KAUNA TA YI NISA
Bismillah Allah sarkina gwanina
Kai ke da ikon dukkanin lammurana
Yau gani da ƙoƙo na ɗaga hannuwana
Roƙon da na yo ka cika burikana
Kai ne ke biya mana dukkan buƙatu
Hakane!
*****
So ya yi nisa zuciya ta yi kewa
Ina mararinta ruhi na ta ƙwawa
Burin idanu fuska su yi ganowa
Su kuma kunnuwa murya su yi jiyowa
Rashi na ganinta yasa na sha wuya
Hakane!
*****
Ita sahibata sam-sam bata da muni
Kyawun idon ta ya wuce kyan furanni
Tana da kyan diri, sura har da kamanni
Takan yi kwalliya da. . .
Allah sarki, rayuwa kenan.
Hakane