KUKAN KURCIYA
Da sunan sarkina zan fara
Wannan da shi ne ya yiwo fara
Ya yi kare kana ya yo kura
Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura
Hikimar Allah sam ba ta da iyaka.
*****
Tsira da aminci gun baban Zahra
Wannan da cikin annabawa ya yo zarra
Wanda duk wata daraja tuni ya tara
Sahabbai da alihi duka na tara
Salati gare shi na ke furtawa babu iyaka.
*****
Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta
Mu zam nutsuwa da neman mafita
A wayi gari junanmu za mu fifita
Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita
Ko ba. . .
Kukan Kurciya jawabi…
Mai hankali ke ganewa. #haimanraees