assalamu alaikum warahamatullahi ta ala wabara katuhu